Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Alamomin cutar kanjamau (HIV/AIDS) da kuma yadda ake gane mai dauke da cutar

 Gabatarwa:

A rubutun da mukayi a baya munyi bayani mai yelwa game da hanyoyin kamuwa da cutar kanjamau ko kuma tsida (HIV/AIDS) haka kuma munyi tsokaci a kan yin wasu mu'amaloli na yau da kullum tare da mai dauke da cutar HIV wadanda cutar bata iya yaÉ—uwa ta hanyar wadannan mu'amaloln. A cikin wannan rubutu zamu yi bayani game da alamomin cutar kanjamau da kuma hanyoyin da ake bi domin gane mai cutar kanjamau a asibiti.

HIV kanjamau 

Alamomin cutar kanjamau (HIV/AIDS)

Yawancin mutanen da ke fama da cutar kanjamau (HIV/AIDS) ba su bayyanar da wasu takamaiman alamomi. Bayanai na baya-bayan nan sun nuna cewa tsakanin kashi 70 zuwa 90% na mutanen da suka kamu da cutar kanjamau (HIV/AIDS) sun fuskanci bayyanar cututtuka kamar mura a cikin 'yan makonni bayan kamuwa da cutar ta kanjamau. Mafi yawan cututtukan da suka fi fuskanta sune zazzabi, kurajen jiki, da ciwon makogwaro mai tsanani duk a lokaci daya. Bayyanar wadannan cututtuka a jikin wani mutum mai lafiya na iya nuna sabon kamuwa da cutar kanjamau HIV/AIDS.[¹]

 Masu cutar kanjamau HIV na iya samun ciwon infection na yeast (na baki ko farji) wanda ke da wahalar warkewa ko ansha magani, ko kuma wanda ke faruwa akai-akai, yana warkewa yana sake dawowa. Haka kuma masu kanjamau, suna yawan samun cututtuka da infections na Herpes virus masu tsanani da ke haifar da Æ™urajen baki Æ™urajen al'aura, ko Æ™uraje a cikin dubura.[¹]

Haka zalika, wasu cututtuka sunfi faruwa a cikin masu fama da cutar HIV sakamakon karayar garkuwa jiki da masu cutar ke fama dashi. Wadannan cututtuka sun Æ™unshi, cutar Herpes Zoster, Cututtukan huhu kama cutar Pneumonia, Cututtuka masu sanya matsananciyar gudawa da ramewa. Haka kuma mata na iya kamuwa da cututtukan sanyin mara, kurajen gaba da dai sauransu.[¹]

Haka kuma bincike ya nuna wasu manyan alamomin da ke nuna kamuwa da cutar kanjamau.
  1. Fitowar kaluluwa wurare daban daban a jiki, musamman fitowar kaluluwa a bayan wuyan hannu, bayan kunne da bayan ƙeya. Akwai cututtuka dayawa da kan iya sa kaluluwa fitowa a waɗannan wurare, amma idan kaluluwa ta fito a waɗannan wurare kuma ta shafe tsawon aƙalla watanni uku (3 months) bata ɓace ba to ana kyautata zaton kamuwa da cutar kanjamau (HIV).
  2. Muguwar rama da ba gaira ba dalili.
  3. Yawan zazzaɓi da cututtuka yau da kullum
  4. Dadewa ana gudawa da ba gaira ba dalili
  5. Tarin fuka
  6. Yawan zufa dadare
  7. Fitowar kuraje masu dadewa basu warke ba a jiki ko a al'aura.
  8. Kurajen baki masu wuyar warkewa.
  9. Fitowar hunhuna a baki (oral thrush).
Alamomin cutar kanjamau (HIV)

A wani bincike da aka gudanar a asibitin koyar da likitanci ta jami'ar Jos, jihar Filato, Nigeria ya gano cewa manyan alamomin da ke kawo masu fama da cutar kanjamau (HIV/AIDS) a asibiti sune : Muguwar rama ko asarar nauyi (65.5%), zazzabi (41.5%), tari na yau da kullun (38.5%), zawo (32.0%), Æ™aiÆ™ayin jiki (13.0%) da Æ™urajen jiki (12.5%). Manyan alamomin da likita ke iya samu yayin duba marar lafiyar sune: Karancin jini (25.0%), hunhunar baki (oral thrush) (20.5%), Mummunar ramewa (20.0%), kaluluwa (18.0%), kumburi da Æ™urajen fata (16.0%), dushewar Æ™umba (hyperpigmented nails) (13.5%) da dunÆ™ulewar gabar yatsa ta karshe (finger clubbing) (8.5%).[²]

Yadda ake gane mai cutar kanjamau (HIV/AIDS) a asibiti

A lokacin da likita ya gama ganawa da marar lafiya kuma ya kyautata zaton cewa marar lafiyar yana dauke da cutar kanjamau (HIV), bayan ya duba shi a kan gadon asibiti za ya tura shi a lab domin yin gwajin cutar. Gwajin cutar Kanjamau HIV shi kadai ne ke da ikon tabbatar da mutum yana dauke da cutar ko kuma akasin haka. Mafi yawanci, a wurin yin gwajin ana amfani da jini ne.

HIV test ko kuma gwajin kanjamau 


Kammalawa

Duk da cewa cutar kanjamau bata da takamaiman alamomin da take nunawa, amma a cikin wannan rubutu mun naƙalto manya manyan alamomin da ke nuni zuwa ga kamuwa da cutar kanjamau ko kuma HIV/AIDS kamar yadda binciken masana ya tabbatar. Idan kuna da tambaya ko neman wani karin bayani ko wani sharhi to zaku iya tuntubar mu ta akwatin sharhi dake kasa, Insha Allah zamu amsa muku tambayar.

Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 

Nassoshi


Print this post

Post a Comment

0 Comments