Abincin Mai Ciwon Hepatitis B

Assalamu Alaikum WarahmatulLah likita barka da warhaka, ina yi maka fatan alkhairi, Allah ya taimake ka fiye da yadda kake taimakon mu. Likita don Allah ina nema ƙarin bayani akan abincin da mai cutar hepatitis B ya kamata ya dinga chi. Nagode.

Abincin mai cutar hepatitis B

Amsa

Tunda kin kawo maganar hepatitis B. Bari in rufe da yin sharhi akan wata mas'ala da ta zama ruwan dare game da abincin masu hepatitis B. za ku ga wasu daga zarar ance suna da hepatitis B, sai ace su daina cin duk wani abincin da ke dauke da sinadarin protein, kamar nama, kifi, kwai, wake, awara da dai sauransu. 

WANNAN BA DAI DAI BA NE KUMA KATOBARA CE, Idan mutum yana da hepatitis ko wane iri ne ba a cewa ya rage chin sinadarin protein har sai hepatitis din ya lalata masa hanta baki daya, ya kai stage inda ake cewa 'cirrhosis' da turanci. 

Ko a wannan stage ana cewa ne mutum ya rage chin sinadarin protein amma ba ya daina chi ga baki daya ba. Saboda a wannan stage hantar sa tayi raunin da bata iya sarrafa sinadarin proteins dayawa, overload din wannan sinadarin zai iya haifar masa da wani complication da ake kira H.E.

Protein sinadari ne da jiki ke buƙata dole, wanda kuma rashin sa zai iya haifarwa mutum illar da hepatitis bai haifar masa ba.

Don haka don ance mutum nada hepatitis ba shi zai sa ace mutum ya daina chin abincin da ke dauke da protein ba, akwai ma wasu masana da ke ganin mutum na iya doubling din protein din da yake chi domin ƙarawa garkuwar jikinsa ƙarfin fada da hepatitis.

Bissalam, sai wani mako Insha Allah

Post a Comment

0 Comments