Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Tambayoyi da Amsa akan Cutar Kanjamau HIV/ AIDS

HIV questions and answers

Tambaya ta farko

Kwanakin baya wata uku da suka wuce wata makwabciyarmu tazo gidanmu to ana zargin tana dauke da ciwan sida (HIV) to da tazo tayi anfani da wukar gidanmu ta yanka Kayan miya ni bani nan toh bansaniba ta yanke da wukar ko Bata yankeba bayan tayi aiki da wukar da kwana Daya Nima nazo nayi aiki da ita wukar se na yanke hannu da ita toh shine abun yake damuna wlh tunda banida tabacin ko ta yanke ko Bata yanke ba.

Abun Yana damuna sosai dayin abun wata uku ba kwana hudu naje akayimin gwaji amma negative ne duk da hankan hankali n'a bai kwanta ba tunda Naji Ance se kuma wasu wata ukun inzo asake gwajin. Dan Allah Ku taimakamin 🙏🏿da cikaken bayani.

Naji kuma wasu sunce tunda wukar har ta kwana nayi aiki da ita cutar ta Riga ta mutu koda ta yankeni bani iya daukar cutar. Wlh banida sukuni kulum cikin damuwa nake dan Allah ataimakamin da cikaken bayani ko hankali na zei kwanta.

Amsa

Munyi bayani game da hanyoyin kamuwa da cutar sida (HIV) daki-daki. Haƙiƙa tarayya wajen amfani da abubuwa masu kaifi kamar reza da wuƙa da allura yana sanya mutum wanda bayada cutar ya ɗauki cutar, saboda akwai yiwuwar abu mai kaifi ya shiga jikin marar lafiya kuma ya shiga jikin mai lafiya. Amma a lura cewa ƙwayoyin cutar HIV ƙwayoyi ne dangin cutar virus, sannan mafi yawancin ƙwayoyin virus basa iya rayuwa da kansu dole sai in suna cikin jinin mutum ko wasu tantanin halittu masu rai.

Duk da haka wasu virus din kamar virus na cutar hepatitis B, suna dadewa basu mutu ba ko bayan sun fita daga jini ko tantanin halittun da suke a ciki. Ƙwayoyin cutar virus na HIV baya cikin masu dadewa basu mutu ba. 

Saboda haka, duk da cewa, akwai hatsari sosai na yaɗuwar cutar daga haka, yiwuwar yaɗuwar cutar yana raguwa a lokacin da aka dade ba'a yi amfani da abu mai kaifi ba bayan mai cutar yayi amfani dashi. Saboda ana tsammanin cutar HIV zata mutu cikin yan sa'o'i bayan ta fita daga jinin mai dauke da ita idan bata samu wani gurin shiga ba.

Don haka, baiwar Allah muna baki shawara da ki kwantar da hankalinki Insha Allah baki kamu da wannan cutar ba, a yayin da muka yi dogaro da wadannan dalilai masu zuwa:

  1. Matar da tayi amfani da wuƙar zargi ne ake yi tana da cutar, ma'ana ba'a tabbatar ba.
  2. Ko da ya tabbata tana da cutar HIV baki da tabbacin ta yanke kanta a lokacin da tayi amfani da wuƙar.
  3. Ko da kinada tabbacin ta yanke kanta da wuƙar, sai bayan kwana ɗaya da tayi amfani da wuƙar sannan ke kika yanke kanki da wuƙar. Wanda hakan yana rage hatsarin yaɗuwar cutar HIV sosai, sakamakon yiyuwar mutuwar cutar a waje bayan ta shafe fiye da sa'o'i ashirin da huɗu ba tare da samun gurin shiga ba.
  4. Kinyi test din cutar HIV bayan watanni uku kuma ya nuna negative. Wanda bayan watanni uku muna tsammanin idan har kin kamu da cutar toh ta zagaya cikin jinin ki ta yadda test dinda ki kayi zai iya nuna akwai cutar a cikin jininki, duk da cewa hakan ya danganta da wane irin test akayi. Amma tabbas idan akwai cutar test din zai nuna bayan wata uku.
Saboda haka muna baki shawarar ki kwantar da hankalinki ki sake yin gwajin bayan watanni shida domin kara tabbatarwa.

*****

Tambaya ta biyu 

Mutane ne ke yin jima'i tare da kororon roba na condom, bayan sun dade suna yin jima'in sai kororon roba na condom din ya fashe Kuma sunka cigaba da juma,I. To ana iya kamuwa da cutar HIV bayan fashewar condom din?

Amsa

Sosai kuwa, ai koda sun daina yin jima'i a lokacin da robar kariya ta condom din ta fashe toh akwai yiwuwar kamuwa da cutar HIV toh balle sun cigaba.

Dalili kuwa shi ne cutar HIV tana yaɗuwa ne a lokacin da aka samu cudanya tsakanin farjin mace da namiji kai tsaye, a lokacin da ruwan farjin mace suka taɓa azzakarin namiji, ko ruwan zakarin namiji suka taɓa farjin mace. A lura da magana ta dakyau, nace ruwa, bance maniyyi ba, don haka ina nufin duk wani kalan ruwa mai fitowa daga cikin al'aurar mace ko namiji to za su iya shafawa mutum cutar HIV.

Don haka a lokacin da kororon robar kariya ta condom da suke amfani da ita ta fashe, akwai yiwuwar ruwan al'aurar su ya samu cudanya. Da ace lokacin da robar condom din ya fashe sun daina jima'in tohm da yafi, saboda hatsarin samun cudanya tsakanin ruwan al'aurar su ya rage, amma kasshhhh! Ko da robar ta fashe daɗi ya kai musu intaha, suka kasa daina wa.

*****

Tambaya ta uku

Tsawon sati nawa ne cutar ke iya bayyana idan anyi gwajin HIV tazama positive?

Amsa

Amsar wannan tambaya ya danganta da irin kayan gwajin da akayi amfani dasu, da kuma yadda aka cire jinin da aka yi gwajin dashi, ta hanyar jijiya ko ta tsinken yatsa. Akwai kaloli daban-daban na test din HIV wanda ko wannensu yana da adadin kwanakin da yake iya gane cutar a cikin jinin mutum.

Kwanakin da HIV ke yi a cikin jinin mutum daga lokacin kamuwa da cutar zuwa lokacin da wani gwajin cutar HIV zai iya bayyanar da cutar  ana kiran su da HIV window period.

HIV window period sun samo asali ne saboda dole idan HIV ya shiga cikin jinin dan adam ya dauki lokaci ya hayayyafa sannan ya yaɗu a cikin jini kamin wani gwaji ya iya nuna shi. Don haka babu wani gwajin da zai iya nuna mutum ya kamu da cutar HIV daga zarar mutum yaci karo da cutar.

Ko wane gwajin HIV yana da na shi window period. Zamuyi bayanin gwaje-gwajen HIV da kuma lokacin da suke dauka kamin su iya nuna akwai cutar bayan mutum yaci karo da cutar.

1. Gwajin Nucleic Acid (NAT) - Gwajin NAT na HIV na iya nuna idan ka kamu da kwayar cutar HIV kwanaki 10 zuwa 33 bayan kamuwa da cutar. Ana yin test din ta hanyar bincike akan jini daga jijiyarka.

2. Gwajin Antigen/Antibody - Gwajin antigen/antibody wanda dakin gwaje-gwaje ke yi akan jini daga jijiyarku na iya gano kamuwa da cutar HIV a kwanaki 18 zuwa 45 bayan mutum ya ci karo da cutar. Gwajin antigen/antibody da aka yi da jini daga tsinken yatsa yafi ɗaukar tsawon lokaci don gano HIV (kwanaki 18 zuwa 90 bayan cin karo da cutar).

3. Gwajin Antibody - Gwajin antibody yawanci zai iya gano kamuwa da cutar HIV kwanaki 23 zuwa 90 bayan mutum yaci karo da cutar. Yawancin gwaje-gwajen da akeyi kai tsaye a fada maka sakamako, da kuma gwaje-gwajen da mutum zai iya gudanar wa da kansa duk gwaje-gwajen antibody ne. 

Zaku iya shiga WhatsApp group dinmu domin turo mana naku tambayoyi ta hanyar danna hoton WhatsApp da ke hannuku na hagu a ƙasa. Idan kuma group din yana kulle zaku iya turo mana tambayoyin ku ta private message.

Print this post

Post a Comment

0 Comments