Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda ake maganin infections (Vaginal infections)

Gabatarwa:


Infection kalma ce ta turanci wadda ke bada ma'anar kamuwa da ko wace irin cuta, amma mafi yawancin mutane a al'ummar Hausa musamman mata idan suka yi amfani da kalmar infection sake ba kaidi suna nufin kamuwa da cututtuka masu sanya fitar wani ruwa ko majina daga al'aurar mace. Amma a tsarin likitanci waɗannan cututtuka ana yi musu laƙabi da 'vaginal infections' watau cututtuka masu shafuwar al'aurar mata ko kuma cututtukan farji. Waɗannan cututtukan na iya shafuwar farji kaɗai ko kuma farji da dukkan abubuwan da ke kewaye da shi (vulvovaginitis) sannan suna haifar da fitar ruwa ko majina daga al'aura, rashin jindaɗi, ƙaiƙayin gaba, warin gaba da dai sauransu.

Alamomin infections

Akwai alamomi da dama da mace ke iya ji a al'aurarta waɗanda ke nuni zuwa ga infections, duk da haka, waɗannan alamun basu keɓanta ga infections kaɗai ba. Alamomin sun ƙunshi:
 1. Fitar da wani mummunan ruwa ko majina daga farji (wannan shine babban alamar vaginal infections)
 2. Kumburin gaba
 3. Warin gaba
 4. Ƙaiƙayin gaba
 5. Zafi ko ciwon gaba
 6. Ciwon mara
 7. Jin zafi ko ciwo yayin fitsari
 8. Jin zafi ko ciwo yayin saduwa
 9. Zubar jini daga gaba
 10. Yawan zafin jiki
A lura cewa, akwai ruwa ko wani majina mai ɗan yauƙi dake fitowa a farjin mace wanda baya nuna rashin lafiyar komai. Ruwan bayada wani kala kuma bayada wari. Yana yawan fitowa a kwanakin da mace ta kusa yin ovulation ko a lokacin da sha'awarta ta motsa ko kuma haka kawai domin ya dawwamar da gaban mace a cikin ni'ima. Waɗannan ruwan ni'ima ne ba na infections ba, da turanci ana kiransu 'Physiological vaginal discharge' saboda ruwan baya tare da matsalar komai. Haka zalika, yawan zubar ruwan yakan ƙaru a lokacin da mace ta ɗauki ciki. Amma a yayin da mace ta kamu da infection ruwan ni'ima zai canza kala ya fara wari kuma adadin ruwan zai ƙaru.

Abubuwan da ke kawo infections (vaginal infections)

Ƙwayoyin cuta iri daban-daban su ke kawo cututtukan farji, kuma ƙwayoyin suna da yawa.  A haƙiƙa, Kwaleji na likitocin mata na Amurka ta ce kusan kashi ɗaya bisa uku na mata za su kamu da cutar farji a wani lokaci a rayuwarsu.
Waɗannan cututtukan na iya faruwa a kowane lokaci, amma sun fi yawa a cikin shekarun haihuwa (watau daga lokacin da mace ta balaga zuwa lokacin da zata daina al'ada).
A lura cewa, mace tana iya samun infection ba tare da ta taɓa yin jima'i ba, duk da cewa yin jima'i yana ƙarawa mace haɗarin samun infections kuma akwai cututtuka masu yaɗuwa ta hanyar jima'i da ke kawo zubar ruwa da majina daga farji. Saboda haka yana da kyau idan mace ta fara ganin wani abu na fita daga farjinta wanda bata saba gani ba ta gaggauta zuwa asibiti domin fayyace mata zare da abawa.
Ƙwayoyin cututtuka masu kawo infections sun ƙunshi 
 • Ƙwayoyin cututtukan fungi - Fungal infections
 • Ƙwayoyin cututtukan bacteria - Bacterial infections
 • Ƙwayoyin cututtukan parasite - Parasitic infections
Kamar yadda muka faɗi a baya akwai wasu cututtuka masu yaɗuwa ta hanyar jima'i masu kawo infection mai sanya zubar mummunan ruwa da majina daga farji, amma baza muyi bayanin su a wannan rubutun ba saboda bayanin su ya riga ya gabata. Domin karanta bayaninsu sai ku shiga wannan rubutun "Bayani game da cututtuka masu yaɗuwa ta hanyar jima'i da kuma yadda ake maganinsu".

1. Fungal (Yeast) infection

Wannan wani kalan infection ne dake shafar farjin mata wanda wata ƙwayar cutar fungi wadda ake kira da Candida albican take kawowa. Wannan fungal infection yana sanya mace fitar wani ruwa fari ƙal kamar madarar nonon shanu, mai kauri da ɗauri. Haka kuma mace zata iya jin ƙaiƙayi ko kumburin gaba.

2. Bacterial infection

Wannan shi ne infection ɗinda ke shafar farji wanda ƙwayoyin cutar bacteria ke kawo wa, a turanci ana kiransa 'bacterial vaginosis'. A lura cewa, shi farji, matattara ce ko kuma hedkwata ce ta dandazon ƙwayoyin bacteria. Har ko yaushe farji baya rabuwa da ƙwayoyin bacteria, saboda akwai ƙwayoyin bacteria da ake kira lactobacilli waɗanda a cikin farjin mace suke rayuwa kuma basu kawowa mata cutar komi, hasali ma, suna hana ƙwayoyin bacteria masu kawo cuta shiga cikin farji ta hanyar samar da wani sinadarin acid da ake kira lactic acid. Bacterial vaginosis yana faruwa ne a lokacin da waɗannan ƙwayoyin bacteria suka haɓaka har yawansu ya wuce yadda ake buƙata. Haka kuma bacterial vaginosis yana faruwa a lokacin da waɗannan ƙwayoyin bacteria da ke rayuwa a cikin farji suka yi ƙaranci, ƙarancin waɗannan ƙwayoyin bacteria zai sa baƙin ƙwayoyin bacteria masu kawo cuta su shiga cikin farji su kawo wa mace infections. Wannan shi yasa ya zama wajibi mace ta kula da tsaftace farjinta ta yadda waɗannan ƙwayoyin bacteria baza suyi yawan da zasu iya kawo mata infection ba kuma baza suyi ƙaranci ba. Haka kuma ba'a son mace ta dinga wanke cikin farjinta da sabulu mai ɗauke da sinadarin antibiotics, ko kuma kullum ta kama ƙwalƙwalar farji tana wankewa da ruwa, wai ita sarkin tsafta. Saboda yin haka zai kashe waɗannan ƙwayoyin bacteria masu rayuwa a farji yasa suyi ƙaranci ta yadda baƙin bacteria masu kawo cuta zasu iya shiga farjinta su kawo mata infections.
Alamomin bacterial vaginosis sun ƙunshi fitar da wasu ruwa ko majina launin toka, ko launin ruwan ƙwai, ko kore. Ruwan yana da ƙarni kamar warin kifi, haka kuma warin yana ƙaruwa sosai a yayin da ake jima'i da mace.


3. Parasitic infections

Wannan wani kalan infection ne da ƙwayar cutar parasite mai suna Trichomonas vaginalis take kawowa. Da turanci ana kiransa 'Trichomoniasis'. Alamomin cutar sun haɗa da fitar da wani ruwa mai warin kifi mai kumfa kuma kalan ɗanyen haki ko ruwan ƙwai ko tsaka-tsaki. Haka kuma, cutar tana iya sanya ƙaikayi da kumburin gaba, da jin zafi yayin da ake jima'i ko fitsari da kuma ciwon mara.


Yadda ake maganin infections (Vaginal infections)

Ya kamata mata su farga su daina cunkusa abubuwa marasa tushe a cikin farjinsu da sunan maganin infection. Nayi wannan magana ne, saboda mata sun karkata zuwa amfani da magungunan gargajiya irinsu tafarnuwa da dai sauransu a wajen maganin infections da kuma matsi. Toh 'yar uwa ki sani cewa waɗannan magungunan gargajiya dadama ba magani suke yi ba sai dai ma su kawowa mace wata matsala. Idan mace taga wasu alamomi na infections tare da ita abu na farko da ya kamata tayi shi ne ta garzaya asibiti domin gano wane irin infection take fama dashi. A chan asibiti za'a ɗebi samfurin ruwan da mace take fitarwa daga gabanta domin yin gwajin da zai nuna ƙwayoyin cutar da suka kawowa mace infection da kuma maganin da zai fi aiki akansu. Bayan haka za'a ɗora mace akan magunguna masu inganci da zasu magance mata infection cikin sauƙi.
 • Fungal (yeast) infections: Ana amfani da magungunan da ake kira 'antifungals'. Misalansu ya haɗa da: Fluconazole, Chlothrimazole, Flucytosine da dai sauransu. Haka kuma akwai man shafawa da kuma magungunan antifungals waɗanda ake sanyawa a cikin farji domin maganin wannan cutar. Misalansu ya haɗa da Chlothrimazole pessary, canestene da dai sauransu.
 • Bacterial vaginosis: Ana amfanin da magungunan antibiotics domin magance infections ɗin da ƙwayoyin cutar bacteria sunka kawo. Antibiotics da ake amfani dasu sun haɗa da: Metronidazole, Clindamycin, Ornilox, Ciprofloxacin, Metronidazole+Clothrimazole da dai sauransu.
 • Parasitic infections: Cutar Trichomoniasis wadda ƙwayoyin parasite ke kawowa ana amfani da magungunan kamar haka, Metronidazole, Tinidazole, Secnidazole, Ornilox, da dai sauransu.

Yadda mace zata kare kanta daga infections

 1. Tsafta
 2. Sanya wandon fatari (pant) na kaɗa wanda zai ba iska dama ya shiga cikin jikinki. Ba'a son sanya fatari mai kauri kuma mai matsewa saboda zai hana farji yin numfashi.
 3. Kar ki wanke cikin farji da ko wane irin sabulu. Cikin farji yana tsaftace kansa da kansa ba sai kinsa sabulu ba. Amma a gabanki kina iya sa sabulu kaɗan.
 4. A daina cunkusa komai aka samu a cikin farji da sunan maganin matsi ko ƙamshin gaba ko magance infections.
 5. Idan zaki wanke gabanki kiyi amfani da ruwan ɗimi kawai.
 6. Ki canja wandon fatari aƙalla sau ɗaya a yini.
 7. Kiyi aure ko kuma ki tsare yin jima'i da mutum ɗaya kacal.
 8. Idan kin shiga toilet kikayi fitsari da kashi a lokaci ɗaya, toh ko yaushe ki fara yin tsarki ki wanke gabanki kamin ki wanke baya.

Kammalawa

Infection ko kuma vaginal infections wasu cututtuka ne dake shafuwar al'aurar mata. Waɗannan cututtuka suna sanya zubar ruwa ko majina daga gaban mata, ƙaiƙayin gaba da kuma warin gaba. Maganin waɗannan cututtuka ya danganta da ƙwayoyin cutar da suka kawo shi. Ana amfani da magungunan antibiotics da antifungals domin magance waɗannan cututtuka.

Idan kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake ƙasa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 
Print this post

Post a Comment

0 Comments