Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Bayani game da yadda ake samun ciki a bayan mahaifa - Ectopic pregnancy

Gabatarwa 

 Samun ciki a bayan mahaifa wanda likitoci ke kira da ectopic pregnancy yana faruwa ne a lokacin da fertilised egg (Æ™wan mace da ya hadu da maniyyin namiji bayan saduwa) ya dasa kansa a wani wuri saÉ“anin cikin kogon mahaifa, haka kuma, kwan ya kyankyashe ya zama ciki ya cigaba da girma a wajen mahaifar. Samun ciki wajen mahaifa abu ne mai haÉ—arin da zai iya zama sanadiyar rashin lafiya mai tsanani ko ma yayi sanadin mutuwar mace mai ciki idan ba'a yi saurin gane shi da É—aukar mataki ba.[¹]

Ectopic pregnancy a cikin bututun Fallopian

A kasashen da suka ci gaba, tsakanin kashi 1% zuwa 2% na duk masu ciki da aka ruwaito suna dauke da juna biyu a wajen mahaifa. A kasashe masu tasowa kamar Nigeria adadin samun ciki a wajen mahaifa ga mata masu ciki ya kai 5%.[¹]

Me ke kawo samun ciki a bayan mahaifa?

 Har ila wa yau babu tabbacin takamaiman abunda ke kawo samuwar ciki a wajen mahaifa ko da yake an gano wasu abubuwan da ke kara haÉ—arin faruwar haka. Wadannan abubuwa ko kuma cututtuka masu kara haÉ—arin samuwar ciki a wajen mahaifa sun haÉ—a da[¹];

  1. Cutar sanyin mara
  2. Matar da ta taɓa samun zubewar ciki a baya
  3. Matar da ta taba samun ciki a wajen mahaifa
  4. Matar da ke da shekaru masu yawa ko da ta dauki ciki (shekaru 35 - 45)
  5. Cututtukan infections masu biyo bayan zubewar ciki
  6. Mace mai shan sigari
  7. Cututtukan infections masu damuwar gaban mace
  8. Cikin da aka samu ta hanyar hanyoyin zamani na assisted reproductive techniques 
  9. Amfani da robar bada tazarar iyali wadda ake sakawa a cikin mahaifa 
  10. Kumburin fibroids 
  11. Sankarar mahaifa
  12. Sankarar ovary 
  13. Matar da ta fara jima'i tun tana da ƙananan shekaru
  14. Matar da ke saduwa da fiye da namiji É—aya
  15. Matar da aka haifa da matsalolin mahaifa
  16. Matar da ta samu toshewar bututun Fallopian

Alamomin ciki a bayan mahaifa 

Samun ciki a wajen mahaifa yana zuwa ne tare da manyan alamomi guda uku. Mafi akasari waÉ—annan alamomin suna zuwa ne a jere kamar yadda zamu ambace su a yanzu:
  1. Rashin ganin jinin al'ada: Wannan itace alama ta farko da mace zata fara kokwanto ko ta samu ciki.
  2. Ciwon mara mai tsanani: Watarana mace ta kan ji wannan ciwon a gefen mara ko ma cikin ciki, ciwon ya danganta da inda cikin yake zaune. A lura cewa, mata suna iya samun ciwon mara a yayin da suke da danyen ciki, amma ciwon mara mai tsanani wanda wani lokaci zai iya kai ga kafadar hannu yana iya nuna cikin da aka samu baya cikin mahaifa.
  3. Zubar jini daga farjin mace: Wasu mata baza su iya bambanta wannan jinin da na al'ada ba, sai dai wannan jinin bai kai yawan jinin al'ada ba. Saboda haka, duk macen da ake saduwa da ita, taji waÉ—annan alamomi guda uku ya kamata ta garzaya asibiti domin binciken kwakwaf.
Haka zalika, bayan waɗannan manyan alamomi guda uku, mace zata iya fuskantar wasu kananan alamomi kamar su zazzaɓi, amai da gudawa, rashin karfin jiki, jiri, ganin juwa, ciwo yayin fitsari da dai sauransu.

Yadda ake gane ciki yana bayan mahaifa a asibiti 

 A halin yanzu, a cikin Æ™asashen da suka ci gaba, da kuma Æ™asashe masu tasowa, ana gane cikin da aka samu a wajen mahaifa ta hanyar yin gwaji guda biyu zuwa uku.

  1. Gwajin ciki (Pregnancy Test): Wannan gwaji ana yinsa domin tabbatar da mace ta samu ciki ko akasin haka.
  2. Hoton ultrasound da ake kira Transvaginal Scan (TVS): Wannan wani hoto ne na musamman da ke nuna duk abinda ke cikin mahaifar mace da kuma kunkuminta. Ana yin wannan hoton ne domin duba mahaifa da kuma abinda ke cikinta. Idan har gwajin ciki ya nuna mace na dauke da ciki amma wannan hoton bai iya nuna komai a cikin mahaifa ba, toh lokacin za'a tabbatar cewa cikin da mace ke dauke da shi yana zaune a bayan mahaifa ko wani wuri na daban. Daganan likita mai daukar hoton zai yi kokarin ya duba wuraren da yake tsammanin cikin zai iya dasa kansa. Wuraren da cikin yafi dasa kansa sune; bututun Fallopian, cikin kogon peritoneum, akan bakin mahaifa da kuma cikin ovary.
  3. Gwajin gane adadin sinadarin β-hCG a cikin jinin mace; Wannan ba dole bane, yawan sinadarin a cikin jinin mace yana nuna cewa mace tana dauke da ciki. Idan sinadarin yakai wani adadi yana kara tabbatar wa likita cewa cikin yana a wajen mahaifa.

Yadda ake maganin cikin da ya zauna a bayan mahaifa


Maganin cikin da aka samu a wajen mahaifa ya danganta da lokacin da aka gane cikin da kuma yanayin da mace tazo da shi.

Idan har ba'a yi saurin gane cikin ba har sai da ya fashe a cikin inda ya zauna (wanda mafi akasari yana fashewa ne a cikin bututun Fallopian) toh mace tana zuwa ne a cikin yanayin gaggawa tare da matsanancin rashin lafiya, ciwon ciki da kuma zubar jini daga gabanta. A irin wannan yanayi ya zama wajibi ayi aikin tiyata cikin gaggawa domin cire wannan ciki da kuma ceto rayuwarta. Haka kuma za'a kara mata jini idan tayi asarar jini mai yawa.[¹][²]

A daya bangaren kuma, idan akayi saurin gane cikin mace yana zaune ne a bayan mahaifa ko wani wuri da bai kamata ba. Da farko za'a iya zura masa ido tare da bibiyar sa akai akai da fatar zai gangara ya koma cikin mahaifa. Idan yaÆ™i komawa bayan wa'adin da aka diba ya cika, sai ayi aiki ko ayi wasu alluran da zasu sa cikin ya tarwatse.[²]

 Kammalawa 

Ectopic pregnancy shi ne samun ciki a wajen mahaifa. Samun irin wannan ciki babbar matsala ce, saboda cikin ba zai iya girma yakai mizanin haihuwa ba. Ya zama wajibi a raba mace da cikin ta ko wane irin hali, saboda barin sa yakan sa ya cigaba da girma har ya fashe cikin ciki ya kawo zubar jini mai matukar hadari ga rayuwar mace.

Idan mai kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake Æ™asa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 

Nassoshi 


Print this post

Post a Comment

0 Comments