Illolin ciwon koda da yadda mutum zai kare kansa daga kamuwa da ciwon koda

Gabatarwa

A rubutun mu na baya munyi bayani sosai game da ciwon koda, alamomin sa da kuma abubuwan da ke haddasa shi, a cikin wannan rubuta zamu yi tsokaci game da illolin ciwon koda da hanyoyin da mutum zai bi domin kare kansa daga kamuwa da ciwon koda(1).




Illolin ciwon koda

Cutar ciwon koda na iya shafar kusan kowane bangare na jikin mutum, wannan shi yasa matsalolin da ciwon koda yake haifarwa suna da dimbin yawa. Kadan daga cikin matsalolin da ake iya samu sun haÉ—a da:
  1. Taruwan ruwa a jiki, wanda zai iya haifar da kumburin fuska, kumburin hannuwa da Æ™afafu ko ma kumburin jiki gaba daya. Haka kuma taruwan ruwa a jiki yana iya haifar da hawan jini, ko kuma taruwan ruwa a cikin huhu (pulmonary edema)(2).
  2. Hauhawar sinadarin potassium a cikin jini (hyperkalemia), wanda zai iya dakushe aikin zuciya, kuma idan hauhawar tayi tsanani takan iya zama barazana ga rayuwa ta hanyar tsayar da zuciya kai tsaye.
  3. Rashin jini (Anemia)(2)
  4. Hawan jini. Ciwon koda yakan iya kawo ciwon hawan jini(3).
  5. Ciwon zuciya(3)
  6. Raunin ƙasusuwa da ƙara haɗarin karayar kashi
  7. Ragewar sha'awar jima'i, rashin karfin mazakuta ko hana samun haihuwa.
  8. Bushewar fata da kaikayin jiki
  9. Yin dameji ga kwakwalwa, wanda zai iya haifar da wahalar maida hankali akan abu daya, canje-canjen hali ko kuma ciwon damuwa.
  10. Rage karfin garkuwar jiki, wanda zai sa mutum ya zama mai saurin kamuwa da cututtuka.
  11. Pericarditis, wannan shi ne kumburin wata yar fata mara nauyi da ke lullube da zuciya. (pericardium)(3).
  12. Matsalolin juna biyu ga mata waÉ—anda zasu iya shafar mai ciki da kuma tayin da ke cikinta(3).
  13. Gazawar koda baki daya, lalacewar da koda ba za ta iya jurewa ba (ciwon koda mataki na karshe), a wannan matakin mutum yana buƙatar ko dai wankin jini (dialysis) ko dashen koda don rayuwa(3).

Yadda mutum zai kare kansa daga kamuwa da ciwon koda 

Don rage haÉ—arin kamuwa da cutar koda:

Ya zama wajibi a bi umarni kan ka'idodin shan dukan magunguna. Lokacin amfani da magunguna masu rage raÉ—aÉ—i, kamar aspirin, diclofenac, ibuprofen (Advil, Motrin IB,) da acetaminophen (Paracetamol, da dai sauransu), dole ne abi umarnin likita, saboda shan magungunan kashe zafi da yawa na dogon lokaci zai iya haifar da lalacewar koda(1).

Kula da lafiyayyan nauyi ko kiba. Idan kana cikin masu lafiyayyan nauyi, toh ya kamata ka kiyaye shi ta hanyar yawaita motsa jiki. Idan kana buƙatar rasa nauyi ko rage kiba, to kayi magana da likita kwararre domin ya aza ka kan hanyoyin da zaka bi ka rage taiba. Lafiyayyan nauyi yana rage hadarin kamuwa da ciwon koda.

 Daina shan sigari. Shan tabar sigari na iya lalata kodan ku, ko kuma ya sa kodar da ta fara lalacewa tayi saurin gazawa. Idan kai mai shan taba ne, yi magana da likitanka game da dabarun dainawa.

  Kula da yanayin lafiyar ku tare da taimakon likitocin ku. Idan kuna da cututtuka ko yanayi waÉ—anda ke Æ™ara haÉ—arin cutar koda kamar wadanda muka ambata a rubutun mu na farko, toh kuyi gaggawar neman magani domin magance su ko sarrafa su yadda ya kamata.

Misali mai hawan jini ya fake shan magani da zuwa ganin likita akai-akai, haka mai ciwon sukari, mai kiba ya fara motsa jiki da kuma cin lafiyayyan abinci, da dai sauransu.

 Daina amfani da magungunan gargajiya. Mafi yawancin magungunan gargajiya da tsime suna yiwa koda da hanta illa sosai.

  Shan ruwa akai-akai yadda ya kamata. Wannan ma yana kara lafiyar koda ta hanyar bata dama tayi aikinta yadda ya kamata da kuma wanke dattin shara da zai iya taruwa ya zama dutse a cikin koda.

 Daina shan giya ko barasa. Barasa tana daga cikin abubuwan da ke kawo lalacewar koda don haka daina shan ta zai taimaka wajen rage hadarin kamuwa da ciwon koda(2).

Kammalawa

Acikin wannan rubutu munga illolin ciwon koda da kuma yadda mutum zai kare kansa daga kamuwa da wannan ciwon. Domin neman karin bayani kuyi tambaya a cikin akwatin sharhi da ke Æ™asa zamu karba muku cikin gaggawa da yardar Allah. Domin samun cikakken bayani a harshen turanci ku duba bayanin da wannan babban shafin 

Idan mai kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake Æ™asa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 

Nassoshi 



Post a Comment

0 Comments