Gabatarwa:
Samun juna biyu abu ne da ya ta'allaka da abubuwa da dama kamar irin su lafiyar mace, adadin shekarun ta, sanin kanta da wayewar ta, lafiyar namiji, yawan jima'i da dai sauransu. A cikin wannan rubutu zamuyi bayani akan yadda mace zata gane ranar da take yin ƙwai (ovulation) da kuma hanyoyin da mace zata bi domin samun juna biyu a cikin sauƙi.
Mene ne ovulation?
Wannan haɗuwar itace ake kira da turanci 'fertilisation' wanda hakan shi zai sa ƙwan mace ya ƙyanƙyashe ta samu juna biyu. Domin ƙarin bayani game da yadda mace ke ɗaukar ciki ku karanta wannan rubutu "Bayani game da kimiyyar jima'in ɗan adam".
Yadda mace ke yin ovulation
Ko wace mace tana da ovary guda biyu a cikin kwankwasonta, waɗannan ovaries su ke da alhakin samar da ƙwai, fitar da shi da kuma samar da wasu sinadaran hormones na mata. Duk da cewa mace tana da ovary biyu amma a duk kowane wata tana samar da ƙwai ƙwara ɗaya kacal. Ovaries ɗin guda biyu suna raba aiki a tsakaninsu, idan ovary ta gefen dama ta samar da ƙwai a wannan wata toh wani wata mai zuwa ɗayan ce ta gefen hagu zata samar da ƙwai ita kuma ta farkon ta huta.
Haka shi ne ɗabi'ar samar da ƙwai daga ovaries. Amma duk da haka wata rana wasu mata sukan sami ovaries dinsu duka biyu su samar da ƙwai a lokaci ɗaya, watau mace zata fitar da ƙwai biyu (2) kenan. Wannan shi ne asalin samun tawaye (Dizygotic twins) idan har mace ta fitar da ƙwai biyu kuma ta samu yin jima'i a lokacin da duka ƙwan biyu ke raye kuma ko wane ƙwai ya samu haɗuwa da tantanin halittun dake cikin ruwan maniyyin namiji.
Mace tana samar da wannan ƙwai ne (tana yin ovulation) a tsakiyar watan ta na al'ada wanda yana kamawa ne bayan kwanaki goma (10) zuwa kwanaki goma sha biyu (12) bayan tayi tsarki daga jinin haila. Ko kuma ranar da zai rage saura kwanaki goma sha huɗu (14) chif kamin zuwan jinin hailarta na gaba.
Amma duk da haka idan ta samu yin jima'i ko sau ɗaya ne a cikin kwanaki biyar (5) kamin tayi ovulation zata iya ɗaukar ciki saboda wasu tantanin halittun da ke cikin ruwan maniyyin namiji sukan ɗauki tsawon kwanaki biyar (5) zuwa bakwai (7) a cikin mahaifar mace suna neman ƙwai kamin daga baya su mutu. Haka kuma idan mace ba ta samu yin jima'i ba sai bayan kwanaki uku (3) da yin ovulation, toh ko sau nawa tayi jima'i a cikin kwanakin da ya rage ba zata samu ciki a wannan watan ba sai dai wani wata idan ta ƙare yin jinin al'ada. Abinda yasa haka shi ne, ƙwan da mace ke fitarwa baya iya wuce kwanaki uku bai mutu ba.
Alamomin ovulation
Kamar yadda muka yi bayani a baya, kwanakin da ake tsammanin mace zata yi ovulation su ne rana ta goma (10th) ko ta goma sha ɗaya (11th) ko ta goma sha biyu (12th) bayan ta gama yin jinin al'ada. A waɗannan kwanakin ana so ma'aurata masu neman haihuwa su dage da nema sosai.
- Zata ga wani ruwa mai yauƙi, marar kala yana yawan zuba daga farjinta
- Zata iya jin wani ciwo kaɗan a gefen marar ta na hagu ko na dama
- Zata kama jin matsananciyar sha'awar jima'i
- Kan nonuwanta zai ɗan yi duhu kuma ya miƙe haka kuma idan aka taɓa akwai ciwo kaɗan
- Jikinta zai ɗan ƙara zafi
- Akwai wani gwajin fitsari da ake yi da wata takarda irin ta gwajin ciki wanda yake nuna mace ta kusan ovulation ko akasin haka. Ana kiran gwajin da turanci ovulation predictor test.
Hanyoyin samun juna biyu a cikin sauƙi
- Dagewa da yin jima'i a kwanakin da mace ke tsammanin ovulation
- Yin jima'i akai-akai da kuma ƙauracewa duk wata hanyar bada tazarar iyali; Masana sun fassara yin lafiyayyen jima'i akai-akai da yin jima'i sau biyu (2) zuwa uku (3) a cikin sati ɗaya. Sannan kwanakin jima'in kar su kasance suna bibiyan juna, anaso a bada tazara a tsakanin kwanakin domin namiji ya huta kuma ruwan maniyyinsa ya taru. Wannan shi yasa ba'a son namiji yayi jima'i kulli yaumin a jere sai a cikin kwanaki biyu ko uku da matarsa ke tsammanin ovulation.
- Anaso mace ta kwanta a bayanta na kamar mintuna goma (10) zuwa goma sha biyar (15) kamin ta tashi zaune bayan kammala jima'i. Yin haka shi zai ƙara bada dama ga tantanin halittun ruwan maniyyin namiji su shiga mahaifar mace.
- Ƙauracewa matsanancin motsa jini: Matsanancin motsa jini yana da illa ga jikin mace, domin yakan iya hana ta samun juna biyu cikin lumana. Wannan shi yasa wasu mata masu ƙwallom ƙafa, ko masu gasar tseren mita ko mata sojoji suke samun matsalar haihuwa da yawan rikicewar jinin al'ada.
- Ƙauracewa shan sigari da barasa
- Chin lafiyayyen abinci
- Ƙauracewa duk nau'in abincin ko abin sha da ke ɗauke da sinadarin caffeine.
- Mace ta kula da jikinta kar tayi ƙiba sosai kuma kar ta zama siririya sosai.
1 Comments
Mungode Amman in a samu ciki alamominnan natafi ya koyaya alamomin ovulation din
ReplyDelete