Slm Likita Ina da tambaya 2_3
1. Shine me yasa idan ana ma mutum ƙarin jini bai ci bai sha ko karin ruwa, kamar yadda na ga wasu ma aikatan lafiya na hanawa?
2. Shin me yasa idan akai accident ko Kuma mutum ya shiga wani yanayi da zai chanja psychological actives ɗinshi due to accident or trauma or any severe condition idan ya nemi a bashi ruwa sai a hanashi
3. Shin mai juna biyu at first trimester za a iya ba ta treatment na malaria with inj. arthemeter or tablet?
Amsar Tambaya ta Farko
Wannan tambaya ta na da fa'ida sosai, abu na farko dai hanyar da ake ba da ƙarin ruwa ko jini ita ake kira Intravenous Route Of Administration watau yin allura, sa ruwa ko sa jini ta hanyar jijiyar jinj mai mayar da jini zuwa cikin zuciya.
Duk abin da ake bayarwa ta jijiyar jini wannan abin yana zuwa kai tsaye a cikin ƙoramar jini da zuciya, idan akai la'akari da amfanin wannan jijiyar dake ɗauke da kalar jinin da ake samu gareta.
Sunan kalar waɗannan jijiyoyin jini masu mayar da jini a zuciya shi ne "veins" sannan amfanin su shi ne ta ɗauko jini daga huhu da sauran sassan jiki zuwa ga zuciya.
Shi kuma abinci hanya ta daban ake sanya shi, ba ta jijiya ba. Abinci yana shiga ta baki ne yabi hanyar sa ta maƙogwaro har zuwa ciki jikkar tuwo (stomach) sannan ya wuce zuwa a hanji.
A lokacin da abinci yaka cikin hanji ne yake samun ƙwaƙƙwarar narkewar da zai iya shiga cikin ƙoramar jini domin samar mutum kuzari da ingantattun sinadarai.
Saboda haka ana iya sha ko cin wani abu ta baki a lokacin da ake ƙarin ruwa ko jini idan bukatan hakan ta taso, domin babu wata kyakkyawar alaƙa tsakanin abincin da aka ci ta baki da ruwa ko jinin da ke shiga ta jijiyar jini da zai hana yin haka. Kowanen su da tashi hanya.
Abin da yasa mu ma'aikatan lafiya bamu cika yarda da wannan ɗabi'un ba saboda rashin natsuwa ta majinyaci da kan iya biyowa baya, yiwuwar kaucewar robar jijiya (cannula) da muke sanya wa jijiya bayan wahalar da akasha kila wajen eman ta, kusan ire iren waɗannan ne ke sa mu hana aci ko asha lokacin ƙarin jini ko ruwa.
Bugu da ƙari, za a iya samun gurɓacewar abinci daidai lokacin da ake amfani da abincin idan babu wadatattar tsafta a inda ake ƙarin jinin musamman a asibiti. Duka waɗannan manyan dalilai ne da ke sawa a hana ci da sha a lokacin ƙarin jini ko ruwa. Amma hakan ba wata doka bace a likitanci na hana ci da sha lokacin ƙarin jini ko ruwa, kamar yadda wasu masu jinya suke ɗauka.
Amsar Tambaya ta Biyu
Tabbas Bai Kamata ana Bayar da Ruwa lokacin da akai Accident ba saboda yana da hatsarin gaske musamman idan akwai buguwar kai (head injury) watau, jin rauni mai tsanani a kai ko kuma mutum ya ɗan fara fita daga hayyacin sa.
Bayar da ruwa ko abinci lokaci da akai Accident bai inganta ba saboda mutane dayawa a irin wannan lokacin ba sa cikin hayyacin su, shan ruwa ko wani abinci a wannan lokaci yana iya haifar da sarƙewa har abinci ko ruwan da aka sha su bi hanyar da bai kamata ba, su kan iya shiga cikin huhu su kawowa mutum cutar aspiration pneumonia, wannan cutar kaɗai ta isa tayi sanadiyar mutuwar marar lafiya.
Haka kuma, idan har jin ciwon da marar lafiya yayi, yana buƙatar aikin tiyata na gaggawa, toh akwai buƙatar cikin marar lafiya ya zama babu komai a cikin sa a lokacin da za'a yi tiyatar. Idan za ayi ma mutum aiki bai kamata yasha wani abu ba domin lokacin aikin zai iya aman sa ko ya dawo ya Shiga huhu inda ba a so ya haddasa cutar pneumonia kamar yadda mu ka yi bayani.
Amma idan raunin bai shafi ciki ko kai ba, kuma mutum yana cikin hayyacin sa lami lafiya, toh za'a iya bayar da ruwa ko abun sha.
Amsar Tambaya ta Uku
A bisa ga binciken masana an tantance magani da allurar quinine a matsayin mafi soyuwa a wajen maganance cutar Malaria ga mace mai juna biyu, saboda masana sun tabbatar da quinine ba ta da illah ga mace mai juna biyu da kuma abin da take ɗauke da shi a cikin ta.
Allurar arthemeter ko magani ko sauran artemesin based combination ba'a tabbatar da cewa basu da illah ga baki ɗaya ba a lokacin da cikin mace yake ƙanƙani, akwai buƙatar ƙara yin nazari akan su, saboda haka a irin wannan lokaci barin amfani dasu shi ne yafi.
0 Comments