Bayani Game Da Maza Masu Ɗabi'ar 'Yan Daudu (EFFEMINACY)


Assalamu, Alaikum, likita Dan Allah ka taimaka mun da amsar wannnn tambayar, tambaya ta ita ce, shin a likitance akwai wani dalilin da ke sakawa a haifi yaro yazo da halayya irin ta mata? Misali kamar mazan da suke yin daudu, shin halittar su ce tazo a haka koh kuwa su ne su ka mayar da kan su hakan saboda yanayin da suka tashi akai, nagode.

Amsa 

Daudanci shi ne namiji ya riƙa yin ɗabi'u irin na mata, maimakon maza 'yan-uwansa. Daudanci shi ne ake kira "effeminacy" a likitance. Shi kuma dan-daudu ana kiransa "effeminate ".

Dalilai na kiwon lafiya (medical reasons) da kuma dalilai na tunanin ƙwaƙwalwa (psychological reasons), waɗanda suke haddasa daudanci suna da rikitarwa matuƙar gaske, sannan suna da yawa. Kadan daga cikin su sune, kamar haka:

1. Tasirin Rashin Daidaituwar Zubar Ruwan Sinadarai A Cikin Jini (Hormonal Influences)

Rashin daidaituwar zubar ruwan testosterone da estrogen da progesterone a cikin jinin namiji zasu iya yin tasirin canja masa ɗabi'unsa, har ya koma yana yin ɗabi'u irin na mata. 

Yawan sinadaran testosterone da estrogen da progesterone waɗanda ake samun su a cikin jinin maza yana bambanta bisa la'akari da shekaru, koshin lafiya, da sauran su. Amma idan yawan sinadaran ya saɓawa adadin da akafi sani da yawa, toh, hakan zai iya haifar da matsalar daudanci kamar haka:

a.) Yawan testosterone da ake buƙata (normal range) shi ne daga 300-1,000 ng/dL (nanograms per deciliter).

b.) Yawan estrogen (estradiol) da ake bukata shi ne daga 10-40 pg/mL (picograms per milliliter).

c.) Yawan progesterone da ake bukata shine kada ya wuce 1.0 ng/mL (nanograms per milliliter).

Testosterone shi ne sinadarin maza kuma shi ne ke kula da duk wasu halayyar maza ta hanyar balaga, sha'awa, jima'i da dai sauran su. Kamar yadda testosterone ke kula da halayyar maza haka su kuma sinadaran estrogen da progesterone ke kula da halayyar mata.

Tsananin sha'awa, rashin sha'awa, rashin jin dadyin saduwa da sauran ababen dake da alaka da juma'i daga hauhawan waɗannan sinadaran hormones ne testosterone a maza progesterone da estrogen a mata.

Mata da maza suna da duka waɗannan sinadaran hormones na testosterone, estrogen da progesterone. Amma sinadarin testosterone ya rinjaye sinadaran estrogen da progesterone a jikin maza, haka kuma sinadaran estrogen da progesterone sun rinjaye sinadarin testosterone a jikin mata.

Idan namiji yana da ƙarancin testosterone, toh, zai iya zamowa bayada kwanji irin na maza (reduced muscles mass), yawan kitse (increased body fat), da rashin kazar-kazar (reduced energy levels), kuma hakan zai sanya ayi masa kallon dan-daudu. 

Idan namiji yanada estrogen mai yawa, to, hakan zai iya haifar masa da yin manyan nonuwa (gynecomastia), rashin gashin baki da gemu (hypogonadism), da yin manyan duwawu (steatopygia). 

Idan namiji yana da progesterone da yawa, to, hakan zai iya sanya masa dabi'u irin na mata (emotional sensitivity) kamar saurin kuka, raunin zuciya, rashin iya rigima da mutane, da sauransu. 

Abubuwan da suke haddasa rashin daidaituwar wadannan sinadaran su ne kamuwa da cututtukan hanta, cancer, yawan ƙiba, laulayin magunguna, rashin motsa jiki, rashin ci da shan abubuwa masu gina jiki, da kuma gado. 

Ana iya magance rashin daidaituwar zubar ruwan sinadaran ne ta hanyar zuwa asibiti domin likita ya ɗora mutum akan maganin da ya dace, da cin ingantaccen abinci, yin ayyukan motsa jiki.

2. Gado (Genetics)

Mutum yana iya yin gadon ɗabi'un daudanci daga iyaye ko kakanninsa. Ya zuwa yanzu akwai ƙarancin bayanai a kimiyyance akan yadda hakan yake faruwa. Amma masana ilimin kimiyya suna cigaba da yin binciken domin gano yadda al'amarin yake. 

3. Tsarin Da Ayyukan Kwakwalwa (Brain Structure and Functions)

Sakamakon binciken kimiyya ya tabbatar da cewa akwai bambanci a tsakanin kira da ayyukan kwakwalen mace da namiji. Don haka, idan halittar tayi kama da ta mace, bisa ga yadda Allah SwT yayi ta, to, akwai yiwuwar mutum ya rika yin dabi'un daudanci.

4. Tunanin Kwakwalwa Da Yanayin Zamantakewa (Gender Dysphoria, Psychological, and Social Factors)

Idan namiji ya kasance yana tunanin cewa shi kamar mace yake, ko yana sha'awar ɗabi'un mata, ko ya tashi a cikin muhallin da baya hulɗa da maza 'yan-uwansa sai dai mata, toh, akwai yiwuwar ya rika yin ɗabi'un daudanci. Maganin wannan shi ne iyaye su riƙa yin kokarin ganin cewa 'ya'yansu maza suna yin hulɗa da maza 'yan-uwansu.

Kammalawa 

Yanada muhimmanci iyaye su kiyaye ɗabi'un 'ya'yansu. Idan suka ga namiji yana nuna alamun ɗabi'un daudanci, ko kuma mace tana nuna alamomin ɗabi'un 'yan-mazanci, to, su ɗauki matakin gane inda matsalar take, domin daukar matakin da ya dace. Ma'ana, su je asibiti domin ayi bincike a tabbatar da abin da yake faruwa, domin ɗaukar matakin da ya kamata.

Post a Comment

0 Comments