Gabatarwa:
Ciwon mara a lokacin jinin haila abu ne da ke yawan damuwar mata musamman matasa 'yan shekara sha huÉ—u (14) zuwa ashirin da biyar (25). Yana da kyau a gane cewa ciwon mara wanda ke zuwa daf da mace zata fara jinin al'ada ko bayan ta fara, mafi akasari ba abu ne wanda wata cuta ko rashin lafiya take kawo wa ba.
Wane irin ciwon mara ne ke da alaƙa da jinin haila
Ciwon mara da keda alaƙa da jinin haila shi ne wanda ke zuwa daf da mace zata fara ganin jinin haila ko da zarar ta fara. Yana zuwa cikin kwana ɗaya ko biyu kamin farawa ko bayan farawa haka kuma zai daina kamin ta gama ko kuma daga zarar ta gama. Yana sanya mata rashin walwala da ɓacin rai wata rana har suji kamar sun shiga ƙunci!(mood swings). Haka zalika yana iya zuwa tare da amai ko gudawa ko tashin zuciya ko kasala. Yanayin wannan ciwo idan ya fara shi ne yakan taso ya kwanta kamin ya ƙara sake sake tasowa.
Me yake sa ciwon mara a lokacin jinin haila/al'ada?
Muhimman abubuwan da ke cikin marar mace sune mahaifar ta da sauran al'aurar ta. Ciwon mara a lokacin jinin haila ko al'ada yana faruwa ne saboda takura da mahaifa ke yi a lokacin da naman jikin ta yake mammatsewa domin tilasta jijiyoyin jinin maihafa su fashe su fara fitar da wannan jinin na haila. Wannan takurar da mahaifa ke sha a lokacin da namanta ya fara mammatsewa yakan hana ta samun isasshen jini da iska, rashin isashen jini da iska shi ne zaisa mahaifa ta fara fitar da wasu sinadarai na frostaglandins (prostaglandins) wanda sune musabbabin jin ciwon mara.
Dangane da abubuwan da ke sa ciwon mara a lokacin jinin haila likitoci masu ƙwarewa ta musamman a fannin kula da mata masu ciki da al'aurar mata (Obstetrics and gynecology) sun raba ciwon mara a lokacin jinin haila gida biyu (2) kamar haka;
1. Ciwon mara a lokacin jinin haila kashi na farko.
Wannan kalan ciwon marar ba abinda ke kawo shi face abinda muka ambata a baya. Shi wannan ciwon baya da alaƙar komai da wata cuta ko rashin lafiya. Kusan ko wace mace zata ɗanɗane shi a rayuwar ta, sai dai na wasu matan ya fi na wasu. Ciwon ya fi tsanani ga mata matasa sabbin fara al'ada, kuma tsananin shi yana ragewa kaɗan-kaɗan lokacin da mace take ƙara shekaru. Wasu matan ciwon yakan daina baki ɗaya bayan sunyi haifuwar farko.
2. Ciwon mara a lokacin jinin haila kashi na biyu
Wannan ciwon mara shi ne ake alaƙan ta wa da wasu cututtuka ko rashin lafiya. Cututtuka da ke kawo irin wannan ciwon sun haɗa da:
1. Endometriosis: Wannan shi ne samun ƙwayar tantanin halittun bangon mahaifa na ciki a wani guri da ba mahaifa ba, musamman cikin kwankwaso.
2. Adenomyosis: Samun ƙwayar tantanin halittun bangon mahaifa na ciki, a cikin naman mahaifa (bangon mahaifa na tsakiya).
3. Cutar sanyin gonoriya ko klamidiya
4. Matsewar bakin mahaifa
5. Ciwon dajin mahaifa
Yanda ake maganin ciwon mara a lokacin jinin haila
Da farko likita zai yi bincike mai zurfi akan marar lafiyar ya domin ya tabbatar da wani irin ciwon mara ne. Sannan zai aika marar lafiya É—akin awo ayi wasu gwaje-gwaje da zasu tabbatar da ce akwai ko babu wata cuta da ta haddasa wannan ciwon.
Gashi da gorar zuwan zafi: Gashi da gorar roba ta ruwan zafi hanya ce mai aiki sosai domin rage raÉ—aÉ—in ciwon dake zuwa tare da jinin haila. Ita wannan gorar roba ana chika ta ne da ruwa masu É—imi sai a aza ta akan mara na É—an wani lokaci.
Akwai gorar roba da ake sa ruwan zafi wadda bature ya ƙirƙira ta musamman domin wannan aiki, kamar yanda muka gani a wannan hoto dake sama👆. Amma idan mace ba ta da irinta takan iya samun galan ɗin da babu komai acikinsa ( empty gallon) ko gorar roba sai ta cika da ruwan zafi ta dunƙule shi da towel ko ragga sannan ta aza akan mara kamar yanda zamu gani akan wannan hoto da ke a ƙasa👇
Tausa da shafa marar da hannuwa (massage): Masana sun gano cewa tausa da shasshafa mara da hannuwa abinda bature ke kira da massage ita ma wata ingantattan hanyace da ke rage raÉ—aÉ—in ciwon mara.
Magungunan da ake amfani da: Ana amfani da magungunan kashe ciwo wajen kula da ciwon mara a lokacin jinin haila kashi na farko. Amma ciwon mara a lokacin haila kashi na biyu (wanda ke faruwa sanadiyar wasu cututtuka, kamar yadda muka yi bayani a sama) shi sai an fara maganin cutar da ta kawo ciwon sannan a haÉ—a da magungunan kashe ciwo. Magungunan da ake amfani dasu sun haÉ—a:
1. Ibuprofen
2. Diclofenac
3. Brustan N da dai sauran su
4. Paracetamol
5. Peroxicam
6. Acetylsalicylic acid+paracetamol
7. Indomethacin.
(A lura cewa yawan tu'ammali da WaÉ—annan magungunan na sama yana haifar da cutar gymbon ciki (ulcer) kamar yanda zamu iya gani acikin wannan rubutu "Abubuwan da ke kawo ulcer, alamomin ta da kuma ingantaccen maganin ta da zaisa ka warke". Saboda haka a kiyaye yanda ake shan su kuma a daina sha da zarar ciwon ya daina).
5. Mefenamic acid (Fenamex)
6. Combine oral contraceptives pills (COCp) idan ansha waÉ—an chan magungunan basuyi ba to likita zai iya baka waÉ—anda ake kira COCP. Su waÉ—annan magungunan na COCP asalin su magungunana ne tazarar iyali amma an gano suna maganin ciwon mara a lokacin jinin haila sosai.
Hanyoyin da mace zata kare kanta da ciwon mara a lokacin jinin haila/al'ada.
Babu takamammiyar hanyar da mace zata kare kanta daga ciwon mara kashi na farko amma takan kare kanta daga kashi na biyu ta hanyar magance cututtukan da ke da alaƙa da ciwon.
Duk da haka wasu masana sun ɗan zaƙulo wasu abubuwan da kan iya kare mace daga ciwon mara yayin da take al'ada. Abubuwan sune kamar haka:
1. Yawaita chin abinci mai gina jiki.
2. Yawan motsa jiki.
3. Daina shan giya da sigari
4. Rage chin abincin da ke dauke da sinadarin caffein.
Bayanin rufewa
A taƙaice munga cewa ciwon mara abu ne mai damuwar matasan mata sosai a cikin al'umma. Kuma Munga cewa masana sun kasa shi gida biyu, kashi na farko shi ne wanda ba a alaƙanta shi da wata cuta, kashi na biyu shi ne wasu cutuka ke haifar wa. Kana munga cewa ana amfani da magungunan kashe jiki da kuma maganin mefenamic acid da cocp wajen kawar da ciwon.
Idan mutum nada tambaya sai yayi ta a akwatin komment dake ƙasa, insha'Allah zamu karɓa masa.
Print this post
2 Comments
Mekesa jini ya dawo period after 10 days please
ReplyDeleteAkwai abubuwa dadama masu kawo rikicewar jinin period. Mun yi bayanin su dallah dallah da kuma yadda ake maganinsu a cikin wannan post din. https://www.lafiyata.com.ng/2023/01/rikicewar-alada-jinin-haila-da-kuma.html
Delete