Akwai matan da suke fahimtar cewa basu kawowa a lokacin jima'i, wanda ake kira "anorgasmia" a likitance. Domin fahimtar wannan yanayin da kuma tasirinsa, ya kamata mu san mene ne ake nufi da kawowa a lokacin jima'i, wanda ake kira "ejaculation" ko "releasing" a turance.
Kawowa shi ne fitar da ruwan maniyyi. Ba dole bane ma'aurata su kawo a lokacin jima'i. Saidai kawowar tana da matukar muhimmanci.
Ga namiji, kawowa tana nuna kaiwa ƙololuwar gamsuwar sa da jima'i, sannan dole sai yayi ta zai iya yiwa mace ciki, domin kwayoyin halittar haihuwarsa (sperm cells) suna a cikin ruwan maniyyi da yake kawowa.
Ga mace kuwa, itama kawowa tana nuna matukar gamsuwar ta da jima'i ne, amma ruwan kawowar ta baya dauke da kwayoyin halittar haihuwar ta (ova).
A kimiyyance, daga lokacin da mace ta balaga zuwa lokacin da al'adarta zai dauke saboda nisan shekaru (menopause), tana samar da kwayoyin halittar haihuwarta (ova) kimanin 300,000 zuwa 400,000 waɗanda ba su ƙosa ba (underdeveloped ova).
Wasu daga cikin su ne za su ƙosa, kuma za ta riƙa fitar dasu a duk bayan lokacin da ta gama al'adarta (ovulation) da kwanaki 13, 14, 15, ko 16, ma'ana lokacin da za tayi ovulation.
Kafin ɗaukewar al'adar mace, za ta yi ovulation kimanin 300 zuwa 400, su kuma sauran ƙwayoyin ova ɗin da ba ta sake su ba, zasu narke su bi jikinta, wannan shi ne ake kira "follicular atresia".
Abin da nake so in nuna anan shi ne, ba dole bane a duk lokacin da namiji yake jima'i da mace ya zamo sai ta kawo, kuma rashin kawowar ta bazai hanata samun juna biyu ba. Amma rashin kawowar mijinta zai iya hana ta samun juna biyu.
Wani lokacin mace zata iya kawowa amma ita ba zata gane ta kawo ba, sai dai mijinta ya gane. Dalilan da zasu iya sanya hakan sune:
1. Bambance-bambancen halitta (anatomical differences)
Wasu mata basu jin fitar ruwan saduwar aure daga gabansu saboda bambance-bambancen halittar jijiyoyin lakarsu (nerve endings) ko kuma yadda jikinsu yake sarrafa jin dadi yayin jima’i.
2. Tunanin zuciya (psychological factors)
Tashin hankali (anxiety), damuwa (stress), ko rashin mayar da hankali ga yadda ake jin dadi a lokacin jima'i yana iya rage fahimtar fitar da ruwa ko samun inzali ga mace.
3. Raguwar jin dadi (reduction of sensitivity)
Canje-canjen zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone a cikin jinin mace, kamar lokacin da ta haihu, ko lokacin da take shayarwa, ko lokacin da shekarunta sukayi nisa, duk suna iya shafar jin daÉ—in jima'i kuma ya haifar mata da raguwar jin abubuwa a jikin ta.
4. Rashin fahimtar fitar da ruwan kawowa (misunderstanding of female ejaculation)
Yawancin lokaci mata sukan rikice su kasa bambanta fitar ruwan santsi (vaginal lubricants) da kuma fitar ruwan kawowa (ejaculate). Hakan zai iya sanyawa mace taga kamar ba ta kawowa, alhalin kuwa tana yi.
Maganin Rashin Kawowa Da Shawarwari
1. Tattaunawa tsakanin ma'aurata
Akwai bukatar mace ta rika tattaunawa tsakanin ta da maigidanta don su fahimci juna da yadda jikin kowannen su yake amsawa yayin jima'i.
2. Mayar da hankali a lokacin jima'i
Mace ta riƙa nutsuwa yayin jima'i tare da mayar da hankalin ta akan yadda take jin abubuwa a jikin ta, ma'ana ta daina tunanin wasu abubuwa can daban a lokacin da take jima'i da mijin ta. Hakan zai taimakawa wajen fahimtar jikin ta sosai da kuma saurin kawowa.
3. Yin atisayen ƙarfafa tsokokin mara
Yin atisaye kamar atisayen Kegel (Kegel's exercise) yana iya ƙarfafa tsokokin mararta da inganta jin dadin gabanta.
A yawancin lokuta, wannan ba wata matsalar lafiya ba ce, sai dai bambancin yadda mace ke jin dadin jima’i. Amma idan akwai damuwa, to, taje asibiti domin ganin likitan mata (gynecologist) domin yayi bincike ya tabbatar da abin da yake faruwa da ita.
Me ke sa ruwan maniyyin da namiji ke kawowa ya tsinke ya zama ruwa-ruwa?
Wannan na daga cikin tambayoyin da ake yawan yi mana. Idan can baya sperm ko maniyyin mutum ya na da kauri sai daga baya ya koma ruwa ruwa, akwai abubuwan da ke sa haka kuma in Shaa Allah ana iya magance su. Rashin magance wannan matsala na sa mutum ya zama ba zai iya haihuwa ba.
Abubuwan da ke sa ruwan maniyyin namiji tsinkewa ya zama ruwa ruwa
1. Yawan jima'i: Idan mutum yana jima'i sosai kuma bai bada lokacin da ruwan maniyyi zai sake taruwa a marar sa, toh ruwan maniyyi din zai fito ruwa ruwa a lokacin da yake kawowa.
2. Yawan istimnai: Wannan ya na sa ruwan maniyyin namiji ya yi ruwa ruwa kamar yadda yawan jima'i ke iya kawo wannan matsala.
3. Infection: Infection ko sanyi a maran namiji shi ma yana sa sperm ya tsinke.
4. Ƙarancin sinadaran zinc a jikin namiji na sa sperm ya yi ruwa ruwa. Idan a ka sha magani ana iya maye gurbin sinadarin zinc ɗin da yake a cikin jini, saboda haka ana warkewa.
5. Ƙarancin kwayar halittar sperm din ya na sa maniyyin ya yi ruwa ruwa, ma'ana ƙarancin halittun haihuwa a cikin ruwan maniyyi oligospermia, ko azoospermia.
6. Wasu maza musamman matasa basu san banbanci tsakanin maniyyi da maziyyi ba. Wannan ya na saka hankalin su ya tashi a lokacin da suka fitar da maziyyi sai su É—auka cewa maniyyin su ne ya tsinke ya koma ruwa ruwa.
Tests da ake yi domin bincikar tsinkewar ruwan maniyyi
1. Sperm count: Wannan shi ne adadin yawan ƙwayoyin halittun haihuwa da ke a cikin ruwan maniyyi. Idan adadin su ya kasa kai ga yanda ake so, shi ke nuna oligospermia, kuma wannan na iya zama dalilin ruwan maniyyin mutum yayi ruwa ruwa ko ya tsinke. Kuma wannan na hana samun ciki.
2. Sperm motility: ma'ana motsi ko gudun ƙwayoyin halittun haihuwa da ke cikin ruwan maniyyi. Idan ya kasance ƙwayoyin sperm din adadin su ko yawan su daidai ne amma kuma basa motsi ko gudu yanda ya kamata ana samun matsala, wannan ma yana iya zama dalilin rashin haihuwa.
3. Sperm shape: ma'ana yanayin halittun ƙwayoyin haihuwa da ke cikin ruwan maniyyi. Ko wane ƙwayar halitta ana buƙatar ya zamo yana da kai, gangar jiki da kuma bindi. Idan Alal misali basu da halitta mai kyau ba za su kaiwa ga wurin da zasu haɗu da ƙwan mace domin a samu ciki.
Yadda ake inganta lafiyar maniyyin namiji
1. Rage damuwa: A lokacin da mutum ke ƙoƙarin gamsar da iyali tare da samun juna biyu a na son namiji ya zamo cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.
2. A guji zafi: Musamman zafin da zai iya shafar mara kai tsaye. Yawan zafi ya na rage lafiya da ingancin ƙwayoyin halittan da ke cikin ruwan maniyyi, haka kuma yana hana musu girma.
3. A nisanci mu'amala da wasu chemicals dayawa irin magungunan kashe ƙwari ko haƙo ma'adanai.
4. A rage kasance wa cikin stress, watau damuwa da tashin hankali da rashin samun isasshen hutu.
5. A kasance da matsakaicin nauyi, ma'ana nauyi madaiddaici. Ka da namiji ya zamo mai rama sosai ko mai ƙiba dayawa.
6. A rage shan giya ko a daina baki É—aya
7. A daina shan miyagun ƙwayoyi, sigari da abubuwan da ke saka maye.
0 Comments