Yadda Ake Amfani Da Hanyoyin Ba Da Tazarar Haihuwa Da Hana Daukar Ciki

Yadda Ake Amfani Da Magungunan Ba Da Tazarar Haihuwa Ko Hana Daukar Ciki 

Yadda ake hana daukar ciki

Mace za ta iya fara yin amfani da magungunan tazarar haihuwa kafin ta fara yin jinin al'adarta, ko lokacin da take yin jinin al'adarta, ko bayan ta gama yin jinin al'adarta. Tasirin magungunan wajen hana mace daukar ciki, ya danganta ne da nau'in maganin. 

Amma magana ta gama-gari ita ce an fi bayar da shawarar fara yin amfani da magungunan a cikin kwanakin farkon fara yin jinin haila. Ga bayanin yadda rabe-raben yake:

Magungunan ba da tazarar haihuwa masu É—auke da sinadaran estrogen da progesterone (COCP)

Ƙwayoyin magungunan tazarar haihuwa masu haduwar sinadaran hormones na mata guda biyu, watau sinadaran estrogen da progesterone, kamar Æ™wayoyin magungunan Microgynon, Levofem, Yasmin, ko Nordette, suna daga cikin magungunan hana daukar ciki waÉ—anda mata suka fi yin amfani dasu. 

WaÉ—annan Æ™wayoyin suna É—auke da sinadaran estrogen da progestins. Idan mace ta fara shan waÉ—annan Æ™wayoyin a cikin kwanaki biyar na farkon jinin hailar ta (rana ta É—aya zuwa ta biyar da fara yin jinin haila), zata sami kariya daga É—aukar ciki nan-take. 

Wannan yana faruwa ne saboda sinadaran da suke cikin ƙwayoyin suna fara yin aiki nan take wajen hana fitar ƙwan haihuwa (wajen hana mace yin ovulation)

Amma idan ta fara shan ƙwayoyin bayan kwanaki biyar da fara yin jinin haila ko ma bayan ta kammala yin jinin hailar, to, rigakafin da magungunan ke bayarwa ba zai yi aiki nan-take ba, kuma dole ne sai ta ƙara da yin amfani da wata hanyar kariya kamar kwaroron roba (condom) har tsawon kwanaki bakwai, domin ƙwayar maganin tana daukar lokaci kafin ta fara aiki.

Magungunan ba da tazarar haihuwa masu É—auke da sinadarin progesterone kawai

Ƙwayoyin magungunan ba da tazarar haihuwa masu É—auke da progestins kaÉ—ai, kamar Æ™wayoyin magungunan Cerazette, Micronor, da Noriday, su na da bambancin fara yin aiki idan aka kwatanta su da Æ™wayoyi masu haÉ—akar sinadaran estrogen da progestins, saboda su waÉ—annan progestins kawai suka kunsa. 

Idan mace ta fara shan waɗannan ƙwayoyin a ranar farko da ta fara jinin hailar ta, toh, za ta sami kariya nan take. Amma idan ta fara shan su bayan 'yan kwanaki da fara yin jinin hailar ta, toh, dole ne tayi amfani da ƙarin wata hanyar kariya idan za ta yi jima'i har sai bayan tsawon sa'a 48 (kwanaki biyu kenan chif) domin tabbatar da samun kariya daga ɗaukar ciki, saboda ƙwayoyin su na buƙatar lokaci kafin su fara yin tasiri wajen hana mace samun ciki ta hanyar hana ta sake ƙwan haihuwa (hana mace yin ovulation) da kuma sanya kaurin bangon mahaifa na ciki.

Yadda ake amfani da na'urorin ba da tazarar haihuwa na mahaifa waÉ—anda ke É—auke da sinadaran magunguna (IUD)

Yadda ake hana daukar ciki


IUDs ko kuma na'urorin ba da tazarar haihuwa na mahaifa waÉ—anda su ke Æ™unshe da sinadaran estrogen da progesterone, su ne kamar irin su na'urorin Mirena da Skyla. WaÉ—annan na'urorin roba ne da ake sanya wa a cikin mahaifa don samar da kariya daga É—aukar ciki na dogon lokaci, kamar shekaru uku zuwa biyar. 

Idan mace ta sanya na'urar IUD a lokacin da take yin jinin hailar ta, musamman a cikin kwanaki bakwai na farkon al'adar, toh, za ta sami kariya daga ɗaukar ciki nan take. Amma idan an sanya mata na'urar IUD a wani lokaci daban ba wannan ba, a zangon jinin hailar ta (menstrual cycle), dole ne sai tayi amfani da wani ƙarin hanyar kariya kamar kwaroron roba (condom), har na tsawon kwanaki bakwai kafin na'urar ta fara yin aikin da ya dace.

Yadda ake amfani da allurar ba da tazarar haihuwa domin hana É—aukar ciki 

Yadda ake hana daukar ciki

Allurai na tazarar haihuwa kamar Depo-Provera ko Sayana Press wasu hanyoyin ba da tazarar haihuwa ne, waÉ—annan allurai suna Æ™unshe da sinadaran estrogen da progesterone da ake bayarwa ga mace a duk bayan watanni uku. 

Idan akayi wa mace allurar a cikin kwanaki biyar na farkon zangon jinin hailar ta (kwanaki biyar da fara yin jinin hailar ta), toh, za ta samu kariya daga É—aukar juna biyu nan take. Amma idan aka yi mata allurar a wani lokaci na daban, to, dole ne sai tayi amfani da wata hanyar samun kariya, kamar condom, na tsawon kwanaki bakwai domin ba wa allurar dama ta fara aiki yadda ya dace.

Yadda ake amfani da dan-maƙale na tazarar haihuwa (Contraceptive patch)

Yadda ake hana daukar ciki

Dan-maÆ™ale, watau faski, na hana É—aukar ciki, kamar Ortho Evra ko Xulane, wani Æ™aramin abu ne da ake manna shi a fatar jiki wanda yake sakin sinadaran estrogen da progesterone zuwa cikin jiki. 

Idan mace ta manna wannan faski, a rana ta farko na jinin hailar ta, toh za ta sami kariya nan take. Amma idan ta manna faski bayan jinin hailar ta yayi kwanaki da farawa, toh, dole ne sai tayi amfani da wata hanyar kariya, kamar condom, na tsawon kwanaki bakwai kafin faski din ya fara aiki da kyau.

Yadda ake amfani da zoben farji (Vaginal ring)

Yadda ake hana daukar ciki

NuvaRing wani sassauƙan zobe ne da ake sakawa mace a cikin farjin ta don sakin sinadaran estrogen da progesterone a cikin sa. Idan mace ta saka zoben nan a rana ta farko na jinin hailar ta, toh, za ta sami kariya nan-take daga ɗaukar ciki. Amma idan ta saka shi a wani lokaci daban a cikin zangon jinin hailar ta, toh, dole ne sai tayi amfani da wata hanyar kariya, kamar condom, na tsawon kwanaki bakwai kafin zoben farji da aka sanya ya fara aikin da ya dace.

Yadda ake amfani da ashanar hannu (Contraceptive implant)

Yadda ake hana daukar ciki

Ashanar hannu, kamar Implanon, dabarar tazarar haihuwa ce, mai kama da Æ™aramar sandar roba wacce ake saka ta a karkashin fatar hannun mace ta sama. Wannan sandar roba ta na sakin sinadarin progestin ne domin hana É—aukar ciki na tsawon shekaru 3 ko fiye. 

Tana hana sake Æ™wan haihuwa, kaurara majinar bakin mahaifa don hana halittun haihuwa da ke cikin ruwan maniyyi shiga a cikin mahaifa, sannan tana kara kaurin bangon mahaifa na ciki domin hana Æ™yanÆ™yasasshen Æ™wan haihuwa maÆ™alewa a jikin bangon mahaifa. 

Idan aka saka ashanar hannu a cikin kwanaki biyar na farkon jinin al'ada (kar a manta, rana ta 1 ita ce ranar da jinin haila ya fara zuwa), tana ba da kariya nan take daga É—aukar ciki. Idan kuwa aka saka ta bayan kwanaki biyar da fara yin jinin haila, toh, dole ne sai mace tayi amfani da wata hanyar kariya, kamar kwaroron roba, na tsawon kwanaki bakwai, har sai allurar ta fara aiki sosai.

Kammalawa 

Sanin lokacin da ake fara amfani da magungunan tazarar haihuwa yana da matuƙar muhimmanci wajen samun cikakkiyar kariya nan take daga ɗaukar ciki. Fara amfani dasu a lokacin ko bayan mace ta fara yin jinin hailar ta yana taimakawa wajen daidaita tsarin jikin mace na halitta, yana rage hadarin fara amfani dasu yayin da ba'a san mace n ɗauke da ciki ba, kuma yana bayar da kariya da wuri. Idan an fara amfani dasu bayan jinin al'adar mace, yawanci za'a bukaci yin amfani da wata kariya (na kwanaki bakwai) don jikin ta ya daidaita da hormones.

Post a Comment

0 Comments