A baya-bayan nan an samu ɓullowar wasu mutane masu iƙirarin warkar da mutane daga cutar HIV ga baki ɗaya, wasu suna tallata magungunan su a fili wasu kuma a kafafen sada zumunta kamar facebook, Instagram, Tiktok da kuma shafin sadarwa na X.
Duk wanda yace muku yana da maganin warkewa daga cutar HIV na gargajiya, toh daga ranar ku fara sanya shi a cikin sahun maƙaryata da 'yan damfara. In dai Allah ya ƙaddara ɗan damfara zai ci abinci cikin aljihun ka, toh sai yaci, ba ka da wata dabara sai ka basu.
Ma'aikatan asibiti na gaskiya waɗanda suka san miye HIV sun san cewa wannan maganar babbar katoɓara ce kuma ƙarya ce ake yi muku, wayau ne ake yi muku, amma wasu ba sa gaya muku suna barin ku da dabarar ku ne idan kun nace.
Akwai wani ɗan'uwa da ya ke gayamin wallahi an damfare shi akan maganin HIV na gargajiya an ci kuɗin sa yafi ƙimar dubu ɗari biyar (#500,000), daga baya ya gaji ya sallama ya koma shan maganin sa na asibiti.
Sau dayawa zaka ga mutum yace ma yana da cutar HIV, idan ka tambaye shi ko yana kan maganin HIV na gaskiya, sai yace maka na'am yana amfani da maganin HIV na gargajiya. Wani ma ce maka zai yi ai shi yanzu yasha maganin HIV na gargajiya kuma ya riga ya warke, ba shi ba cutar HIV.
Duk mai aikin lafiya kuma a É“angaren HIV yasan akwai waÉ—anda zasu zo da cutar HIV su fara shan maganin HIV na asibiti daga baya sai su gudu su daina zuwa asibiti su koma wajen maganin HIV na gargajiya.
Idan suka cigaba da amfani da maganin HIV na gargajiya daga baya, a lokacin da cutar HIV tayi nisa ta karya musu garkuwar jiki sai a sake dawowa dasu asibiti akan ciwon bayan ya zama AIDS.
A irin wannan lokacin sake É—ora su akan maganin HIV na asibiti ba wani tasiri yake yi ba, saboda sun riga sun samu abin da ake kira resistance da turanci. (RESISTANCE TO ANTI-RETROVIRAL THERAPY).
Yadda Ake Yaudarar Mutane Da Maganin HIV na gargajiya
Masu magungunan gargajiya suna yaudarar jama'ah suna cewa suna da maganin HIV na gargajiya kuma duk wanda yayi amfani da shi zai warke, ko yaje asibiti idan an yi gwajin cutar to ba za'a ganshi É—auke da cutar ba.
Wannan ƙarya ce, yaudara ce. Kaɗan daga cikin hanyoyin da masu bada irin waɗannan magunguna na gargajiya suke bi sune;
Masu wannan badaƙalar ta bada maganin HIV na gargajiya za su tura ka inda za ka je kayi test bayan ka gama amfani da maganin su. Waɗannan masu yin tests din su na da kyakkyawar alaƙa tsakanin su da masu maganin gargajiya, sai ka ga an rubuta ma result ga plain A4 paper wai negative.
Instead of su ce kaje asibitin koyarwa mafi kusa (Teaching Hospital) ko wata government hospital ayi ma test, sai su ce ma test ɗin asibitin ƙarya ne, suna son tara patients ne saboda su tura a asibitocin da suka yarda dasu domin aunawa.
Wani ma mai maganin gargajiyar yana haÉ—a kai da ma'aikatan asibiti É“ara gurbi waÉ—anda za su rubuta ma test É—in ka na HIV is negative, amma ba akan ingantacciyar takardar asibiti ba, za'a rubuta akan takardar plain A4.
Munyi ta samun ire iren waÉ—annan result É—in test na bugi. Koda an zo asibiti neman waya ba da wannan result É—in kowa zai ce ba shi bane, ko signature ba'asan mai ita ba. Wannan ma har wasu manyan asibitoci akwai wasu É“ara gurbi da ke yin haka. Shi yasa wasu asibitoci sun daina ba da result ga hannu sai dai online za'a turawa likita.
Wasu masu maganin gargajiya na HIV su na amfani da tsafi, iskoki ko rahwanai, idan suka ba ka maganin su tsawon wata 3 ko 6 kana gama sha za su ce kaje kayi test, koda kaje test É—in, wanda zaiyi test É—in zai ga ba kada cutar HIV, ma'ana test É—in zai zo negative, instead of positive.
Daganan sai ka iyar da biyan su maƙudan kuɗin jingar su. Koda kuwa government teaching Hospital ne akaje akayi gwajin sai ya nuna NEGATIVE. Amma da ka koma gida da wani lokaci sai ciwon ya dawo har ya ci ƙarfin garkuwar jiki ya zama cutar AIDS.
A lura cewa lallai waɗannan masu iƙirarin ba da maganin cutar HIV na gargajiya suna da hanyoyi da dama na yiwa jama'a dabaru da daɗin baki domin karɓe musu abin aljihun su. Suna nan a wurare daban daban har ma suna tallata hajojin su a shafukan sada zumunta.
Yarda da su da kuma amfani da magungunan su ba ƙaramin haɗari ne dashi ba, saboda mafiyawanci suna sanya mutum ya saki jiki ya daina shan magungunan asibiti da sunan shi ya warke daga cutar HIV. Wannan zai sa cutar HIV damar haɓaka da cin ƙarfin garkuwar jikinsa.
Muna ƙalubalantar duk wani mai maganin HIV na gargajiya da duk wani mutum ma da yaji haushin wannan rubutu ko ya ga muna kashe masa kasuwa, toh ya zo da maganin sa na HIV na gargajiya a tantance maganin da abubuwan da ake haɗa maganin da kuma yadda maganin sa na gargajiya ke warkar da cutar HIV. Akwai maras lafiya da dama da za'a ɗauki nauyin gwada maganin a kansu.
Lallai idan har maganin sa yana warkar da cutar HIV ga baki É—aya toh zai sami É—aukaka ta musamman a duk faÉ—in duniya kuma sunan sa zai shiga tarihin duniya saboda ya samo solution ga mas'alar da turawan yamma ma suka kasa.
Idan kuwa ba ku iya yin haka, toh kuji tsoron Allah ku daina damfara da zalunci, ko hana mutum neman maganin asibiti wanda zai taimaka masa kuma ku karɓe masa kuɗaɗen hannun sa, sai cutar sa tayi nisa ta koma AIDS kuma a dawo asibiti ana da nasani. Allah yasa mu dace.
0 Comments