Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Jin Zafi Yayin Fitsari da Kuma Ciwon Magudanan Fitsari - (Dysurea and Urinary Tract Infections)

Jin zafi yayin fitsari

Magudanar fitsari (Urinary Tract) wani bangare ne na jikin mutum da yake da alhakin tace dukkanin ruwan jiki da sinadaran dake cikin jini domin ware masu amfani da mayar da su a cikin jini da kuma fitar da marar amfani a matsayin fitsari. Magudanar fitsari ya ƙunshi sassan jiki kamar haka:

  1. Koda guda biyu (1 dama, 1 hagu) - Kidneys
  2. Bututun Koda guda biyu (1 Dama, 1 Hagu) - The 2 Ureters
  3. Mafitsara - Urinary bladder 
  4. Bututun fitsari - Urethra
Jin zafi yayin fitsari
Magudanar fitsarin maza

Koda ita ce jigon magudanar fitsari, saboda ita ce ke tace dukkanin jini da sinadaran shi sannan ta fitar da sinadarai da ruwa marar amfani a matsayin fitsari, fitsari yana fara fitowa daga koda zuwa bututun koda sannu-sannu, É—igo bayan É—igo, sannan ya wuce zuwa mafitsara, a inda zai taru na dan wani lokaci har sai mafitsara ta cika tumbul sai mutum ya fara jin fitsari daga nan sai yaje bandaki domin fitar da fitsarin da ya taru a cikin mafitsara.

A lokacin da mutum ya je ban daki da niyyar fitsari, fitsarin da ya taru a cikin mafitsara shi ne ke biyo ta bututun fitsari zuwa waje, har sai duk fitsarin da ya taru a mafitsara ya ƙare.

Jin zafi yayin fitsari
Magudanar fitsarin mata 

Jin zafi yayin fitsari yana faruwa ne a lokacin da ƙwayoyin cuta (mafi yawanci ƙwayoyin cutar bakteriya) suka kama daya ko dukkan wadannan sassan magudanar fitsari da muka ambata a sama. Idan hakan ya faru, a lokacin ake cewa mutum ya kamu da cutar magudanar fitsari, watau urinary tract infection, a likitance.

Mata su ne suka fi kamuwa da cututtukan magudanar fitsari, saboda bututun fitsarin mata baya da tsayi, É—an gajere ne kuma yafi na maza faÉ—i, saboda haka Æ™wayoyin cuta sukan iya shiga a cikin bututun su cimma mafitsara a cikin sauki. 

Haka kuma, bututun fitsarin mata ya bude ne kai tsaye a gaban su. Wanda kuma munsan cewa gaban mace wata gagarumar hedkwata ce ta ƙwayoyin cuta. Rashin kula da gaban mace yakan sa wadannan ƙwayoyin cuta yaɗuwa da haɓaka, hakan zai ba ƙwayoyin cuta damar yin hijira daga gaban mace zuwa cikin magudanan fitsarin ta, musamman macen da bata kula da gaban ta yadda ya kamata.

Alamomin da ke iya biyo jin zafi yayin fitsari - Sauran alamomin cututtukan magudanar fitsari 

A lura cewa, jin zafi yayin fitsari ba shi kadai ne alamar kamuwa da cutar magudanar fitsari ba, akwai wasu alamomi na musamman kamar haka:

  1. Zazzabi
  2. Yawan jin fitsari da rana, idan mutum ya je yin fitsarin sai yayi dan kadan.
  3. Yawan tashi fitsari da dare
  4. Ciwon mara
  5. Ganin farin ruwa bayan an gama fitsari ko yayin da akeyi
  6. Yin fitsari fari ko kalar madara
  7. Yin fitsari mai kauri, wata rana kamar kindirmo
  8. Ciwo a bayan ciki ko
  9. Tashin zuciya da amai
  10. Rashin jindadin jiki

Me ke kawo jin zafi yayin fitsari

Kamar yadda muka yi bayani a sama, abu na farko da ke kawo jin zafi yayin fitsari shi ne cututtukan magudanar fitsari (urinary tract infections), kuma fiye da kashi 90 cikin dari na jin zafi yayin fitsari suna da alaƙa da wadannan cututtukan.

Amma duk da haka masana sun ayyana wasu cututtuka da ke kawo jin zafi yayin fitsari kamar haka:

  1. Cutar sanyin mara
  2. Cututtuka masu yaduwa ta hanyar jima'i kamar cutar sanyin Gonorrhoea da Chlamydia
  3. Dutse a cikin magudanan fitsari, musamman dutse a bututun fitsari ko kuma mafitsara
  4. Rauni ga mafitsara ko bututun fitsari
  5. Cutukan gaban mace
  6. Cutar sankarar prostate ga maza
  7. Cutar BPH ga maza
  8. Cutar Endometriosis ga mata 

Yadda Ake Maganin Jin Zafi Yayin Fitsari 

Ana so mutum ya garzaya a asibiti domin ganin likita Æ™wararre a duk lokacin da ya fara jin zafi yayin fitsari. Wannan yana taimakawa wajen gano wace irin cuta ce  ta haddasa jin zafi yayin fitsari da kuma fara maganin ta nan take, wannan zai taimaka wajen hana illoli kamar irin su ciwon koda aukuwa.

A asibiti ana ba mutum shawarar yawan shan ruwa, yawan shan ruwa yana taimakawa wajen wanke duk wata kwayar cuta da ta shiga cikin magudanan fitsari.

Haka kuma ana ba mutum magungunan antibiotics domin kashe kwayoyin cuta.

Haka kuma ana ba da magungunan masu rage PH value na fitsari, yin haka yakan kara sanya fitsari ya zama sinadarin acid ta yanda kwayoyin cuta baza su iya wanzuwa a cikin magudanan fitsari ba.

Kammalawa

A cikin wannan rubutu mun tattauna jin zafi yayin fitsari da kuma cututtukan magudanar fitsari. Munga cewa mata su ne suka fi fama da jin zafi yayin fitsari, saboda sun fi maza haÉ—arin kamuwa da cututtukan magudanar fitsari. Haka kuma munga cewa ana iya magance jin zafi yayin fitsari cikin sauki ta hanyar amfani da magungunan asibiti.

Nassoshi 

1. Dysuria: What You Should Know About Burning or Stinging with Urination. Am Fam Physician. 2015 Nov 01;92(9):Online. [PubMed]

2. Michels TC, Sands JE. Dysuria: Evaluation and Differential Diagnosis in Adults. Am Fam Physician. 2015 Nov 01;92(9):778-86. [PubMed]

3. Geerlings SE. Clinical Presentations and Epidemiology of Urinary Tract Infections. Microbiol Spectr. 2016 Oct;4(5) [PubMed]

4. Stamm WE. Chlamydia trachomatis infections: progress and problems. J Infect Dis. 1999 Mar;179 Suppl 2:S380-3. [PubMed]

Print this post

Post a Comment

0 Comments