Gabatarwa:
Ƙungiyar lafiya ta duniya (world health organisation) ta ƙiyasta cewa kullum sama da mutune miliyan ɗaya suna kamuwa da cututtuka ta hanyar jima'i wadanda aka fi sani da sanyin mata, amma mafi yawancin cututtukan basu nuna alamomin komai kai tsaye.
Mene ne sanyin mata / cututtuka masu yaÉ—uwa ta hanyar saduwa?
Masana sun fassara ma'anar sanyin mata ko cututtuka masu yaÉ—uwa ta hanyar jima'i a matsayin cututtuka waÉ—anda ake iya samu ta hanyar haÉ—uwar fata da fata a lokacin saduwar al'aura da al'aura (vaginal sex) ko saduwar al'aura da dubura (anal sex) ko kuma saduwar al'aura da baki (oral sex).
Saduwa ita ce hanya ta farko da ake iya samun waɗannan cututtukan, amma duk da haka, ana iya samun waɗannan cututtukan na sanyin mata ta hanyar ƙarin jini, tarayya wajen amfani da abubuwa masu kaifi ko tsini, ko kuma iyaye mata masu ciki su yaɗawa jarirai da ke cikinsu.
Ire-iren sanyin mata ko cututtukan da ke yaÉ—uwa ta hanyar jima'i
1. Bacterial sexually transmitted infections(STIs)
- Cutar sanyin Gonorrhoe wadda ƙwayar bacteria mai suna Neisseria gonorrhoe ke kawo wa.
- Cutar sanyin Chlamydia wadda ƙwayar bacteria mai suna Chlamydia trachomatis ke kawowa.
- Cutar sanyin Sphyllis wadda ƙwayar bacteria mai suna Treponema pallidum take kawowa.
- Cutar chancroid wadda ƙwayar cutar bacteria mai suna Haemophilus ducreyi take kawowa.
- Cutar lymphogranuloma venereum wadda wasu ƙwayoyin cutar bacteria daga cikin iyalan Chlamydia trachomatis suke kawowa
- Cutar granuloma inguinale wadda ƙwayar cutar bacteria da ake kira Klebsiella granulomatis
2. Viral sexually transmitted infections
- Cutar ƙurajen herpes wadda ƙwayoyin cutar Herpes simplex virus suke kawowa.
- Cutar human papilloma virus wadda ƙwayar cutar Human papilloma virus suke kawo wa.
- Cutar HIV/AIDS wadda ƙwayoyin cutar Human immunodeficiency virus suke kawo wa.
- Ciwon hanta na Hepatitis B da Hepatitis C wanda ƙwayoyin cutar Hepatitis B virus da Hepatitis C virus ke kawo wa.
3. Parasitic sexually transmitted infections
- Cutar sanyin Trichomonas wadda ƙwayar cutar parasite da ake kira Trichomonas vaginalis.
- Cutar sanyin Gadnerella wadda ƙwayar cutar parasite da ake kira Gadnerella vaginalis ke kawo wa.
- Ƙwarkwatar gashin mara: Wata cutar parasite ce wadda ƙwarin ƙwarkwata da ake kira pubic lice suke kawo wa.
- Cutar ƙazuwa (scabies); Wata cutar parasite ce wadda ƙwarin itch mites suke kawo wa.
- Cututtukan jima'i masu kawo zubar ruwa daga al'aura (STIs with discharge) misali; Sanyin Gonorrhoe, Chlamydia, Trichomonas da Gadnerella.
- Cututtukan jima'i masu kawo ƙuraje a al'aura (STIs with genital rashes). Misali: Herpes simplex virus, Human papilloma virus da kuma Sphyllis.
- Cututtukan jima'i da basu kawo zubar ruwa ko ƙurajen al'aura. Misali; HIV/AIDS, Hepatitis B da Hepatitis C.
Alamomin sanyin mata ko cututtukan da ke yaÉ—uwa ta hanyar jima'i
- Discharge; Wannan shi ne zubar mummunan ruwa daga al'aura. Kalar ruwan ya danganta da cutar da ya kawo zubar sa, mafi yawanci ruwan yakan kasance mai wari. Ruwan yana fitowa ne daga farjin mace ko azzakarin namiji ko duburar masu luwaÉ—i.
- Genital rashes or ulcers: Ƙurajen al'aura, haka ma ƙuraje zasu iya fitowa a baki, ga masu amfani da baki wajen jima'i.
- Dysurea: Jin zafi lokacin fitsari.
- Dyspareunia: Jin zafi a yayin jima'i.
- Genital itching: Jin ƙaiƙayi ga al'aura.
- Fever: Yawan zafin jiki.
- Lower abdominal pain: Ciwon mara.
- Irregular menses: Rikicewar jinin al'ada.
- Inguinal lymphadenopathy: Kaluluwa.
Yadda ake maganin cututtukan sanyin mata
Ana amfani da magungunan antibiotics domin magance cututtukan da ke yaɗuwa ta hanyar jima'i waɗanda ƙwayoyin cutar bacteria suke kawowa.
Misali. Ceftriaxone, Cefixime, Flagyl, Doxycycline don magance cutar Chlamydia da Gonorrhoe, Penicillins don magance cutar Sphyllis. Cutar Gadnerella duk da cewa cuta ce wadda ƙwayoyin parasite ke kawo wa, amma ana amfani da magungunan antibiotics wajen magance ta, magungunan da ake amfani su ne Ornilox, Ofloxacin+Clindamycin, da flagyl da dai sauransu.
Ana amfani da magungunan shafawa da ake kira anti-parasitic lotions domin magance ƙwarƙwatar gashin mara.
A lura cewa idan mutum ya kamu da ɗaya daga cikin cututtukan jima'i toh dole ne sai anyi masa magani tare da duk waɗanda yake yin jima'i dasu ko da lafiyar su ƙalau. Kuma dole su daina yin jima'i har sai sun gama shan magani.
Illolin cututtuka masu yaÉ—uwa ta hanyar jima'i - Sanyin Mata
- Rashin haihuwa
- Rashin jin daÉ—in jima'i
- Ƙurajen al'aura
- Tsukewar bututun fitsarin maza
- Cutar sanyin Sphyllis tana iya taɓa ƙwaƙwalwa
- Ramewa
- Shiga yanayin ƙunci.
- Mutuwar garkuwar jiki - HIV/AIDS ke kawo wannan
- YaÉ—uwar cututtukan zuwa cikin kwankwaso
- Kawo cutar sanyin mara
- Cutar sanƙarar bakin mahaifa - HPV ke kawo wannan.
- Ciwon hanta da kuma cutar sanƙarar hanta - Hepatitis B da Hepatitis C ke kawo wannan.
Ya zan kare kaina daga kamuwa da cututtukan sanyin mata?
- Yin aure da kuma tsayawa ga abokin jima'i É—aya kacal.
- Daina yin jima'i baki É—aya.
- Amfani da robar kariya ta condom.
- Amfani da robar kariya ta baki da ake kira "dental dam" ga masu yin jima'i da baki.
- Allurorin riga-kafi, misali riga-kafin cutar HPV da kuma Hepatitis B.
- Saurin neman magani ga waÉ—anda cututtukan suka kama.
0 Comments