Bayani Akan Cutar Murar Mashaƙo (Diphtheria)

Maganin murar mashaƙo

Murar mashaƙo ko kuma cutar diphtheria cuta ce wacce ake saurin ɗaukarta wadda ƙwayar cutar bacteria mai suna "corynebacterium diphtheriae" take haddasa wa. Tana kama hanyoyin numfashi ne waɗanda suke daga maƙogwaro zuwa ƙirji, sai ta haifar da matsalar tari, ciwon maƙogwaro da sarƙewar numfashi. Haka kuma, takan iya kama sassan fatar jiki ta haddasa ƙuraje masu gunɗar ruwa.

Alamomin Cutar Murar Mashaƙo 

Cutar murar mashaƙo ta na saurin kisa saboda ba a saurin gane ta da wuri idan an kamu, kuma a mafiyawanci sai ta kai ga yaro ya fara numfashi cikin wahala, ko kuma ya gaza cin abinci ko ya kamu da zazzabi mai tsanani ko kuma yawan tari sannan ake fara tuhumar cutar. Ga wasu alamomi na cutar murar mashaƙo;

Murar Mashaƙo

  1. Kumburin wuya
  2. Sarkewar numfashi
  3. Zazzabi
  4. Rashin ƙarfin jiki
  5. Rashin iya haɗiye yawu ko chin abinci
  6. Ƙurajen jiki
  7. Yawan tari
  8. Yoyon hanci
  9. Jajayen ido da dai sauransu. 

Yadda Ake Kamuwa Da Cutar Murar Mashaƙo 

Ana daukar cutar murar mashaƙo ta hanyar shaƙar iskar tari, numfashi ko atishawar da mai cutar yayi. Sannan ana iya kamuwa da ita ta hanyar mu'amalar cuɗanya da mai cutar, ko kuma yin amfani da kwano, cokali, kofi, da sauran kayayyakin gida waɗanda mai cutar yayi amfani dasu.

Hanyoyin Kariya Daga Cutar Murar Mashaƙo 

1. Yin allurar rigakafinta cutar, watau "diphtheria, tetanus, pertussis - DTaP" waɗanda ake yiwa yara a lokacin da suke jarirai, kuma ake ƙara yin su saboda ƙarfafa garkuwar jiki (booster dose) idan mutum ya girma.

2. Kyautata tsaftar jiki, abinci, tufafi, da muhalli.

3. Wanke hannaye da ruwa ko sabulu idan mutum yayi atishawa ko yayi mu'amala da mai cutar.

4. Kaucewa zama wuri ɗaya da mai cutar.

5. Rufe hanci da baki a lokacin da mutum zaiyi tari ko atishawa. 

6. Sanya takunkumi (face mask) a lokacin da mutum zai shiga muhallin da annobar cutar ta ɓarke.

7. Killace waɗanda cutar ta kama a wurin jinya sa kuma hana su cuɗanya da sauran jama'a.

Rigakafin Gaggawa Ga Wanda Ya Kamu Da Cutar Murar Mashaƙo 

1. Ya wajaba a kebe shi daga cudanya da mutane masu lafiya.

2. A gaggauta zuwa asibiti dashi domin samun kulawar likita ta gaggawa.

3. A sanya masa takunkumi saboda rage yawan fallatsar ruwan tari da atishawar sa a cikin muhalli.

Yadda Ake Maganin Cutar Murar Mashaƙo A Asibiti

1. Yin amfani da magungunan kashe ƙwayoyin cuta na antibiotics kamar su penicillin, erythromycin, da sauransu.

2. Yin amfani da magungunan kashe guba na"diphtheria antitoxin" domin dallashe kaifin dafin cutar a jiki. 

3. Yin amfani da magungunan da zasu taimaka wajen farfaɗowar maras lafiyan kamar iskar oxygen, kwayoyin kashe raɗaɗi, karin ruwa na drips da dai sauransu.

Post a Comment

0 Comments