Bayanin Saduwar Aure Da Yadda Ake Daukar Ciki (Conception)

Gabatarwa:

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ƙiyasta cewa, duk bayan minti ɗaya aƙalla mata goma sha biyu (12) suna daukar ciki a ƙasar Nigeria. Kwanciyar aure ko kuma saduwar aure abu ne mai matuƙar muhimmanci a rayuwar ɗan adam domin ta wannan hanyar ne jinsin ɗan Adam zai ci gaba da wanzuwa a doron kasa. 

Duk da cewa, a kimiyyance ana iya samun haihuwa ba tare da namiji da mace sun haɗu sun sadu da juna ba, watau ta hanyar da bature yake kira "assisted reproductive techniques", toh amma hanyar saduwar aure itace hanya ta asali kuma hanya mafi sauƙi da ɗan adam zai bi domin cigaba da samar da jinsin sa a doron ƙasa[¹].

Ba ɗorewar jinsi kaɗai ba, saduwa tana da amfani ga jikin ɗan adam kamar rage ƙishirwar sha'awa da ke damun samari da 'yan mata, inganta lafiyar ƙwaƙwalwa, ƙara ƙarfafa garkuwan jiki da kuma taimakawa wajen daidaita wasu sinadaran hormones a jikin mutum[¹].


Sassan jima'i a jikin ɗan adam

Sassan jima'i wasu gaɓoɓi ne a jikin dan adam da ake amfani da su ko kuma suke taimakawa wajen saduwa ko yiwa mace ciki. Waɗannan gaɓɓai sun bambanta tsakanin mace da namiji[¹].

Sassan jima'in namiji:

  • Penis : Azzakari
  • Testes :Ƴaƴan marina
  • Scrotum : Fatar da ke ɗauke da ƴaƴan marina
  • Urethra : Bututun da ke fitar da fitsari da ruwan maniyyi
  • Prostate : Gland ne mai samar da wasu ruwa masu yauƙi
  • Seminal vesicles : Gland ne mai samar da wasu ruwa masu kauri
  • Epididymis: Wani bututu ne dake manne a bayan ya'yan marina, yana ajiye tantanin halittun haihuwa (ya'yan maniyyi) kafin lokacin inzali.
  • Vas deference : Wani bututu ne da ke ɗauko tantanin halittun haihuwa daga epididymis zuwa tushen azzakari a yayin inzali.


Sassan jima'in mace

  • Vagina : Farji
  • Uterus : Mahaifa
  • Ovaries : Gland ne dake samar da ƙwan haihuwa a duk wata(month)
  • Fallopian tubes: Bututun Fallopian wani bututu ne dake ɗaukar ƙwai daga ovaries zuwa cikin mahaifa
  • Clitoris : Dan tsele ko kuma beli
  • Labia majora : Laɓɓan farji manya
  • Labia minora : Laɓɓan farji ƙanana
  • Hymen : Tantanin budurci, yana fashewa da zarar aka fara saduwa da mace.


Yadda ake tsokano sha'awa budurwa ko saurayi

Sha'awar ɗan adam tana motsawa ne a lokacin da ƙwaƙwalwar sa ta karɓi wasu saƙonnin da zasu iya motsa masa sha'awa daga jakadun ƙwaƙwalwar sa dake gangar jiki (idanu, kunne, hanci, baki da kuma jakadun ƙwaƙwalwa dake kan fata)[²]. Misali:

  • 1. Idanu - mutum ya kalli wani abin da zai motsa masa da sha'awa, kamar kallon matarsa, irin kallon sha'awa.
  • 2. Kunne - mutum ya saurari wani abin da zai motsa masa sha'awa, kamar kalaman soyayya ko kalaman batsa.
  • 3. Hanci - mutum ya shinshina wani abin da zai motsa masa sha'awa, kamar turaren matar sa, ko wani ƙamshi da ya saba ji a lokacin da yake jima'i ko yake cikin sha'awa.
  • 4. Taɓi - mutum ya taɓa ko a taɓa masa wani wurin da sha'awar sa zata motsa. Jakadun fata zasu ɗauki saƙon zuwa ƙwaƙwalwar sa. Misali, sumbata, runguma, massaj da shafar jiki.
  • 5. Baki - mutum yaci wani abinda ke motsa masa sha'awa. Ko kuma yaci abincin da matarsa ke yawan kawo masa kamin suyi jima'i. A duk lokacin da yaci irin abincin zai iya jin sha'awar sa ta motsa.
  • 6. Tunani - mutum ya kama tunanin saduwa ko tunanin matar sa ko tunanin batsa. Shima wannan yakan motsa sha'awar ɗan adam.

Me ke sa azzakarin namiji ya miƙe a lokacin sha'awa?

Da farko a duk lokacin da sha'awar ɗa namiji ta motsa ƙwaƙwalwar sa za ta karkatar da samar da isasshen jini zuwa ga azzakarin sa. Azzakari yana ɗauke da jijiyoyin jini da wasu tsokoki na musamman waɗanda za su iya ƙara tsawo kuma zasu iya ragewa. 

Cikar waɗannan jijiyoyin jini a lokacin da zuciya ta karkatar da samar da jini zuwa azzakari shi zai sanya azzakari ya miƙe kuma tsokar jikin sa tayi tauri[²].

Yadda namiji yake kawowa a lokacin jima'i

A lokacin da ake saduwa tsakanin namiji da mace, namiji yana shige-da-fice da azzakari a cikin gaban mace, wasu jakadu dake jikin fatar azzakari zasu ɗauki taɓi da kuma shafar da fatar azzakari ke yiwa fatar farji a matsayin saƙon jindadi na musamman sannan su aikawa ƙwaƙwalwa.

Ƙwaƙwalwar ɗan adam za ta fassara wannan saƙo a matsayin wani jin dadi na musamman sannan ta fara fitar da wasu sindaran hormones. 

A yayin sha'awar namiji yayi nisa, jindadin ya kai ƙololuwa, ƙwaƙwalwar namiji za tayi umurni ga tantanin halittun haihuwa (sperm cells) da ke cikin kwararon epididymis da su kama hanya zuwa cikin azzakari. 

Daga nan zasu kama hanyar su ta cikin vas deference har zuwa tushen azzakari, a yayin da suka zo tushen azzakari daga nan zasu haɗu da wani ruwa da prostate gland ke fitarwa mai yauƙi da kuma wani ruwa mai kauri wanda seminal vesicles ke samarwa. 

Waɗannan ruwan guda uku (tantanin halittun haihuwa da suka taso daga epididymiys zuwa tushen azzakari, ruwan da prostate gland ke fitarwa da kuma ruwan da seminal vesicles ke fitarwa) su ne zasu gauraya su fito ta hanyar azzakari a matsayin ruwan maniyyi lokacin da namiji yake kawowa ko kuma yin inzali.

Waɗannan ruwan maniyyin da namiji yake kawowa a lokacin saduwar aure suna ɗauke da tantanin halittun haihuwa da zasu kai kimanin miliyan talatin da tara zuwa miliyan ɗari biyu(39 - 200 millions) ga lafiyayyen namiji. 

Ko wane ɗaya daga cikin waɗannan miliyoyin tantanin halittun zai iya yiwa mace ciki (juna biyu) idan ya haɗu da ƙwan tantanin halitta ɗaya da macce ke kawowa a duk wata.[²][³].

A lura cewa, a lokacin da namiji yake cikin ƙaramar sha'awa kamin ya fara saduwar aure ko lokacin da ya ke tunanin saduwa, ko yayin wasa da matar sa yakan iya samun wasu ruwa marar kauri suna fito masa daga azzakari (ruwan da ake kira maziyyi da Hausa), waɗannan ruwan gland ɗin prostate ne kawai ba tare da maniyyi ba, su ruwan maniyyi basa fitowa sai a lokacin babbar sha'awar lokacin da namiji yake kawowa, kuma da sun gama fita sha'awar namiji za ta dauke[³].

Yadda ake tsokano sha'awa budurwa ko duk wata mace

Yadda ake tsokano sha'awar budurwa ko duk wata mace shi ne, ta hanyar yin wasa da ita da kuma shafa mata sassan jima'inta waɗanda mun ka ambata a baya. A lokacin da sha'awar mace ta motsa ƙwaƙwalwar ta zatayi umurni ga zuciyarta domin ta samar da isasshen jini zuwa ga al'aurar ta. Samar da wannan isasshen jini zuwa al'aura zai sa al'aurar mace ta kumbura kuma tayi jaa sosai. 

Haka zalika ƙwaƙwalwarta za ta yi umurni ga wasu glands da ke cikin mahaifarta su fara samar da wasu ruwa masu yauƙi, waɗannan ruwan sune zasu gangara zuwa a gabanta domin su samar da ni'ima, da santsi a lokacin da fatar azzakari ke shafar fatar farji. Waɗannan ruwan suna ƙaruwa sosai a duk lokacin da sha'awa da kuma jin daɗin jima'in da mace keyi ya ƙaru[¹][²].


Yadda mace ke kawowa idan taji dadin saduwa 

A lokacin da mace ta kai ƙololuwar jindadin jima'i, ƙwaƙwalwar ta takan yi umurni da fitar da waɗancan ruwan da muka ambata a sama dayawa, fitar da wadannan ruwan da yawa shi ake kira da kawowar mace ko inzalin mata ko fitar ruwan maniyyin mata. Haka kuma fitar wannan ruwan yana kai maƙura ne a lokacin da mace ta kai maƙurar jindadin saduwa.

Amma a lura cewa, waɗannan ruwan da mace ke kawowa a lokacin da ake jima'i da ita har yanzu suna wani babi na mahawara ga masana ilimin kimiyyar ɗan adam. Amma bisa ga magana mafi inganci ruwan da mace ke kawowa basu da wata alaƙa da tantanin halittun haihuwar da take bada gudunmawa domin daukar ciki. 

Saɓanin ruwan maniyyin da namiji ke kawowa daga azzakarin sa a lokacin jima'i, su ruwan maniyyin da mace ke kawowa daga farjinta aikinsu kawai shi ne samar da ni'ima da santsi da kuma inganta jindaɗin saduwa. 

Tunda abin ya zama haka, nasan mai karatu zai so yasan yanda mace ke bada gudunmawa domin samun ciki[²][³].

Yadda ake daukar ciki 

Mace tana daukar ciki ne ta hanyar samar da wani ƙwai dake fitowa daga ovaries dinta, watau yin ovulation. A duk kowane wata (month) mace tana yin ƙwai a cikin ovaries nata wanda yana samuwa ne a tsakiyar watan ta na al'ada, akwai alamomin ovulation da mace ke iya gani a wannan lokaci. 

Hakan zai yi dai dai da rana ta goma ko ta sha ɗaya zuwa ta sha huɗu bayan tayi tsarki daga jinin al'ada. A lura cewa fitar da wannan ƙwai baya da alaƙa da yin jima'i. Har matan da ba'a taɓa yin jima'i dasu ba duk wata sai sunyi wannan ƙwai in dai sun balaga sun fara jinin al'ada[¹][³].

Yadda ake yiwa mace ciki (shigar ciki a jikin mace)

A duk lokacin da mace tayi ƙwai ta fitar dashi ya kan fito daga ovaries dinta zuwa mahaifarta. Idan ta samu nasarar yin saduwar aure a lokacin da ƙwan yake da rayuwa (ƙwan ya kan dauki kwana biyu zuwa uku kamin ya mutu) har ruwan maniyyin namiji ya zuba a cikin farjin ta, toh tantanin halittun haihuwar da ke cikin ruwan maniyyin namiji za suyi tsera domin su je cikin mahaifarta su sadu da ƙwan da ta sake domin a samu ciki. 

Daga zarar tantanin maniyyin namiji ɗaya ya haɗu da ƙwan mace shikenan sauran zasuyi haƙuri, shikenan mace ta dauki ciki. Daga nan kuma maniyyin namiji da kuma ƙwan mace zasu haɗu su zama ƙyanƙyasasshen ƙwai sannan su ci gaba da girma a cikin mahaifa har zuwa haihuwa[³].

Illolin yawan saduwa a jikin namiji 

Duk da cewa saduwar aure yana da amfani a jikin mutum amma yawan yin saduwa barkatai kuma yakan haifar da wasu illoli a jiki. Manyan illolin sun haɗa da;
1. Kamuwa daga cututtukan da ake iya samu ta hanyar saduwa 
2. Yawan mantuwa
3. Jin ciwo yayin jima'i
4. Raguwar ruwan maniyyi
5. Rashin maida hankali akan muhimman abubuwa 

Bayanin rufewa

Saduwar aure abu ne mai matuƙar muhimmanci a jikin ɗan adam, a cikin wannan rubutu munyi tsokaci sosai game da falsafar saduwa tsakanin mace da namiji a kimiyyance. Munyi bayanai tun daga yanda sha'awa take motsawa har zuwa yadda ake daukar ciki. Duk mai tambaya sai yayi ta a cikin akwatin sharhi dake ƙasan wannan rubutu. Insha'Allah zamu karɓa masa.

Nassoshi



3. Shtarkshall RA, Carmel S, Jaffe-Hirschfield D, Woloski-Wruble A. Sexual milestones and factors associated with coitus initiation among Israeli high school students. Arch Sex Behav. 2009 Aug;38(4):591-604. doi: 10.1007/s10508-008-9418-x. Epub 2008 Dec 18. PMID: 19093197.