Bayani Game Da Tsiro A Cikin Ƙwan Haihuwa Na Mata (Ovarian Cyst)

Gabatarwa:

Yadda ake maganin ovarian cyst

Ovarian cyst wani tsiro ne ko kumburi a cikin maran mace wanda ke fitowa a cikin ƙwan haihuwa na mata. Ovarian cyst yana iya zama empty, ma'ana ba komai acikin sa, haka kuma yana iya zama cike da wasu ruwa ko jini ko wani kalar nama mai laushi. 

Ovarian cyst yana kasancewa ne a cikin ovary na mace, watau ƙwan mahaifa wanda shi ke samar da ƙwan da mace ke bada gudunmawa domin samun ciki. Ovary bangare ne na mahaifa inda ke fitar da kwan mace domin ya haɗu da sperm ɗin namiji domin ciki ya shiga.

Alamomin Ovarian Cyst 

Mafi yawancin Ovarian Cyst ba sa kawo wa mace matsalar komai. So dayawa mace tana dauke da Ovarian Cyst ba za ta sani ba har ya warke ko ya narke, wata kuma sai ta samu ciki taje yin hoton ultrasound sai a gano ashe ma tana ɗauke da wannan ovarian cyst. Yawancin Ovarian Cyst basu zama matsala kuma basa yiwa mace ciwo, amma akwai masu sanya ciwo, kaɗan daga cikin alamomin ovarian cyst da za'a iya samu sun haɗa da:

1. Ciwon mara, mafi yawanci a gefen mara na hagu ko na dama. Ya danganta da gefen da cyst din yake

2. Nauyi a cikin mara ko gefen mara

3. Ciwo a lokacin saduwa da maigida

4. Period ko al'ada mai ciwo sosai

5. Rikicin jinin haila

6. Kumburin ciki 

7. Rashin jindadin abinci

Yadda Ovarian Cyst Ke Zama Matsala Ga Mace

1. Functional ovarian cyst shi ne mafi yawa kuma yana da alaƙa da al'ada ko lokacin da mace ta ke ɗauke da ciki. Irin wannan ovarian cyst din ba yada matsala. Kuma ba a yi masa magani, da kansa ya ke narke wa ko kuma ya zuƙe. Yana samuwa ne saboda hauhawan sinadaran mata a irin wadannan lokutan, daga sinadaran sun daidaita zai iya ɓacewa da kansa.

2. Functional ovarian cyst ko ma wani kala na daban yana iya zama matsala ga mace ta hanyar sanya ta matsanancin ciwon mara akai-akai.

Yadda ake maganin ovarian cyst

3. Ovarian cyst na zama matsala idan ya rikide ya zamo cutar daji ma'ana cancer ovary. Kaɗan ne daga cikin ovarian cyst ke rikiɗe wa ya koma cancer.

4. Ovarian cyst na iya zama matsala ne idan ya kasance yana da girma sosai ko kuma idan yanada girma sosai kuma sai ya fashe.

5. Ovarian cyst na iya zama wa mace matsala a lokacin da ya rikiɗe ya fara samar da wasu sinadaran hormones na mata ko na maza. Waɗannan sinadaran hormones din zasu iya rikitawa mace al'ada ko su hanata samun juna biyu ko su fara sanya ta wasu halayyar maza.

6. Ovarian cyst na iya zama matsala ne idan ya laulaye jijiya daga cikin jijiyoyin da ke cikin mahaifar mace. Wannan emergency ne kuma a na yin tiyata ne domin warware shi.

Yadda Ake Maganin Ovarian Cyst Mai Matsala 

Ovarian Cyst mai matsalar ciwo kawai, idan har ciwon ba mai tsanani ba ne ko kuma ciwon baya zuwa akai-akai, toh, ana ba mace magungunan kashe ciwo. Idan kuwa ciwon ya tsananta ko kuma ovarian cyst din ya girma sosai toh, za'a yi aikin tiyata a cire wannan ovarian cyst.

Sauran ovarian cyst masu matsala dukkan su maganin su shi ne ayi aikin tiyata a cire wannan tsiron ko kumburin daga ƙwan mahaifa. Watarana dole ne a cire ƙwan mahaifar da ovarian cyst din ya fito a cikin sa baki daya.

Amma shi kam ovarian cyst din da ya rikiɗe ya zama ciwon daji, watau cancer, to wannan ana yin tiyata a cire dukkanin ƙwan haihuwar mace guda biyu tare da mahaifar baki ɗaya sannan a biyo da shan magungunan kashe ciwon daji.

Post a Comment

0 Comments