Kalmar likitanci ta 'Dyspareunia' ta na nufin zafi ko raÉ—aÉ—i ko ciwo a al'aura yayin da ake daf da fara saduwa ko a lokacin da akeyi ko bayan an gama yin jima'i.
Ga mata, jin zafi yayin saduwar aure zai iya zamo wa daga wajen farji ne (externally) wanda ya ƙunshi laɓɓa guda biyu da su ke rufe da mashigar farji (labia majora and labia minora), ko dan-tsaka (clitoris), ko farkon ramin farji (vaginal canal).
Zafin zai iya zamo wa kuma daga can cikin farjin ne (internally), wanda ya ƙunshi bakin mahaifa (cervix), ko mahaifa (uterus), ko mara (pelvis).
Ga maza, jin zafin zai iya zamowa a kan azzakari ne (glans penis), ko bututun azzakari (corpus cavernosa), ko mara (pelvis).
Abubuwa dayawa kamar rashin sabawa da jima'i, rashin ni'ima, yanayin rashin lafiya ko wasu cututtuka ne ke haifar da jima'i mai raÉ—aÉ—i, kuma mafi yawanci ana magance wannan matsalar ne ta hanyar gano ainihin abin da ke haifar da ciwon.
A likitanci, jin zafi yayin saduwar aure an kasa shi gida biyu kamar haka:
- Jin zafi ko ciwo yayin fara saduwa
- Jin zafi ko ciwo a lokacin da ake yin saduwar aure
Jin zafi yayin fara saduwar aure
Wannan shi ne jin zafin da mace ke yi a al'aura yayin fara saduwa, a lokacin da namiji yake neman shigar da azzakarinsa a cikin farji. A likitanci ana kiran wannan irin jin zafi yayin shigar azzakari a cikin farji da 'Superficial Dyspareunia '.
Irin wannan jin zafi shi ne mafi akasari, kuma kusan ko wace mace za ta iya samun shi a wani lokaci na rayuwar ta na jima'i, musamman mata masu ƙananan shekaru da kuma sabbin fara jima'i.
Haka kuma, irin wannan jin zafi yayin jima'i ana jin sa ne a bakin kofar farji da kuma wajensa ba a jinsa ta chan ciki sosai ko a cikin mara.
Me Ke Kawo Jin Zafi Yayin Fara Saduwa
Mafi yawancin abubuwan da ke kawo jin zafi yayin fara saduwar aure ba su da alaƙa da wata cuta ko wani rashin lafiya, kuma ba abubuwa ne masu bukatar magani ba. Abubuwan da likitoci suka ayyana da kawo wannan irin jin zafi yayin saduwa su ne:
1. Jima'in farko ga budurwa - Virginity loss
Wannan zafin ciwo ne na gama gari, ko wace mace tana samun sa, sai dai na wasu yafi na wasu. Saduwar aure a daren farko baya da daÉ—i ga mace, saboda saduwa ne da zai fara buÉ—e mata kofar farji. Zafin zai cigaba da ragewa sannu-sannu har mace ta saba.
2. Rashin wasa da mace kamin fara saduwar aure- Poor foreplay
Wannan shi ne babban abin da ake alaƙanta wa da wannan matsalar ta jin zafi yayin saduwa. Ya kamata ma'aurata su gane cewa, ita mace kamin jikin ta ya shirya wa yin jima'i dole ne sai an motsa mata da sha'awa.
A lokacin da sha'awar mace ta motsa a lokacin ne kadai za ta iya samar da sinadarai da ruwan da zai dararo daga mahaifar ta domin samar da ni'ima a cikin farjin ta, sauƙaƙa shigar azzakarin namiji a cikin farji da kuma inganta jin dadin jima'i.
Rashin samar da wannan ni'ima a cikin farji yana sanya wahalar shiga azzakari a cikin farji da kuma haifar da ciwo da zafi yayin fara saduwa ba ga mace kadai ba har da ma namiji.
An so na namiji yayi wasa da mace tare da luguiguita ta kamar na minti goma zuwa minti goma sha biyar kamin yayi kokarin shigar da azzakarinsa a cikin farjin ta.
Wannan shi ne zai ba jikin mace damar da zai shirya wa yin jima'i sannan ya samar da isasshen ni'ima.
3. Rashin ni'ima - Vaginal Dryness
Akwai wasu mata, duk yadda sha'awar su ta motsa, duk yadda namiji yayi wasa da su, farjin su baya samar da isasshen ni'imar da za ta sa suji dadin saduwa. Wasu matan haka Allah ya halicce su, wasu kuma cututtuka ne ke sa farjin su bushewa, kamar cutar sanyin mara.
4. Samun rauni ga al'aura - Genital trauma
Wannan shi ma wani abu ne da ke kawo jin zafi yayin fara saduwar aure. Jin rauni a al'aurar mace yayin haihuwa, ko aikin tiyatar asibiti, ko wasu al'adu na gargajiya kamar kaciyar mata, yankan gishiri ko yankan gurya duk suna kawo jin ciwo yayin fara yin jima'i, watarana ma su hanawa mace jin dadin rayuwar jima'i baki daya.
5. Cututtukan al'aura - Genital Infections
Wasu cututtukan al'aura da kuma fatar al'aura kamar irin su kurajen gaba, ƙazuwa kwarkwatar gaba, da dai sauransu, suna kawo ciwo yayin fara yin jima'i.
6. Ƙanƙamewar tsokokin farji - Vaginismus
Wannan wani al'amari ne da wasu mata ke samu a lokacin da zasu fara jima'i, tsokokin farjin su zasu ƙanƙame gaba daya su rufe kofar farji sosai ta yadda namiji ba zai iya shigar su ba, idan ma ya samu shiga kamin al'amarin ya faru, ko kuma yana ciki abin ya faru, to ba zai iya fita da kansa ba har sai abin ya lafa. Wannan yafi faruwa a lokacin da mace ke cikin tsoro, ko shakka ko kuma bata son yin jima'in, sannan ba ko wace mace ke samun irin wannan al'amari ba.
Wannan ƙanƙamewar tsokokin farji (Vaginismus) al'amari ne mai tsananin ciwo ga mace har da namiji. Idan kun taba jin wani labari kamar almara ana cewa wasu suna jima'i sun laƙe sun kasa fita da juna, toh ba almara bace, wannan yana faruwa idan vaginismus ya faru a lokacin da namiji ya riga ya shigar da azzakarinsa a cikin farji.
A lura cewa, mace bata iya yin vaginismus da kan ta, hasali ma bata da wani iko da faruwar sa, vaginismus yana cikin abubuwan da bature ke kira involuntary actions. Wannan shi yasa idan ya faru ko mace taso ta sake namiji ya fitar da azzakarinsa ba za ta iya ba. Shi kuma namiji, ciwo ba zai bar sa ya ja azzakarinsa da ƙarfi domin ya kubuce ba. Haka zasu tsaya sai yadda hali yayi, har sai abin ya lafa.
Jin zafi a lokacin da ake yin saduwar aure
Shi kuma wannan jin zafi yayin saduwa kashi na biyu yana faruwa ne bayan an fara yin jima'i, ma'ana, namiji ya riga ya sanya azzakarinsa a cikin farji ba tare da wani zafi ko raÉ—aÉ—i ba. Amma a lokacin da namiji yake bakin aiki, sai mace ta fara jin ciwo, raÉ—aÉ—i ko kuma mummunan zafi a chan cikin farjin ta, ko a cikin marar ta ko ma a bayan kunkuminta. Ana kiran wannan irin jin zafi yayin jima'i da "Deep Dyspareunia" a likitanci.
Me Ke Kawo Jin Zafi a Lokacin da Ake Yin Saduwar Aure
Irin wannan jin zafi wanda ke faruwa a lokacin da aka riga aka fara yin saduwa, shi ne mafi akasari ke da alaƙa da cututtuka da kuma raunin da aka ji ga al'aura. Abubuwan da ke kawo shi sun haɗa da:
1. Soka azzakari da zurfi sosai a cikin farji: A lokacin da azzakarin namiji ya shiga sosai a cikin farji har ya kai ƙoli to zai fara zuzar bakin mahaifa da kuma bangon farji na ciki a yayin jima'i. Wannan yakan sanya mata jin zafi sosai.
2. Cutar Sanyin Mata - Pelvic inflammatory disease: Cutar sanyin mata cuta ce da ke haifar da zubar wani mummunan ruwa mai wari da yauqi daga gaban mace, haka kuma tana haifar da ciwon mara da kuma jin zafi bayan fara yin jima'i.
3. Cutar endometriosis: Endometriosis wata cuta ce da ke faruwa sakamakon samun tantanin halittun bangon mahaifa na ciki, a wani gurin da ba bangon ba. Idan aka samu wadannan tantanin halittun a cikin kunkumi ko mara suna haifar da ciwo a lokacin jima'i.
4. Jin rauni a al'aura - Genital trauma: Munyi bayanin wannan a sama.
5. Matan da aka yiwa fyade; Wasu mata idan aka yi musu fyade da farko, toh har abada ba za su kara sha'awar jima'i ba.
6. Matan da suka daina yin al'ada - Postmenopausal women: Matan da suka yi tsufan da ya kai su daina yin jinin al'ada sukan samu raguwar sinadaran jima'i na mata da ake kira estrogen da progesterone. Hakan yakan sa sha'awar su ta ragu, ni'imar su ta É—auke ko ma farjin su ya bushe. Wannan yana hana su jin dadin jima'i baki daya.
7. Sauran cututtuka masu iya kawo rashin jindadi ga mata yayin jima'i sun hada da; Ƙarin mahaifa, cutar adenomyosis, cutar irritable bowel syndrome, da dai sauransu.
Amma ya kamata mu gane cewa tsananin tsawo ko girman azzakarin namiji bai zai zamo dalilin jin zafin saduwar aure ba, sai idan hakan ya haÉ—u da rashin ni’ima sakamakon rashin gamsasshen wasannin motsa sha’awa.
Dalilin haka shi ne Allah SwT ya halicci farjin mace da yanayin buÉ—ewa (elasticity) a lokacin saduwar aure domin ya iya daukar duk wata al’aurar namiji komai girman ta. Zamu iya yarda da hakan ta ganin yadda jariri yake iya fitowa ta cikin farjin mace. Nasan kuwa mawuyaci ne a sami al’aurar namijin da ta kai girman jariri.
Rabe-Raben Jin Zafi Yayin Saduwa Ga Mata
1. Wanda mace take jin sa tun lokacin da tayi aure ko kuma tun lokacin da aka fara saduwa da ita kuma bai daina daga baya ba (primary dyspareunia). Abubuwan da suke haddasa shi su ne:
- Cututtukan al’aurar mace (female vaginal infections)
- Cututtukan sanyin mara na mata (PIDs)
- Ƙarin mahaifa (uterine fibroids)
- Makalewar halittun mara a jikin juna (pelvic adhesion)
- Rashin daidaituwar sinadaran hormones na mata (hormonal imbalance)
- Rashin kwanciyar hankali a rayuwar aure (marital psychological factors)
2. Jin zafi yayin saduwa wanda mace ta fara jin sa daga baya alhalin da chan ba haka take ba (secondary dyspareunia). Abubuwanda suke haifar dashi iri daya ne da na primary dyspareunia. Abin da yake Æ™ari akai shi ne gabatowar É—aukewar al’ada (menopause).
3. Jin Zafin saduwa wanda mace take jinsa a duk lokacin da mijinta yake saduwa da ita (complete dyspareunia): Shi ma duk abubuwanda suke haifar da primary da secondary dyspareunia su ne suke kawo shi.
4. Jin zafin saduwa wanda mace take jinsa lokaci-lokaci (situational dyspareunia). Shi ne wanda mace take jinsa a wasu keɓantattun lokuta, kamar salon saduwa (sex style).
Jin Zafin Saduwa Ga Namiji
Shi kuma jin zafin saduwa ga namiji yana faruwa ne saboda wasu dalilai kamar haka:
1. Nakasar fatar kan mazakuta (foreskin damage) wanda yake faruwa saboda rashin damshi a lokacin saduwa, ko kuraje a wurin. WaÉ—anda aka yiwa kaciya basu samun irin wannan matsala.
2. Kamuwa da cututtukan da ake É—auka a lokacin jima’i (sexually transmitted infections - STIs) kamar cutar herpes ko cutar gonorrhea.
3. Nakasa a halittar mazakuta (penile deformity) kamar karkacewar mazakuta (peyronie’s disease).
4. Rashin kwanciyar mazakuta bayan gama saduwar aure (priapism), wanda yakan faru saboda rashin fitar jini daga mazakuta bayan an gama saduwar. Don haka mazakutar za ta kasance a mike lokaci mai tsawo, sai mutum ya rika jin zafi sosai.
Yadda Ake Maganin Jin Zafi Yayin Saduwa
Maganin jin zafi yayin saduwa ya danganta da abin da ya kawo shi kamar yadda mukayi bayani a sama. Amma zamu zaƙulo hanyoyin gama gari da ake bi domin maganin wannan jin zafi yayin jima'i a taƙaice.
1. Yin saduwar aure sannu a hankali ba tare da hauka ba, musamman idan mace budurwa ce, ko kuma kwanciyar aure ta farko tsakanin ango da amarya. Haka kuma ba'a so namiji ya kama soka azzakarin sa da karfi sosai har yadda zai kama zuzar bakin mahaifa. Koda dole sai anyi shige da fice da karfi toh kar a bari ya kai ga bakin mahaifa.
2. Maza su daina amfani da maganin ƙarfin maza. Magungunan karfin maza na gargajiya da na bature suna ɗaya daga cikin abubuwan da ke sa maza suyi ta saduwa na ƙarfi har su sanya mata daina jindadin saduwa su koma jin zafi da ciwo.
3. Yin wasa da mace, tare da luguiguita ta da kuma shafata na akalla minti goma zuwa sha biyar kamin a fara sanya azzakari a cikin farjin ta. Wannan shi ne zai motsa mata sha'awa har ta samar da ni'ima.
4. Amfani da man shafawa ko kirim kamin sanya azzakari a cikin farji, wannan hanyar ana amfani da ita ga mata marasa ni'ima, budurwa a yayin jima'in farko har sai ta saba da kuma matan da suka daina yin al'ada. Wannan man shafi yakan samar da wata gagarumar ni'ima da santsi domin inganta jin dadin jima'i. Akwai man shafawa da kirim na musamman da ake amfani dasu, kamar irin su, Night secret, KY jelly da Xylocain gel.
5. Magance cututtuka masu kawo jin zafi yayin jima'i kamar irin su cutar sanyin mara da dai sauransu.
6. Jiyyar raunuka da aka samu a al'aura ta hanyar haihuwa ko wani abu. Musamman dinkin da ake yiwa mata bayan sun samu ƙari a wajen haihuwa. Ana so mace rika yin gashi da ruwan zafi kuma ta yi jiyyar wurin da kyau har sai ya warke sarai kamin ta fara jima'i.
7. Kai matan da akayi yiwa fyade gurin likitocin ƙwaƙwalwa domin su basu shawarwari akan hanyoyin da zasu bi domin su tafiyar da rayuwar su ta jima'i.
Kammalawa
A nan muka zo karshen wannan rubutu, muna fatar kun amfana, idan mai karatu yana da wata tambaya to ya hanzarta rubuta mana a cikin akwatin sharhi da ke ƙasa. Insha Allah zamu karba masa bada dadewa ba.
Nassoshi
1. https://www.mayoclinic.org/diseases-conditions/painful-intercourse/symptoms-causes/syc-20375967
2. Bergeron, Sophiea,b,*; Rosen, Natalie O.a,c; Morin, Mélanied. Genital pain in women: Beyond interference with intercourse. Pain 152(6):p 1223-1225, June 2011. | DOI: 10.1016/j.pain.2011.01.035
3. Elmerstig, E. (2009). Painful Ideals : Young Swedish women´s ideal sexual situations and experiences of pain during vaginal intercourse (PhD dissertation, Linköping University Electronic Press). Retrieved from https://urn.kb.se/resolve?urn=urn:nbn:se:liu:diva-20277
0 Comments