Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Alamomin Nakuda: Yaushe Ya Kamata Mace Mai Ciki Taje Asibiti Haihuwa

Gabatarwa:

Alamomin Nakuda

Masana ilimin kimiyyar mata masu ciki da al'aurar mata sun bada ma'anar nakuda a matsayin wani al'amari dake tasowa sannu - sannu ga mata masu ciki wanda zai iya sanadiyyar fitar ciki da duk abinda ke cikin mahaifa tare dashi ta hanyar farji bayan cikin ya shafe wa'adin da zai iya rayuwa a wajen mahaifa.

A kimiyyar haihuwa an kasa nakuda gida biyu kamar haka;

  • Matakin nakuda na farko: Wannan shi ne a lokacin da bakin mahaifa ya fara budewa domin haihuwa har zuwa lokacin da zai bude baki daya. 
  • Matakin nakuda n biyu: Wannan matakin yana farawa ne bayan bakin mahaifa ya bude baki daya zuwa lokacin da za'a haihuwar jariri.
  • Matakin nakuda na uku: Wannan shi kuma yana farawa ne bayan haihuwar jariri zuwa lokacin da aka fitar da uwa (placenta).
Mafi yawancin alamomin nakuda suna faruwa ne kamin shigar nakuda matakin farko (pre labour signs and symptoms) da kuma a lokacin da nakuda ke a mataki na farko.

Manyan Alamomin Nakuda

1. Ciwon mara

Yadda alamomin nakuda ke farawa ya danganta daga wata mace zuwa wata mace, amma mafi akasarin mata ciwon mara shi ne alama ta farko da ke nuna cewa nakuda ta fara.

Ciwon mara na nakuda yana kama da irin ciwon marar da mata ke yi a lokacin al'ada, amma shi na nakuda yana tasowa ne sannu - sannu sannan ya cigaba da yawaita kuna yana yin tsanani har sai mace ta haihu. Mata suna kwatanta shi da murɗawar mara mai zuwa yana kwantawa da kansa.

Ciwon mara na nakuda yana iya zuwa har a bayan mace, sai taji kamar an riƙe mata baya, haka kuma wani sa'ilin yana sauka a ƙafafu.

Ciwon marar nakuda yana tasowa da kansa kuma idan ya taso ba abinda mace zata iya yi ta kwantar dashi, sai dai yana kwantawa da kansa bayan ya dauki wani dan lokaci kamin daga baya kuma ya sake tasowa. A haka zai cigaba yana yawaita da tsananta har sai an haihu baki daya.

2. Zubar majina mai haɗe da jini kadan daga gaban mace

A lokacin da ciwon mara ya fara ko kuma kamin ya fara, mace zata iya ganin wani majina mai dauke da jini kadan yana mata zuba a gaba. A turance ana kiran wannan da "passage of show". Wannan babbar alama ce da ke nuna bakin mahaifa ya fara budewa kuma nakuda ta fara shiga matakin farko saboda wannan majina tana fitowa ne daga bakin mahaifa.

A lura cewa, jinin da yake dauke a cikin wannan majinar bayada yawa, wani sa'ilin ma mace ba zata ga jinin ba sai dai ta ga majina mai duhu. Saboda haka idan mace taga jini ya barke mata ko jini zallah na yi mata zuba sannu-sannu, toh wajibi ne ta garzaya asibiti da sauri saboda wannan alama ce ta babbar matsala.

3. Buɗewar bakin mahaifa 

A lokacin da nakuda ta fara, bakin mahaifa yakan fara buɗewa sannan ya takura ya shige a cikin mahaifar domin baiwa kan jariri hanyar fitowa. Wannan ita ce babbar alamar da ke nuna cewa mace ta fara nakuda. Sai dai bayan zubar majina mai ɗan jini da muka yi bayani a baya, ba wani alama da mace za ta gane bakin mahaifa ya fara buɗewa. Gane wannan sai mace tazo asibiti idan likita ko unguzoma sun sanya yatsu a gaban ta.

4. Fashewar faya

Faya wata siririyar fata ce da take dauke da ruwan zaƙi wanda yaro yake iyo a cikin sa. Faya da kuma ruwan da ke cikinta sun zama kamar wata gagarumar ƙorama a cikin mahaifa da yaro yake iyo a ciki. Wannan ruwan ya samo asali ne daga fitsarin da jariri ke yi a lokacin da yake a cikin mahaifa.

Fashewar faya tana daya daga cikin manyan alamomin nakuda. Lokacin da faya ke fashewa ya danganta daga wata mace zuwa wata mace ko ma daga wani ciki zuwa wani ciki. Wata fayar ma ba za ta fashe dakanta ba sai an fasa ta a asibiti. Wannan shi yasa watarana idan an haihu a gida ana iya haihuwar jariri a cikin jikkar faya sai an fasa an fidda shi, amna wannan bai faye aukuwa ba.

A lokacin da faya ta fashe mace zata ga ruwa mai yawa ya ɓarke mata har ya jika jikinta, tufafin ta da kuma gadon da take kai. Hakan kuma wani sa'ilin faya takan fashe sannu a hankali ta yadda mace ba zata ga ruwan dayawa ya barke mata ba, sai da ta kama ganin ruwan sannu-sannu yana mata zuba yana bin ƙafafuwan ta.

A lura cewa, watarana wasu matsaloli sukan iya sa faya ta fashe kuma nakuda bata fara ba, wannan wani al'amari ne mai bukatar kulawa a asibiti. Idan har mace ta ga farin ruwa marar kauri, marar yauƙi na mata zuba har yana bin jikinta kuma ba tare da ta soma jin wasu alamomin nakuda ba, toh wajibi ne ta ruga asibiti.

Alamomi masu nuna nakuda ta kusa farawa

1. Idan ciki ga cika watanni tara

2. Saukowar kan jariri a cikin mara

3. Yawan fitsari akai-akai: A lokacin da ciki ya tsufa kan jariri yakan sauko a ƙasan marar mace. Wannan saukowar takan sa kan jariri ya ɗan taushe mafitsarar uwa wanda haka zai sanya adadin fitsarin da mafitsara ke iya riƙewa ya rage. Wannan shi kesa mace zuwa fitsari akai-akai.

4. Ciwon baya

5. Gudawa ko rashin yin ban haya

Yaushe mai nakuda ya kamata taje asibiti

A duk lokacin da mace ta lura da daya daga cikin manyan alamomin nakuda da muka ambata a sama toh ya kamata ta garzaya zuwa asibiti domin ganin unguzoma ko likita.

Idan mace taje a asibiti da alamomin nakuda za'a duba ta domin tabbatar da nakuda ta fara. Ana tabbatar da nakuda ta fara ne idan an sanya yatsu a gaban mace an tabbatar da cewa bakin mahaifa ya fara budewa.

Idan har bakin mahaifa yayi buɗewar da zai iya ɗaukar yatsu biyu da ake sanya wa a gaban mace, toh a lokacin ne za'a iya ba mai nakuda gado a ɗakin haihuwa domin cigaba da nakuda da kuma samun kulawa ta musamman a asibiti.

Idan kuwa bakin mahaifa ya fara buɗewa amma bai yi buɗewar da za'a iya sanya yatsu biyun ba. Toh a lokacin nakuda ta fara amma bata kai kimanin da za'a kai mace ɗakin haihuwa ba. A irin wannan yanayi za'a iya ba mace shawarar ta koma gida ta dawo bayan wani dan lokaci. Ko kuma ta dawo idan har taji ciwon mara ya yawaita kuma ya tsananta, ko kara jin wasu alamomin.

Kammalawa 

Nakuda al'amari ne dake tasowa domin haihuwar abin da ke ciki ta gaban mace. Mata suna bukatar kulawa ta musamman a lokacin da suka shiga yanayin nakuda, akwai alamomi daban daban masu nuna nakuda ta fara ko kuma nakuda ta kusan farawa.

Print this post

Post a Comment

0 Comments