A yau ina so na taba abin da ya shafi tsokano sha'awa a auratayya, musamman sha'awar namiji. Dayawa daga cikin mata suna ganin cewa wasa da motsa sha'awa aikin namiji ne shi kaɗai, duk matar da take tunanin haka ta faɗi jarrabawa a fagen soyayyar zamantakewar aure, kuma wata mata a waje zata iya kwace mata miji cikin sauƙi
Galibin maza sunfi so da karkata wajen matar da take musu wasannin motsa sha'awa kala-kala. Don haka kar kiji kunya ko gudun kar mijin naki yace kina da jaraba, ba haka bane, kar kiyi wannan tunani sam. Kisani cewa saduwar aure ibada ce kuma duk lokacin da zaki yiwa mijin ki wasa a lokacin saduwa ke ma fah kina samun wani kaso na jindaÉ—i da nishaÉ—i.
Kamar yadda nayi bayani a sama, yau zan yi bayani ne akan kwanciyar aure, amma kafin mu fara 'yar uwa ina so idan aka zo irin wannan harkar toh ki cire kunya ki ajiye ta a gefe. Dalilin da yasa nace haka shi ne, abin da ke cutar damu mu Hausa-Fulani kenan kunya a wajen zamantakewar aure.
Tabbas mun san cewa kunya ado ce ga 'ya mace, amma ba a shimfiÉ—ar miji ba, in aka je shimfiÉ—a, aje kunya ake yi har sai komai ya kammala, da anyi magana akan wata kwanciyar auren zaki ji matan Hausa-Fulani na cewa walLahi ni ba zan iya ba kunyar shi nake ji, amma za ta iya tsayuwa a gaban shi yana faÉ—a tana faÉ—a a nan bata jin kunya sai a gun kwanciyar aure, Allah ya shirya mana su.
A yanzu za mu fara ne da sirrin kwanciyar aure kafin mu kawo muku kalolin kwanciyar, ma'ana sirrin yadda za ki kwanta da mijin ki har ki gamsar da shi ke ma kuma ki gamsu. Sau da yawa zaku iya samun mace bata da aiki sai amfani da kayan mata, ko nawa ne wata zata kashe ta siya, maganin mata da suka dace da waÉ—anda ba su dace ba, har ta jawa kanta wata cutar, garin neman kiba a kwaso rama.
Lallai kayan mata gaskiya ne kuma suna ba da tasu gudunmawa sosai wurin jima'i amma Bahaushe yace in kana da kyau ka ƙara da wanka, kuma yanxu komai na duniya an samu cigaba, domin masana ilimin jima'i kullum sai ƙara bincike suke yi.
Sau da yawa muna samun ƙorafi daga wasu mata cewa su sun kasa ganewa, suna jin ana cewa namiji na fita hayyacin sa a lokacin jima'i har ya dinga yin surutai yana ihun daɗi, amma sufa hakan ba ya faruwa akan su. Toh 'yar uwa ki saurara ga sirri.
Zama za kiyi ki koyar da kanki wannan ilimin na saduwar aure, yadda za ki dinga sarrafa farjin ki, ki tsukeshi sosai da kanki, ta yadda in mijin ki ya shiga da azzakarin sa, za ki riƙe shi gam a cikin shi.
Akwai wata halittar tsoka a saman kofar farjin ki wadda take tashi ta miƙe yadda ki ka san azzakari, yayin da ki ka faɗa a cikin sha'awa mai ƙarfi, ko kuma lokacin da ki ke kokarin tsuke farjin naki. A lokacin da ogah ya shigar da azzakari a cikin farjin ki dama kin riga kin tsuke farjin naki, toh wannan tsokar zaki koyi motsi da ita ta yadda yayin jima'i za ta dinga gugar kan azzakarin mijinki, da ke da shi za ku ji ku a cikin wata duniya mai wuyar fassara wa.
Mun nema muku sunan wannan tsokar amma ko wanne masanin da yadda yake kiranta a hausance, shi yasa bamu rubuta sunan ba kuma fahimtar tsokar yafi amfani, amma da turanci ana kiranta da Clitoris.
Bincike ya nuna mafi yawan matan Hausa-Fulani ba sa amfani da salon kwanciyar aure. Kuma bincike ya nuna wannan salon kwanciyar jima'i kabilu na amfani dashi sosai, shiyasa matar da mijin ta yake neman matan ƙabilu ba zai taba bari ba sai dai wani ikon Allah, komai ya samu akan su zai ƙare, kina xaman aure amma wata ke juya miki miji a waje
Bincike ya nuna cewa duk matar dake wa mijinta irin wannan salon kwanciyar aure, duk matar da ya kwanta da ita sai ya ji ita ta fita daÉ—i, sai dai kiji ana cewa, ai mijin tace ne ta mallake shi, alhali ba boka ba mallan sirrin kwanciyar ne kawai.
Muhimmin Abubuwan Dake Motsa Sha'awar Namiji
Kamshi
Kamshi yana bada gudunmawa sosai gurin kwanciyar aure domin yana taimakawa gurin saurin tada sha'awar namiji, kuma ya kwantar masa da hankali. Idan son samu ne a duk lokacin da zaki kusanci mijin ki ki kiyaye saka turare ɗaya mai ƙamshi. Idan kina haka tohm ko a waje mijinki yaji kalar ƙamshin turaren ki toh sai hankalinsa ya tashi.
Kalaman Soyayya
Kalaman soyayya da kauna suna tada sha'awa tare da kwantar da hankali.
Iya Sarrafa Jikin ki
Iya sarrafa kwankwaso a wurin mace yana karama kwanciyar aure armashi sosai.
Wasannin Motsa Sha'awa
Wasannin motsa sha'awa suna bada gudunmawa gurin gamsar da masu kwanciyar aure, amma in mijin ki yana saurin inzali toh ku dinga taƙaita wasanni, in ba haka ba zai iya kawowar farko tun kamin ya shiga a farjin ki.
Sumbatar baki (Kiss)
Kiss watau sumbata shi ma yana taka rawar gani gurin tada sha'awa, tare da bada natsuwa, ya kasu kashi-kashi in mun zo kanshi za muyi bayani.
Saka Tufafi Masu Jan Hankali
Shigar kayan jan hankali yana ƙara miki ƙima a idon mijin ki kuma yana rage miki shekaru a idon shi.
Kallo
Kallon jan hankali shi ma da tashi gudunmawar gurin namiji domin kallo kawai yana iya isar da saƙonni dayawa.
Gyaran ÆŠaki
Ki dinga gyara gadon ki kar ki bar shi a wargaje kamar makwancin birai, mijin ki zai raina miki hankali ya kamata kullum ya sami gadon ki a gyare, kuma da ya sauka ko da toilet ya shiga kiyi ƙoƙari ki sake gyara shi kafin yadawo.
Iya Tafiya
Idan zaki yi tafiya kuma kin tabbatar yana gurin ko ma yana kallon ki daga gurin da yake, toh ki dinga tafiyar da za ta ɗauke masa hankali zuwa gare ki. Misali ki dinga tafiya kamar baki son taka ƙasa. Wani lokaci ki dinga tafiya kina karairaya kina jujuyawa jikin ki.
Wani lokacin kuma sauri-sauri zaki dinga yi kina juya mazaunan ki, idan kuma ta gaba yake kallon ki, toh ki san yadda zaki dan dinga girgiza ƙirjin ki cikin hikima ba ta sigar da zai gane da gangan kike yi ba.
Da yamma kuma ya dace ya dawo ya same ki da wasu kaya na daban. In mai shawar English wears ne, ki dinga saka masa, in ko baya son English wears to ki dinga saka normal kayan ki amma fa su É—ame jikin ki sosai.
Rubutu Masu Alaqa
1. Jin Zafi Yayin Saduwa: Abubuwan da Ke Kawowa da Kuma Yadda Ake Maganin sa
2. Yadda Ake Shirin Saduwar Aure: Abubuwan Da Ya kamata Mata Suyi Kamin Saduwa Da Namiji
3. Ire-iren Azzakari Da Sahihan Bayanai Akan Azzakarin Namiji
4. Shin Rashin Aure Yana Sa Gaban Mace Budurwa Ya BuÉ—e Bayan Wasu Shekaru?