Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Bayani game da ganin jini a cikin ruwan maniyyi (Haematospermia)

 Gabatarwa

Ganin jini a cikin maniyyi na iya sanya mutum cikin damuwa.  Abin farin ciki, yawanci ba ya nuna alamar babbar matsalar ko rashin lafiya.  Ga mazan da ke ƙasa da shekarau 40 kuma basu da wasu matsaloli masu alaƙa da ganin jini a cikin maniyyi, ko kuma wasu abubuwan haɗari na yanayin rashin lafiya, jini a cikin maniyyi yakan ɓace da kansa ba tare da sunyi wani magani ba(1). Amma ga maza yan shekaru 40 zuwa sama, ganin jini a cikin maniyyin su yana buƙatar kulawa ta musamman, don haka wajibi ne su hanzarta ganin likita ba tare da jinkiri ba.  Wannan dole ne musamman ga maza waɗanda(1):
 •  Ke yawan ganin jini a cikin maniyyi
 • Samun alamomi masu alaƙa yayin yin fitsari ko fitar maniyyi
 • Suna cikin haɗarin kamuwa da ciwon dajin prostate. 
 • Suna fama da matsalar zubar jini da dai sauransu(1).

Mene ne haematospermia?

 Haematospermia shi ne kalmar likitanci da ake amfani da ita wajen nuna ganin jini a cikin ruwan maniyyin namiji. Yawancin lokaci ganin jini a cikin maniyyi ba ya zuwa da zafi ko ciwo, amma ganin jini a cikin maniyyi na iya zama mai ban tsoro. Amma duk da haka ganin jinin sau ɗaya yawanci ba abin damuwa bane(2).


 Abu ne mai wahala a gane yadda cutar haematospermia ta zama ruwan dare domin mutane dayawa ba sa kallon maniyyinsu bayan sun fitar da shi. Mutanen da suka lura da jini a cikin maniyyin su mafi yawanci ba za su iya magana da likitan su ba saboda suna jin kunya ko tsoro(2).

Matsalar haematospermia tana iya zama ruwan dare ko kuma gama gari a cikin maza a ƙarƙashin shekaru 40, amma bayanan da ake samu ba abin dogaro bane. Daga cikin fiye da maza na Amurka 26,000 da aka yi wa gwajin cutar kansar prostate (yan shekaru 40 ko sama da haka), kashi 0.5 ne kawai ke ganin jini a cikin maniyyin su. 

 Alamomin haematospermia (jini a cikin maniyyi)

 Jini a cikin maniyyi na iya fitowa a matsayin saren jini a cikin ruwan maniyyi mai haske, ko kuma dukkan maniyyin naka yana iya rikida ya zama kalar jini.

 Jini ja mai haske sabo ne kuma ana ganin sa ne saboda zubar jinin da vai dade da aukuwa ba daga magudanan jini, yayin da jini launin ruwan kasa ko baƙar fata ya tsufa kuma yana nuna ɗan lokaci ya wuce tun lokacin da zubar jinin ya faru(2).

 Idan kun wuce shekaru 40 kuma an lura da haematospermia na tsawon lokaci, yana iya zama alamar matsala da ke buƙatar magani, musamman ma idan kuna da wasu alamun cututtuka irin su ciwo ko matsala yayin fitsari.

Abubuwan da ke haifar da jini a cikin maniyyi 

 Jini a cikin maniyyi zai iya fitowa daga wurare daban-daban kamar haka:

 Kamuwa da infection. Wannan shine mafi yawan sanadin ganin jini a cikin maniyyi.  Jini na iya fitowa ta hanyar kamuwa da cuta ko infection, a cikin kowane daga cikin gland, tubes, ko ducts waɗanda ke samar da ruwan maniyyi a jiki.  Waɗannan sun haɗa da(2):

 • Prostate (Gland ne da ke samar da sashin ruwa mai yauƙi na maniyyi).
 • Urethra (bututun da ke ɗauko da fitsari da maniyyi daga azzakari zuwa sararin waje).
 • Epididymis (Wani kwararo ne mai kama da bututu inda halittun haihuwa na maniyyi ke girma kafin fitar maniyyi).
 • Vas deference; Wani bututu ne dake ɗauko maniyyi daga epididymis zuwa cikin azzakari lokacin inzali).
 •  Semal vesicles (Gland ne da ke kara ruwa mai kauri a cikin maniyyi a lokacin da yake fita).

 Hakanan ganin jini a cikin maniyyi yana iya fitowa daga STI (cututukan da ake ɗauka ta hanyar jima'i) kamar gonorrhea ko chlamydia, ko kuma daga wani ƙwayar cuta ko infection.  Kamuwa da infection shi ne abinda yafi komai kawo matsalar ganin jini a cikin maniyyi(3).

 Rauni ko aikin likita.  Ganin jini a cikin maniyyi ya zama ruwan dare a cikin wadanda akayiwa aikin asibiti a cikin mara. Misali, kusan kashi hudu cikin biyar na maza na iya samun jini na wani dan lokaci a cikin maniyyinsu sakamakon biopsy na prostate.

Haka kuma, aikin tiyata da ake yi a domin magance wasu matsalolin fitsari na iya haifar da rauni mai sauƙi wanda zai iya haifar da zubar jini na ɗan lokaci.  Wannan yawanci yana ɓacewa cikin makonni kadan bayan anyi aikin.  Magungunan Radiation, Vasectomy, da allura don basur na iya haifar da jini.  Rauni ga sassan jima'i bayan karyewar kugu, rauni ga al'aura, matsanancin yin jima'i dayawa ko istimna'i, ko wani rauni yayin wasa da al'aura na iya haifar da jini a cikin maniyyi(3).

Toshewa. Toshewar duk wani karamin bututun da ke cikin al'aura na iya sa hanyoyin jini su fashe su saki ƙananan jini.  Haka kuma yanayin da ake kira BPH, wanda ke sa gland din prostate ya kara girma kuma ya toshe bututun fitsari yana iya haifar da jini a cikin maniyyi.

 Ciwon daji ko kansa. Ɗaya daga cikin bincike na marasa lafiya sama da 900 masu jini a cikin maniyyi ya gano cewa kawai 3.5% ne a zahiri suke fama da ciwon daji.  Yawancin waɗannan ciwace-ciwacen sun kasance a cikin prostate.  Jini a cikin maniyyi na iya zama sanadiyyar  kansar 'ya'yan marina, mafitsara, prostate, da sauran gabobin jima'i da na fitsari.  

 Wasu matsalolin kiwon lafiya.  Yanayin rashin lafiya kamar, hawan jini mai tsanani, cutar tsida HIV, ciwon hanta, cutar sankarar bargo, da sauran yanayin kiwon lafiya suna iya haifar da jini a cikin maniyyi.

 Kimanin kashi 15% na cututtukan jini a cikin maniyyi ba za a iya alaƙanta su zuwa ga wani sanannen dalili ba. Mafi yawanci wannan matsalar tana da iyaka. Ma'ana jinin da ke cikin maniyyi yakan tafi da kansa ba tare da magani ba(3).

Wasu alamomin rashin lafiya masu alaƙa da ganin jini a cikin ruwan maniyyi

 Lokacin da likita yake neman gane tushen dalilin jini a cikin maniyyi, yakan yiwa marar lafiya tambayoyi game da duk wani alamun da ke da alaƙa da ganin jini a cikin maniyyi. Alamomin sun hada da(3):

 •  Jini a cikin fitsari (wanda ake kira hematuria)
 • Zafi, kona fitsari ko wasu alamomin fitsari mai raɗaɗi
 •  Wahalar fitar da fitsari gaba daya
 • Yunkuri yayin fitsari 
 •  Mafitsara mai raɗaɗi wanda ke jin tashe
 • Fitowar maniyyi da ciwo ko zafi
 • Kumburi ko kurajen a kan al'aura
 • Fitar farin ruwa daga azzakari ko wasu alamun infection.
 • Zazzaɓi
 • Hawan jini sama da na al'ada

Kammalawa 

 Haematospermia ko kuma ganin jini a cikin maniyyi abu ne da zai iya tada hankalin mai shi, amma mafi yawanci ba abu ne dake faruwa saboda wani mummunan rashin lafiya ba. Amma duk da haka idan kun ga jini a cikin maniyyi, ya kamata ku je ku ga likitan ku game da shi, saboda akwai abubuwa masu haɗari da zasu iya haifar da hakan.

Idan mai kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake ƙasa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 

Nassoshi


3. Jawabin da WebMD sukayi game da haematospermia

Print this post

Post a Comment

0 Comments