Cututtukan Da Ke Sanya Yawan Shan Ruwa Da Fitsari

Assalamualaikum don Allah mene n yake sa mutum kusan ko da yaushe yayi ta jin Æ™ishirwa kamar me azumi, kuma in tasha ruwan maÆ™ogwaro baya Æ™oshi sai dai cikin ya cika da ruwa, kusan kullum yini shan ruwa da yin fitsari, kuma anje asibiti likita ya tabbatar da cewa babu ciwon sugar kuma yace ma babu ciwon Æ™oda amma tana da Olsa. Ko olsa tana sa haka ne? gaskiya tana shan wahala da kishirwar nan. 

 

Yawan shan ruwa

 

Amsa

Ulcers ba ta haddasa yawan jin kishirwa ko yawan fitsari. Alamomin daka bayyana kamar yawan shan ruwa da fitsari suna iya zamowa na wasu cututtukan daban. Banda ciwon koda da ciwon sugar, wasu cututtukan dake iya haifar da yawan jin kishirwa da kuma yawan yin fitsari sun hada da:

1. Diabetes insipidus: Wani nau'in ciwon sugar ne wanda ba'a cika samunsa ba wanda yake hana samarda isasshen sinadarin antidiuretic (ADH) ko kuma kodojin mutum basu tasirantuwa dashi, wanda hakan yake haifar da yawan fitsari da kishirwa mai yawa.

2. Hypercalcemia: Hauhawar sinadarin calcium a cikin jini yana iya haifar da yawan fitsari da kuma yawan jin kishirwa.

3. Psychogenic polydipsia: Wata matsalar kwakwalwa ce inda mutum ke jin kamar dole sai ya sha ruwa da yawa ba tare da jiki yana bukatar shan ruwan ba.

4. Laulayin amfani da wasu magunguna (medication side effects): Magungunan karin fitsari (diuretics), lithium, ko steroids suna iya kara jin kishirwa da yawan fitsari a matsayin illoli.

5. Ciwon zuciya: Yana iya haifar da matsalar daidaita ruwa a jiki, wanda ke haifar da yawan jin kishirwa.

6. Sjögren's syndrome: Wani ciwon garkuwar jiki ne wanda ke shafar gland din dake samar da danshi, yana haifar da bushewar baki da kuma yawan jin kishirwa.


Idan wadannan alamomin suna ci gaba, yana da kyau a sake ganin likita don fadada bincike. 

Amsa tambayar:  Usman Shehu Hassan 

Post a Comment

0 Comments