Abubuwan Da Ke Kawo Kurajen Gaba Ko Kumburin Gaban Mace


Aslm Dr Dan Allah nazo tambaya da neman taemako. Banyi magana a grp ba sbd ina da Yan uwa aciki. Dr wani Dan kurjine y fitomin kamar tsuro a gefan farji nah. Yana da Dan girma kadan sannan yana kaikayi lokaci zuwa lokaci. Kuma idan muna sex da oga banajin zafi sai dai idan y dunguri gurin. Nayi ciwan gefen ciki hagu da dama kwanaki sae naje asibiti kawae aka bani magani da allura basu fadamin komai ba. Danasha maganin sosae gabana y Dade amma iya t waje yayi kuraje. Da kansu Kuma suka mutu. Dana gama Shan maganin. Aure n wata4.

Amsa

Ƙurajen gaba da kumburin farji

Amarsu ta ango mai zakin miya. Toh ai matsalarki ta riga ta kare tunda kin ce har kin warke. Amma idan kina neman sanin abinda ya faru dake ne tunda likitan ki bai yi miki bayani ba, to, mawuyacin abu ne mu iya fada miki ainihin abinda ya faru, tunda bamu gani ba, sai dai muyi hasashe, kamar haka:

1. Cutar kurajen fatar gaba na HPV (HPV infection)

Wannan yana faruwa ne sakamakon cutar human papillomavirus (HPV), inda wani dan tsiron fata zai iya fitowa a gaban ki. Yana iya yin É—an kaikayi amma ba ya yin ciwo sai an taba ko idan ana yin jima’i.

2. Toshewar bututun ruwan maikon gaba (Bartholin's cyst)

Idan bakin jakar ruwan maikon Bartholin ya toshe, wacce take makale a gefen bakin farji, hakan yana iya haifar da wani tsiro ko kumburi maras tsanani. Baya yin ciwo, amma zai iya haifar da dan radadi lokacin jima'i ko idan an taɓa shi.

3. Fitar tsiron fata (skin tags)

Tsiron fata na skin tags suna iya fitowa a farji. Basu zamowa masu ciwo, sai dai su haifar da rashin sukuni lokacin jima'i ko dan kaikayi.

4. Zazzagowar fatar farji (vaginal polyps) 

Wannan yana faruwa ne sakamakon raunin tsokoki da jijiyoyin farji. Ba lallai bane ya haifar da jin ciwo, amma yana iya haifar da ƙaiƙayin gaba ko radadi kadan idan aka taɓa shi.

5. Cutar kurajen Molluscum (Molluscum contagiosum)

Wannan cuta ce  wace take haifar da fitowar tsiro masu tauri da tudu a fatar jiki ko ma farji. Suna iya sanya jin kaikayin farji.

6. Cutar hunhuna ta farji (yeast or candidiasis) 

Duk da cewa cutar yeast yawanci tana haifar da kaikayin gaba sosai da kuma fitar ruwa daga farji, wani lokacin zata iya sanya fitowar karamin tsiro mai kaikayi ko haifar da radadi yayin jima’i.

7. Cutar Lichen Planus ko Lichen Sclerosus

Wadannan cututtuka ne na kumburi a fatar jiki ko farji, kuma suna haifar da canje-canje a fata da fitowar tsiro. Yawanci suna haifar da kaikayi ko raÉ—aÉ—i yayin jima'i.

8. Cutar Condylomata Acuminatum (Condyloma Acuminatum)

Wannan nau'ukan HPV ne wadanda suke haifar da fitowar tsiro masu kama da cauliflower. Zasu iya yin kaikayi tareda haifar da radadi lokacin jima'i.

Kammalawa 

Abin da ya kamata ayi domin samun cikakken bayani akan abinda yake faruwa dake shine awon farji na pap smear ko biyopsi, ko kuma yin gwaje-gwajen cututtukan da ake iya kamuwa dasu ta hanyar jima’i (STIs).

Wanda ya amsa tambayar Dr. Usman Shehu Hassan 

Post a Comment

0 Comments