Yadda Ake Saduwar Aure: Abubuwan Da Ya kamata Mata Su yi Kamin Saduwa

Yadda ake saduwa


1. Me Ya Kamata Mace Ta Chi Kamin Saduwa?

Ba ko wane irin abinci mace ya kamata taci ba kamin tayi kwanciyar aure da mijinta, domin da akwai wasu abincin da ba su dace mace ta chi su ba daf da lokacin da za ta soma saduwar aure. Domin wasu kalan abincin suna iya ragewa mace ni'ima ko kuma su kwantar mata da sha'awa na saduwa, don hake ne ya zama dole mace ta san irin abinci da ya kamata taci kamin gudanar da jima'i.

Abinci mai nauyi bai kamata mace taci ba a  sa'o'i hudu ko uku kamin ta soma jima'i da mijinta a cewar Anna Robensun wata mai illimin girke-girke. A nazarin Mrs. Anna abinci mai nauyi yakan jawo kasala ga mace kuma ya hana ta kuzari a lokacin saduwa, inda ta bada shawarar cewa duk matar data san da akwai aikin kwanciya na jima'i a gabanta to dole ne ya kasance sa'o'i 6 kamin lokacin da zata sadu da mijinta ba ta chi abinci mai nauyi ba.

Dukkanin masana illimin girke-girke da kayan maÆ™ulashe sun nuna cewa, mace kamin saduwar aure abincinta ka da ya wuce abinci mara nauyi, kuma ya kasance mai ruwa-ruwa ba busashe ba. Abinci irinsu taliya mai ruwa-ruwa, fatai-fatai da ire iren su, sune abinci da mace za ta ci kamin jima'i. 

Haka kuma kifi ko soyayyen kwai mai ruwa-ruwan wanda bai soyu sosai ba yafi dafaffe amfani a jikin mace kamin jima'i. Haka shima ferfesu da naman da aka gasa mai ruwa-ruwa a jiki yafi tsirai ko balangu amfani a jikin mace kamin saduwar aure.

Abubuwan sha irin su madara da zuma, su lemun zaki ko mai tsami, haka su kunun aya ko juice suna da amfani a jikin mace kamin saduwa. Haka kuma abarba, kwakwa, kankana, ayaba da lemun bawo suna da amfani mace ta chi kamin kusantar miji. 

Amma kuma mata su sani cewa, kada ki cika cikin ki sosai da abinci awa daya da rabi kamin soma saduwar aure, shi yasa ake buÆ™atar chin abinci ya kasance shi ne abu na farko da mace za ta fara yi a shirin ta na tunkarar jima'i, domin abinci ya narke kamin lokacin da za ta sadu da maigidan ta. 

Muddin mace ta tunkaro jima'i bayan ta cika ciki taff, toh akwai yiwuwan za ta iya yin amai, haka kuma tana iya gajiya da wuri watakila tun kamin mijin nata ya samu gamsuwa da ita wanda hakan kuma illa ne babba.

Wadannan abinci dana sha da muka ambata a sama dukkanin su suna da matukar amfani da mahimmanci a jikin mace. Shi yasa dukkannin abincin da muka ambata suna karawa mace ruwane da kuma ni'ima a jikinta, wanda hakan zai kara mata jindadin jima'in ita kanta da mijinta. 

2. Gyaran Dakin Saduwa

Abu na gaba a cikin jerin abubuwan da mace za ta yi kamin jima'i shi ne ta gyara dakin da zasu kwanta da mijinta domin jima'i bayan ta samu abincin da muka ambata ko masu kama dasu tayi kalachi.

Dole ne mace tayi wa dakin kwanciyar jima'i ko saduwar aure gyara na musamman ba irin gyran ɗakin da take tsammanin zuwan ƙawaye ko 'yan uwa ko abokan miji ba. Dakin kwanciyar jima'i ko saduwar aure yana bukatar tsafta kamar kowani ɓangare na gida, haka kuma yana buƙatar a kauda duk wani dauɗa ko abu mai wari, ɗoyi, zarni ko tsami daga cikin ɗakin.

Ɗakin kwanciyar jima'i ko saduwar aure baya bukatar fitila mai haske haka kuma yana bukatar mace ta bulbule shi da turare mai ƙamshi musamman wanda ta san maigidan ta yana sha'awar kamshin sa. Haka kuma ana son mace tayi amfani da zanin shimfiɗa mai dauke da zanen fulawa ko kuma mai wani alamomi na motsa sha'awa. Shima wannan shimfiɗar dole ne a bishi da turare ko ina har da matashin kai na shimfiɗar.

Wasu masana jima'i suna ganin cewa yana da kyau mace ta samu wani waÆ™a mai sosa zuciyar masoya ta saka yana tashi kamin wannan lokacin, hakan a cewar su shi ma wani tsimi ne dake ratsa zuciyar ma'aurata tare da kuma zaburar da sha'awarsu. 

Haka kuma É—akin jima'i ana bukatar jin sa da sanyi mara cutarwa musamman ga mazajen da basu bukatar sanyi, dole mata su tabbatar da dakin da za suyi kwanciyar jima'i ko saduwar aure da mazajen su ba ya dauke da zafi, domin mafi akasarin maza basa bukatar yin jima'i a yanayi mai zafi ganin jima'i yana haifar da yin zufa ko da kuwa dakin nada sanyi.

3. Yin Wanka Kamin Saduwa 

Dole ne mace tayi wanka na musamman kamin lokacin ta na jima'i, domin shi wanka na jima'i ya bambanta da sauran wankan da mata ke yi na zuwa kasuwa, unguwa wajen aiki ko sana'a, shi wanka na jima'i da akwai wasu muhimman wuraren da sune akafi la'akari dasu a lokacin wanka, don haka da zaran an tsaftacesu wankan jima'i ya samu.

A lokacin da mace za ta shiga wankan jima'i, dole ta tabbatar da cewa sabulun da zata yi wanka dashi yanada Æ™amshi da mijinta yake so, kada ta sake tayi amfani da wani sabulun da tasan cewa mijinta baya bukatar jin Æ™amshin sa, domin hakan yana iya kauda masa sha'awar jima'i gaba daya. 

Yadda ake saduwa

Saboda haka dolene mata su fahimci irin sabulun da mazajen su ke so domin yin amfani da shi a wajen wanka kamin fara saduwa. Namiji yana iya kawo wa matar sa sabulun wanka ba domin shi yana son ƙamshin sa ba, sai don ya fahimci matarsa nada sha'awar yin amfani dashi.

4. Yadda Ake Wankan Fara Jima'i 

Abu na farko shi ne, ki tabbatar da cewa kin wanke bakin ki tsaf da buroshi ko aswaki, ki tabbata babu wani wari da ke iya fitowa daga cikin bakin naki. A lokacin da kika shiga wankan fara jima'i, hamattanki, lungunan kunenki, matsaimatsinki, farjinki da kuma duburanki, ƙasan nonuwanki, sune manyan abubuwa kulawa a lokacinda ki ke wankan jima'i, domin dukkanin wadannan wuraren sunada matukar mahimmanci a jima'i, (za ayi bayanin amfaninsu a gaba).

Don haka warin É—aya daga cikin su yana iya hana mijin ki kusantar ki. Saboda haka mata su tanadi kayan tsaftace wadannan wuraren na zamani domin yanzu haka ana samunsu.

4. Kwalliya Kamin Jima'i 

Bayan mace ta fito daga wankan ta na fara jima'i, abu na gaba dake gabanta a shirye-shiryen ta na kwanciyar jima'i shi ne, kwalliya kamin jima'i. Domin muddin mace bata san yadda zatayi kwalliyar ta na jima'i ba, yana da matukar wahala ta iya shawo kan mijinta a wannan daren domin ya sadu da ita.

Mafiya yawan mata suna dauka cewa da zaran mace tayi wanka ta wanke waÉ—ancan wuraren da muka ambata a baya shi kenan ta gama mai wuyan a kokarinta na shawo da kuma motsa sha'awar mijin ta suyi jima'i, ba tare da sanin cewa wanka babu kwalliya maigida ba zai sanma anyi ba.

Kwalliya na fara jima'i shima yana da banbanci da sauran kwalliyar da mata ke yi, domin shi wannan kwalliyar akasarin sa anayin sa ne da kayan kwalliyan da suke da Æ™amshi na motsa sha'awa. Kwalliya ne da baya buÆ™atan gazal, jam baki, ja gira, fankeke bare kuma foda a fuska. 

Kawai abunda wannan kwaliyar yake bukata shi ne ki tabbatar da cewa kinada man sanya baki ƙamshi, tare kuma da samun wata alawa ko chingam mai kamshi ki sanya a baki. Haka kuma ki tabbatar da cewa, idan mijin ki baya bukatan gashi a gaba ki tabbata kin aske a lokacin wanka, idan kuma yana bukata sai ki shafa masa man gashi mai sheƙi da kuma ƙamshi.

Hamattanki da kuma matsematsinki suma ki tabbatar da cewa sun samu turare mai ƙamshin gaske. Gyara gashin kanki a wannan lokacin ya zame maki dole, domin mace da gashin kanta kawai tana iya ɗimauta namiji idan har tasan yadda za ta sarrafashi, don haka yana da kyau mace ta gyara gashin kanta sosai ta hanyar wanke shi da kuma sanya masa man gashi mai ƙamshi irin wanda tasan mijinta yana buƙatar jin ƙamshin sa ba irin mai warin nan da wasu mata ke sanyawa wanda kuma akasarin maza basu bukatar ƙamshin sa.

Man shafin da zaki shafa a lokacin kwalliyar ki na fara jima'i shi ma abun la'akarine, dole ne ki tabbatar da cewa man mai sa taushin jikine ba mai busar da jiki bane, domin namiji baya bukatar jin jikin mace a bushe. Haka kuma ki tabbatar da cewa hannunki kin shafe shi da man shafawa mai laushi domin hannun shine sarkin aiki.

5. Ado Kamin Saduwa 

Bayan mace ta kammala kwalliyar ta na jima'i, abu na gaba shine ado ta hanyar sanya tufafi, domin shi ma jima'i yana da tasa irin adon daya kamata mata suyi masa amma akasarin mata basu da fahimtar hakan. Don haka shi ke sa wasu matan bayan sunyi wanka sunyi kwalliya sai kuma suga mazan basu kula ba, wannan kuwa na faruwa ne saboda rashin ƙarasa wannan kwalliyar da akayi da ado mai kyau.

Adon kwanciyar jima'i ba a sanya masa zobe, sarka ko a warwaro. Haka kuma ba a daura masa atamfa ko sanya masa wando mai tauri irin jeans, abin da adon jima'i yake buƙata shi ne kaya masu nuna tsiraici, kaya masu shara-shara, kayan da zasu fito da nonuwanki a kamar a fili, kayan da mijin ki zai dinga hango kan nonuwanki, kayan da zasu rika fito da kuma nuna motsin ɗuwawunki a duk lokacin da kika motsa.

Ado na jima'i yana son mace ta sanya kayan da baza su danne hakkin É—uwawun ta ba idan kina bukatar son juyawa mijinki. Kaya ne da babu damuwa idan sun fito da sashen cinyoyin ki a fili, ko kuma suna baiwa mijinki sararin haÉ—a idanuwa da tsiraicin ki. Akwai rigan nono da kuma wandon fatari na mata wanda da zaran mace ta yi adon jima'i dasu kamin mijin nata ma ya matsota yayi zuwan farko. Wadannan sune irin shiga na ado da yakamata mata su dinga yiwa mazajen su. Haka kuma da akwai riguna na bacci masu kyau da kuma sauki ga mata domin amfani dasu a lokacin adon su na fara jima'i.

6. Yanayin Lokacin Jima'i

Abu na ƙarshe a wannan babin kamin fara jima'i shi ne na zama dole mace tayi la'akari da lokacin da ya kamata ta shiryawa jima'i ganin shi lamari na jima'i lamari ne dake bukatar lokacin da babu wani da zai shiga rayuwar ma'aurata.

Kashi 80 cikin 100 na ma'aurata sun fi son yin jima'i a tsakiyar dare ne domin ganin cewa shi ne lokacin da babu wani da zai shiga rayuwar su, don haka mace ta tabbatar da cewa kamin ta shirya yin jima'i babu wani da zai raba mata hankali. 

Ta tabbatar da cewa idan ita mai shayarwa ce ta shayar da ɗanta nono har lokacin da take tunanin ba zai sake tashi ba. Haka kuma idan tana da ƙananan yara, ta tabbatar sunyi baccin da baza su sake neman kulawar ta ba. Idan tana da baƙi ko ƙawaye da suka kawo mata ziyara na kwana ta tabbatar ta kamala dasu. Haka kuma babu barin waya a kunne ko kuma duk wani abinda tasan cewa yana iya dauke hankalinsu a lokacin da suka soma jima'i.

Post a Comment

0 Comments