Tambayoyi da Amsa

Lafiyata logo


1. Aslm,Dr barka da safiya meyake kawo yawan yin fitsari sannan anfiso mutum ya yawaita fitsarin ko kuma rashinsa.

Amsa 1

Yawan yin fitsari ya danganta:

  1. Kina yawan fitsari amma idan kika je fitsari zai fito dan kaɗan ba da yawa ba.
  2. Kina yawan fitsari, amma idan kika je fitsari kina yin fitsari dayawa ko kuma normal yadda kika saba. Mafi akasari wannan zai saka mutum yawan shan ruwa, ko fitsari mai kumfa.

Na ɗaya alama ce ta urinary tract infection (cutar magudanan fitsari).

Na biyu kuma alama ce ta wasu cutuka. Musamman sugar. Haka kuma yanayin sanyi ma (cold weather) yana sa irin wannan yawan fitsari. Shi wannan ba cuta ba ce, idan yanayin ya wuce mutum zai daina.

Amsa 2. 

Waalaikum mussalam. 

Akwai abubuwan da ke sa yawan fitsari da dama:

Amma kafin inyi bayani kansu;

Yawan fitsari Wanda a likitance ake kira da _frequency_ yana nufin yin fitsari fiye da sau bakwai (7) a rana.

Wani lokaci mutane na misinterpreting dinshi da yin fitsari dayawa abinda akecema _polyuria_ aa likitance. Shi polyuria yana nufin volume and quantity din fitsarin ne yayi yawa.

To ga wani Dan bayani akan kowanen su.

In ya kasance yawan yin fitsarine na *frequency*

Sai alura; ko akwai

Ciwo in ana fitsar, ko yawan fitsari cikin dare( nocturia) ko akwai alamun jini cikin fitsari,ko akwai ciwon Mara, ko chanja kalar fitsari,ko discharge. 

Duk Alamomin da su ka gabata suna nuni ne zuwa ga UTI( urinary tract infection) wato infection na mafitsara. Sai shikuwa yawan fitsari na polyuria( wato yawanshi interms of volume and quantity) 

Yana zama cikin alamomi na ciwon sugar tareda; yawan Shan ruwa akai akai( polydipsia) ,yawan cin abinci akai akai(polyphagia) da kuma ciwon rama( weight loss). Sai dai akwai lokacin da yawan yin fitsari yake iya zama ba wani matsala ba; kamar lokacin sanyi saboda yanayin weather.

2. Dan allah kwanaki nawa ake dauka dantabbatar da test na hiv daka lokacin dakai zanrgin kanka.

Amsa

Daga lokacinda mutum ya samu exposure ta hanyar saduwa, ko amfani da sharps kamar su razor blade da sauransu da Wanda yake da cutar yayi amfani dasu ko kuma yaron da uwa mai cutar ta haifa.

Anayin gwajin ne bayan tsawon wata 6 domin banyan lokacin ne garkuwar jikin mutum ta isa tayi haifar da abinda zai fatattake qwayoyin halittar cutar, wato antibodies. 

Shi gwajin anayin sane domin duba su antibodies din da jikin mutum ya haifar Don su kareshi daga cutar. Bayan tsawon wata 6 idan aka duba akaga ba kwayoyin ajikin mutum, to lokacin zaace bayada wannan cutar daga exposure din da ya samu.

Amma akwai wasu gwaji da zasu iya nuna kwayoyin halittar cutar as early as har 3 weeks a yanzu. Ya Dan ganci wane irin test ne akayi.

Amma akwai wasu gwaji wadanda zaa iya ganin kwayoyin halittar dawuri kamar cikin 3 weeks ,6 weeks da sauransu.

Ya danganta daga wane irin test ne akayi. Akwai test dinda kwayoyin halittar suke dubawa( Antigen) akwai wand kuma kwayoyin garkuwar Dan Adam suke dubawa( Anti bodies)

Jan Hankali;

Maana Ana iya screening tests din aga negative bayan exposure. Amma bazaace ba cutar ba har sai anyi Antibody test bayan 6 months din anga babu.

3. Assalamualaikum Dan Allah docter ciki na be Kai 3month ba Amma inajin ciwon Mara jefi-jefi,ga matsanancin ciwon Kai da Nike Dama dashi kullum,Kuma tun kafin cikin yakai 2month Nike jin nauyi a marata,Amma cikin farko na ba haka naji ba,haihuwa tabiyu zanyi.

Amsa

Waalaikum mussalam!.

Yawan ciwon Mara a kowane lokaci na ciki abune Wanda yakamata ya jawo hankalin mai ciki amma musamman wata uku na farko domin lokacin ne ankafi samun zubar ciki. Sai ki lura, ciwon ciki ne kawai ko akwai fitar ruwa ko jini ta gaban mai ciki.

Ya kamata ko akwai ko babu zubar jinin ko ruwa aje aga likita a asibiti mafi kusa domin a kara tantancewa.

4. Assalamu Alaikum Likita barka da safiya. Don Allah ina neman karin bayani akan Pancreatic cancer.

Amsa

Waalaikum mussalam. 


Pancreatic cancer ,wato ciwon daji dake affecting din pancreas ( wani sashe na kayan cikin Dan Adam). Kamar kowane ciwon daji , yanasa, rama, kumburin ciki, ciwon ciki da sauransu.

Kamar sauran cutukan cancer: 

Rashin lafiyar yanada mataki depending on lokacin da akayi diagnosing marashi lafiya. Magani da ake bayarwa ya danganta da stage din rashin lafiya. Akwai Wanda ake bada drugs, wani Radiotherapy wani har surgery akeyi.

Amma : mafi yawancin cutar cancer baa warkewa saidai a bada magani domin inganta rayuwar Dan Adam.

5. Assalamu alaikum 

Likita barka da safiya. Dan Allah ina tambaya akan period bayan mace tayi 40 days, yaushe ya kamata ya kuma dawo mata?

Amsa 

Waalaikum mussalam.

Bayan lokacinda mace tagama 40 days( 6 weeks), wato Arba'in a hausance, daga lokacin halittar jikinta zata dawo kusan kamar lokacin kafin ta dau ciki. Kuma zata fara expecting dawo war ala'da daga lokacin.

Saidai saboda halittar dan Adam daban daban ne, mata zasu samu dawowar jinin su lokaci daban daban wasu har fiye da 6 months. 

Akwai abinda likitoci ke ma "lactational amenorrhoea" wato rashin yin al ada saboda shayarwa.

So saboda haka matan da ke shayarwa da kyau( wato breastfeeding) su kan iya daukar lokaci kafin dawowar jinin al ada fiye da wadanda basu shayarwa.

6. Assalamu alaikum barka da war haka dkt mai ke kawo jinkiri wajan samun haihuwa ga mace ?

Amsa

Rashin samun haihuwa a likatance yana nufin;

Rashin samun daukar ciki ga maaurata bayan wata goma sha biyu da yin aurensu tare da kasancewar suna saduwa da juna sau biyu zuwa uku na kowane sati har tsawon wata 12. A likitance bazaace maaurata basu haihuwa ba sai sun cika wannan dokar.

Rashin haihuwar maurata ba matsalace ta mace kadai ba. Takan iya zama matsalar mace , ko ta namiji ko matsalarsu baki daya.

I dan har maaurata basu samu haihuwa ba bayan tsawon wannan lokaci , akwai abubuwa da dama da yakamata ayi bincike kansu na daga tambayoyi har ma na gwaje gwaje.

Shawarace mai kyau a samu kwararren likitoci, wato gynecologist a asibiti mafi kusa domin tantance matsalar.

7. Ni tawa babyn rasuwa tayi, bayan nayi 40days da sati biyu jini ya dawo yake ta wasa dr. Akwai matsala faruwar hakan?

Amsa

Babu matsala dawo warshi bayan 40 days tunda baki shayarwa.

8. Slm doctor kurji ne yafitomin a gefan duburata shine naje chemist aka bani tab PCM da Diclofenac da ampiclox shene ya ya warke kuma yanxu Sai yadinga fitowa agorin Sai nasha nagani kuma Yanayi ruwa.

Amsa

Maganin da anka baka daidai yake.

Maganin ciwo ne sai kuma antibiotic .

Saidai yana yuwa ba asha maganin tsawon lokacin ta ya kamata ba ko kuma yanda ya kamata.

Haka zalika yana yiwuwa abinda ke damunka yafi ƙarfin antibiotic kawai, akwai abubuwan da ke iya fitowa a gefen dubura masu fitar da ruwa, waɗanda ke bukatar aikin tiyata kamar irin su fistula-in-ano, ischiorectal abscess da dai sauransu.

Shawara shi ne kaje asibiti babba domin a bincika. Kuma sai akiyaye akan hygiene din wurin shima zai taimaka sosai.

9. Sorry Dr ba matsala daga kasha ruwa kayi fitsari kuma narage Shan ruwa saboda yawanyi fitsari?

Amsa

Ka karanta rubutun da Dr. ⁨Yusuf Ayama⁩ yayi a sama game da yawan fitsari sai ka auna da naka zaka gane idan yanayin ka akwai matsala ko babu.

10. Slm barka da sfy Dr. Dn Allah meye kesa gashin jikin mutun ketashi?

Amsa

Tsima ko tashin gashin jiki ko abinda ake cema goosebumps alama ce kawai ta sympathetic overdrive. Kowa na iya samun haka a lokacin da ya shiga wani yanayin da zai yi activating na sashen ƙwaƙwalwar shi da ake kira da sympathetic nervous system. 

Ba takamaiman ciwon da zamu ce miki gashi shi ke kawo yawan tashin gashin jiki. Amma idan kinji kamar naki yayi yawa kije asibiti domin ayi miki gwaje-gwaje da bincike domin tabbatar da matsalar ki.

11. Assalamu alaikum doctor dan Allah ywan xazzabi yana ga illa gamai juna biyu?

Amsa

Sosai kuwa, yawan zazzaɓi yana da illoli da dama ga mai ciki har ma da abin da ke cikinta. Kadan daga ciki:

  1. Zai iya kawo zubewar ciki
  2. Zai iya hanawa abinda ke ciki girma yadda ya kamata
  3. Zai iya kawo mutuwar jariri a ciki. 
  4. Zai iya haifarwa mace mai ciki ƙarancin jini
  5. Ya danganta kuma me ya kawo yawan zazzaɓin, wasu infections suna iya sakawa yaro naƙasa.

Don haka, idan mace tana da ciki daga taji zazzabi ta garzaya asibiti mafi kusa domin samun kulawar da ta dace.

12. Toh Dan Allah wane rigakafi za abani indai nasamu ciki banda ciwo sai zazzabi.

Amsa

A farkon ciki mafi yawancin mata na yawan samun laulayi da yawan zazzaɓi saboda a wannan lokacin garkuwar jikin su ta kan ɗan yi rauni domin jure baƙon cikin da mace ke dauke dashi. Wannan shi yasa 'yan ƙananan cututtuka zasu yi amfani da wannan damar su kawo wa mace yawan zazzaɓi da wasu cutuka.

Bugu da kari, wannan lokaci ne mai muhimmanci da ba ko wane magani ake ba mace ba, saboda wasu magunguna su kan iya interfering da girman abinda ke cikin ciki, wasu kuma kan iya zubar da cikin.

Saboda haka babu wasu magungunan da ake ba mace domin kareta daga zazzabi a irin wannan lokacin, sai dai ana ba ta shawarwari kamar haka:

  1. Kiyayewa da kwana a cikin gidan sauro domin samun kariya daga cutar cizon sauro ta maleriya
  2. Kiyayewa da tsaftar jiki da kuma toilet hygiene domin kariya daga cutar magudanan fitsari, wasu masana suna ba mace vitamin C sau uku a yini domin kariya daga UTI.
  3. Ana yiwa mace allurar TT har guda biyar domin kariya daga cutar tetenus.
  4. A lokacin da cikin ya tasa yakai makonni 18 za'a fara ba mace ƙwayoyin fansidar domin kariya daga maleriya duk wata har sai ta haihu.
  5. Haka kuma a duk lokacin da taji zazzabi ana ba bata shawara ta garzaya a asibiti domin samun kulawar da ta dace.

13. Aslm dn Dr mikesa yawan ciwon kai?

Amsa

Migraine headache shi ne yafi kawo wa mutane yawan ciwon kai a al'ummar mu. Amma causes na ciwon kai suna da yawa aje a ga likitan ƙwaƙwalwa.

14. Dr dan allah tabbaya shine yawan infaction wallahi dr nakai shekara da rabi inashan mgn infaction idan yatafi sai yadawo kullum inayanwa asibity dr to sai yau nashi ga tictok naga wata dr tana bayani akan yawan infection wani sain matselace ta houman inbalan kwayoyin mahaifa suke rikice kuma abaya natabashan mgn planining na possino dan allah ko zakitaimaka kirubu damin mgn homan inbalanc ko zantace gashi shutu ba haihuwa kudai makamin ngd.

Amsa

Ki koma asibiti a tabbatar da hormonal imbalance ne ke damunki kamin a doraki kan maganin da ya dace. Amma akan kawai kina tunanin kina fama da yawan infection da kuma wani bayani da kika ji a kafar tiktok ba daidai bane ni in doraki akan wani maganin hormonal imbalance.

Ya kamata mutane su gane wannan dandalin ba asibiti ba ne, kuma ba zai taɓa maye gurbin zuwa asibiti ko ganin likita ba, shafi ne na fadakarwa, wayar da kan jama'a da kuma tura su a inda ya dace domin samun ingantaccen kulawa.

15. Assalamu alaikum inayiwa likita ftn alkhairi,Dan Allah likita mi ke kawo yawan jin yunwa da zarar mutum yaci abinci lkci kadan kamar Bai ciba se ya koma ci.

Amsa

Tsutsar ciki na yawan kawo haka, anason kowa ya rinƙa deworming kansa akalla sau biyu a shekara ta hanyar shan kwayar maganin albendazole 400mg ƙwaya ɗaya tak.

16. Assalam alaikum, barka da wuni Dr, Please I’ve something that was bothering me for a long period of time, shine nace bara nayi tambaya koda xan iya samun solution

Wallahi narasa meyassa duk time da tafiya ya kamani, whether by vehicle or aircraft, 30 minutes baya wucewa sai amai yafara damuna**

A takaice dai duk xanyi tafiya kusan sai nayi amai a hanya. So, please i need to know… what really be the cause of such to me?

Nagode sosae!🙏

Amsa

Wannan yana damuwar mutane dayawa. Ba cuta ba ce, ana kiransa "motion sickness" da turanci. Yana faruwa ne sanadiyyar yanayin da ƙwaƙwalwar wasu ke samun kanta a lokacin da abin hawan da suke kai ke gudu.

Yadda ake maganin haka shi ne. Da ka shiga mota ko jirgi ka ɗauko ɗaya daga cikin wadannan magungunan kasha

Tabs Navidoxine 25/50mg stat

Ko kuma

Tabs Promethazine 25mg start

Insha Allah ba zaka samu wannan amai ba har ku sauka.

17. Salam Dr dan minene alamomin ciwon hakin wuya?

Amsa

Malam ba wani cuta da ake kira cutar hakin wuya. Cire hakin wuya al'ada ce ta gargajiya da akeyi a bisa rashin ilmi. Ana kiran cire hakin wuya traditional uvulectomy da turanci.

Wannan abun da wanzamai da sauran mayu ke kira hakin wuya, sashe ne na ganɗa ma'ana soft palate a turance. Gaɓa ce ta furuci wanda kowa na da shi, sai dai na wani yafi na wani girma.

Kuskure ne babba daga yaro ya fara samun canjin murya ko ciwon maƙoshi sanadiyyar mura ko wani respiratory tract infection sai a kai shi wurin wani maye ace hakin wuya ne ke damun sa. Sai ayi amfani da aska a cire.

Wasu mutane ma suna cirewa haka kawai ba tare da yaro ya samu wani alamun komai ba, saboda jahilci.

Akwai illoli sosai wajen cire wannan hakin wuya kamar haka:

  1. Zubar da jini; wasu yara su kan zubar da jini sosai har su mutu, saboda suna zubar da jini a cikin baki suna hadiyewa ba'a saurin ganewa.
  2. Yaɗuwar cututtuka kamar su hepatitis B & C da kuma HIV.
  3. Matsalolin furta wasu kalmomi.
18. Slm Dr dn Allah mekesa macce taji gabanta Yana danmata ciwo kadan Amma ba kowani lkc yk yiba?

Amsa

Vulvovaginitis infection ne da ke iya shafuwar gaban mace da kuma chan cikin farjinta. Yana bayyana ne ta hanyar;

  1. Ƙaikayin gaba ko ciwo
  2. Kumburin gaba
  3. Discharge mai wari
  4. Jin zafi yayin fitsari
  5. Jin zafi yayin saduwa
  6. Da kuma zazzaɓi

Kammalawa 

Zaku iya shiga WhatsApp group dinmu domin turo mana naku tambayoyi ta hanyar danna hoton WhatsApp da ke hannuku na hagu a ƙasa. Idan kuma group din yana kulle zaku iya turo mana tambayoyin ku ta private message.

Post a Comment

0 Comments