Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Wayar da kan jama'a akan alamomin ciwon daji/kansar kwan haihuwa na mata (Ovarian Cancer Awareness)

Cutar kansar kwan haihuwa


A kowace shekara a Burtaniya mutane 7,000 ne ke kamuwa da cutar kansar kwan haihuwa na mata. Mutane da yawa da suke fama da wannan cutar kansar suna fara samun bayyanar alamomin kansar na tsawon watanni amma suyi watsi da su a matsayin matsalolin da ba komai ba, ko kuma su alaƙanta su da alamomin lokacin haila ko tsufa. 

Yawancin mutanen da ke fama da cutar kansar ƙwan haihuwa na mata, ana gano su ne lokacin da ciwon kansar yayi nisa har ya kai ga yaɗuwa a sauran sassan jiki, wanda a irin wannan yanayi, lokacin da za'a iya magance kansar ya riga ya ƙure.

Sanin alamomin ciwon daji ko kansar kwan haihuwa yana da mahimmanci domin gane ciwon sauƙaƙe kuma tun a cikin lokacin da za'a iya wani magani. Babu shakka, saurin gane ciwon yana inganta sakamakon hanyoyin maganin da za'a bi.

Domin sauƙin wayar da kan jama'a game da cutar kansar ƙwan haihuwa, ƙungiyar bada tallafi ta overcome da ke ƙasar Burtaniya ta fidda wata gajeruwar kalma da ta ƙunshi mafiyawancin alamomin da cutar kansar ƙwan haihuwa ke nunawa a lokacin da ta ke farko. Wannan kalmar ita ce kalmar "BEACH".

Abu ne mai kyau ga kowace mace ko mata maza masu ƙwan haihuwa su san wadannan alamomin da ke kunshe a cikin kalmar BEACH.

Alamomin Ciwon Daji Ko Cutar Kansar Kwan Haihuwa 

Ma'anar Kalmar BEACH

B - Bloating (Cushewar Ciki)

Yawan kumburin ciki ko cushewar ciki na daya daga cikin manyan alamomin ciwon daji ko cutar kansar ƙwan haihuwa na mata, idan mace na fama da cushewar ciki da yaƙi ci yaƙi chanyewa to ya kamata ta tuntubi likita domin tabbatar da abinda yake kawo mata wannan cushewar ciki, musamman idan ta kusan kai shekaru 45 a duniya.

E - Easy Satiety ( Saurin Ƙoshi)

Idan mace na samun saurin ƙoshi da abinci, ko kuma saurin cushewar ciki daga taci abinci dan kadan wanda kuma ba haka ne ɗabi'ar cin abincin ta ba, watakila yanzu ba ta iya cinye ko rabin abincin da ta saba ci a baya, toh shi ma wannan yana iya nuni zuwa ga cutar kansar ƙwan haihuwa.

A - Abdominal Pain (Ciwon Ciki)

Idan mace na yawan samun cushewar ciki tare da ciwon ciki ko ciwon mara a ɓangaren hagu ko na dama, ko ciwon baya, wannan ma zai iya zama alama ta ciwon dajin ƙwan haihuwa na mata.

C - Changes in Bowel and Bladder Habit (Samun Canji Wajen Yin Bahaya Da Fitsari)

Yawan yin fitsari ko gudawa ko rashin yin bahaya akai-akai duk yana iya nuni zuwa ga a kansar ƙwan haihuwa na mata. Bugu da ƙari, yawan samun kumburin ciki, rashin narkewar abinci da jin amai duk na iya zama alamomin kansar ƙwan haihuwa na mata.

H - Heightened Fatigue (Yawan Kasala/ Doguwar gajiya)

Yawan kasala ko yaushe ko yawan gajiya ba tare da anyi wani aiki ba, na iya zama sanadiyyar kansar ƙwan haihuwa na mata, har dai idan kasalar ta hanawa mace nishadi ko yin ayyukan ta na yau da kullum.

Akwai wata babbar alama ɗaya wadda kalmar BEACH ba ta ƙunsa ba, wannan alamar ita ce, yawan ramewa. Idan mace ta lura tana ramewa, rama wadda babu gaira ba dalili, duk ta cewa tana cin abinci yadda ya kamata, kai ko ma cin abincin ta ya ragu, toh ta garzaya asibiti domin gano asalin wannan ramar, domin tana iya zama alamar kansar kwan haihuwa.

Kammalawa 

Wadannan sune muhimman alamomin da kansar ƙwan haihuwa na mata ke nunawa a lokacin da take farko. A lura cewa samun daya ko biyu na wadannan alamomi ba shi ke nuna cewa mace tana da kansar ƙwan haihuwa na mata ba, amma idan mace tana samun mafi yawa daga cikin wadannan alamomin toh ya kamata ta garzaya asibiti domin duba lafiyar ta.
Print this post

Post a Comment

0 Comments