Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Bayani game da ƙarancin halittun ruwan maniyyi da yadda ake maganin shi (Oligospermia)

Gabatarwa:

Mafi akasari ba za ku san cewa kuna da ƙarancin halittun da ke cikin ruwan maniyyi ba (wanda ake kira oligospermia) har sai kuna ƙoƙarin samun haihuwa kuma ba ku ci nasara ba.  Gwaje-gwaje na iya nuna cewa namiji yana da ƙasa da adadin halittun ruwan maniyyi da ake buƙata domin yiwa mace ciki. Wannan shi yasa wasu masana suka bada shawarar yin gwajin haihuwa domin ma'aurata su san matsayin su kamin kulla niyyar aure. Ƙarancin adadin halittun haihuwa da ke cikin ruwan maniyyi ana iya magance shi ta hanyar magance wasu abubuwan da ke kawo shi.

Mene ne ƙarancin adadin halittun maniyyi (Oligospermia)


Oligospermia kalma ce da ke nufin namiji yana da ƙarancin ƙidayar halittun samar da haihuwa da ke cikin ruwan maniyyi.  Ɗaya daga cikin fassarar likitanci shi ne cewa namiji yana da ƙasa da halittun haihuwa miliyan goma sha biyar (15 millions) a cikin millilita ɗaya na ruwan maniyyin da yake fitarwa yayin inzali (1ml of semen).  Saboda lafiyayyen adadin halittun haihuwa da ke cikin ruwan maniyyi ya fi miliyan goma sha biyar (15) a kowace millilita ɗaya (1) na ruwan maniyyi.

Yayin da ake kiran wannan matsalar da oligospermia, akwai kuma wata matsalar halittun ruwan maniyyi da ta fi tsanani wadda ake kira da oligozoospermia. Ita oligozoospermia ƙididdigar halittun haihuwa da ke cikin ruwan maniyyi yayi ƙasa da miliyan biyar (5) a cikin millilita ɗaya (1) na ruwan maniyyin. Haka zalika, akwai wata matsala da ta fi oligozoospermia tsanani, ana kiranta azoospermia. Ita azoospermia ba'a samun halittun haihuwa ko ƙwaya ɗaya a cikin ruwan maniyyi. Wanda keda matsalar azoospermia ko ya kawo ruwa yayin inzali, toh ruwan banza ne yake ɗurawa mace.Mene ne bambancin oligospermia da azoospermia

Oligospermia yana nufin akwai halittun haihuwa a cikin ruwan maniyyi amma adadin su yayi ƙasa da yadda ake buƙata domin yiwa mace ciki. Azoospermia kuwa yana nufin babu halittun haihuwa ko ƙwaya ɗaya a cikin ruwan maniyyi. Namiji mai fama da oligospermia yana iya dacewa da samun haihuwa watakila bayan ya sha wahala yana nema, watarana kuma yakan iya samu cikin sauƙi kamar sauran lafiyayyin maza, wani ma ba zai gane yana da wannan matsala ba har ya gama rayuwar sa. Amma wanda ke fama da matsalar azoospermia toh fah bashi ba haihuwa har abada. Haka zalika wanda ke fama da matsalar oligospermia ana iya yi masa wasu dabaru kamar irin su in-vitro fertilisation, intrauterine sperm insemination, domin ya samu haihuwa amma wanda ke da azoospermia fah ba wani hanya da za'a iya taimakon sa domin samun haihuwa. 
In vitro fertilization wata dabara ce da turawa suka ƙirƙira domin taimakawa ma'aurata masu neman haihuwa ruwa a jallo. A wannan dabarar ana karɓar ruwan maniyyin namiji da kuma ƙwan da mace ke samarwa duk wata sai aje cikin ɗakin lab a haɗa su ayi rainonsu tare. Bayan sun ƙyanƙyashe sun zama ciki sai a maida cikin a cikin mahaifar mace domin ya cigaba da girma.

Alamar ƙarancin halittun ruwan maniyyi

Babban alamar ƙarancin adadin halittun dake cikin ruwan maniyyi shine rashin iya yiwa mace ciki bayan aƙalla namiji ya shafe shekara ɗaya yana saduwa da mace akai-kai (jima'in da bai kasa aƙalla sau uku a cikin mako ɗaya ba) ba tare da amfani da hanyoyin hana ɗaukar ciki ko bada tazarar iyali ba. Wannan kasa yiwa mace ciki a cikin shekara ɗaya shi ne babban alama. 
A lura cewa, adadin ruwan maniyyin da ake samarwa yayin inzali yanada bambanci da adadin ƙwayoyin halittun haihuwa da ke cikin ruwan maniyyi. Matsakaicin adadin ruwan maniyyin da namiji ke fitarwa yayin inzali shi ne mililita uku (3) zuwa mililita biyar (5). Anason ko wane mililita ɗaya ya kasance yana ɗauke da aƙalla ƙwayoyin halittun haihuwa sama da miliyan goma sha biyar (15). 
Namiji mai ƙarancin halittun haihuwa da ke cikin ruwan maniyyi akan iya samun shi da isasshen ruwan maniyyi da yakai mililita biyar (5) ko ma fiye da haka, amma bashida isasshen ƙwayoyin halittun haihuwa a cikin ruwan maniyyin. Wani kuma yana da isasshen ruwan, amma ruwan banza yake ɗurawa mace saboda basu ɗauke da ƙwayoyin halittun haihuwa ko ƙwaya ɗaya. Haka kuma anasamun wani bayada isasshen ruwan maniyyi amma 'yan ruwan da yake da suna ɗauke da isassun ƙwayoyin halittun haihuwa, don haka zai iya yiwa mace ciki ba tare da wata matsala ba.

Abubuwan da ke kawo ƙarancin halittun haihuwa da ke cikin ruwan maniyyi

Akwai abubuwa da yawa da zasu iya sa namiji ya fuskanci ƙarancin halittun da ke cikin ruwan maniyyi ko wasu cututtuka na maniyyi.  Jerin dalilan sun hada da:

1. Cututtuka, ciki har da waɗanda ke da alaƙa da kwayoyin halitta, rashin daidaituwar sinadaran hormones da toshewar hanyar da halittun haihuwa ke fitowa daga ƴaƴan marina zuwa cikin azzakari (blockages).
2. Gurɓataccen muhalli.
3. Zafi.
4. Wasu magunguna.

1. Cututtuka

Akwai wasu cututtuka da dama masu kawo ƙarancin halittun haihuwa da ke cikin ruwan maniyyi, kaɗan daga cikinsu sun haɗa da:
 • Cututtuka masu alaƙa da ƙwayoyin halitta kamar irin su Klinefelter's syndrome da Cystic fibrosis.
 • Cututtuka masu yaɗuwa ta hanyar jima'i, cututtukan mafitsara da kuma wasu cututtuka da ƙwayoyin cutar virus ke kawowa kamar mump virus (mumps ƙwayar cutar virus ce mai kawo kumburin mummuƙe da ƴaƴan marina).
 • Cututtuka masu kawo ƙarancin sinadaran hormones na maza (hypogonadism)
 • Cututtuka masu kawo toshewar hanyar da halittun haihuwa ke fitowa daga ƴaƴan marina zuwa azzakari.

2. Gurɓataccen muhalli

Muhallin da mutum yake rayuwa a cikinsa yana ɗaya daga cikin abubuwan dake shafuwar lafiyarsa. Gurɓataccen muhalli irin wanda ke ɗauke da sinadaran heavy metals kamar su Arsenic, Cadmium, Lead da mercury yana iya haifar da ƙarancin halittun ruwan maniyyi ga mutanen da ke rayuwa a cikinsa.

3. Zafi

Zafi yana da illah sosai ga rayuwar tantanin halittun haihuwa da ke cikin ruwan maniyyi haka kuma yana hana samar dasu a cikin ƴaƴan marina. Zafin da ke iya shafar halittun haihuwa ya haɗa da;
 • Zafin ciki, idan har an samu rashin saukowar ɗaya daga cikin ƴaƴan marina daga cikin ciki zuwa jikkar scrotum (fatar tsuwayyu).
 • Cutar varicocoel
 • Daɗewa cikin ruwan zafi yayin gashin ɗankanoma.

4. Magunguna

Akwai nau'ikan magunguna da yawa waɗanda zasu iya kawo ƙarancin adadin halittun dake cikin ruwan maniyyi.  Wasu daga cikin waɗannan magunguna sun haɗa da:
 • Testosterone.
 • Methadone.
 • Nitrofurantoin.
 • Lamotrigine.
 • Clomipramine.
 • Paroxetine.
 • Prednisone.
 • Methotrexate.
 • Finasteride.
 • Sirolimus

Yadda ake gane mai ƙarancin halittun ruwan maniyyi a asibiti

Idan namiji yazo da matsalar rashin haihuwa a asibiti, likita zai ɗauki bayani da kuma cikakken tarihin lafiyar shi da kuma bayanin yadda yake gudanar da mu'amalarsa ta aure. Bayan haka za'a duba shi akan gadon asibiti sannan ayi odar wasu gwaje-gwaje kamar haka:
 • Seminal fluid analysis: Wannan shi ne babban gwajin da ake buƙata, domin shi ne zai nuna lafiya da kuma adadin halittun da ke cikin ruwan maniyyi.
Sauran gwaje-gwajen da likita zai yi sun danganta da abubuwan da likita ke tunanin sun kawo matsalar. Kaɗan daga ciki sun haɗa da:
 • Hormonal assay
 • Urinalysis
 • Trans-scrotal Uss
 • Genetic tests
 • Da dai sauransu

Yadda ake maganin karancin halittun ruwan maniyyi

Yadda ake magance wannan matsala ta ƙarancin halittun haihuwa da ke cikin ruwan maniyyi ya danganta da abinda ya kawo matsalar. Ana iya shawo kan wannan matsala da kuma ƙara adadin halittun ruwan maniyyi ta hanyar dakatar da magunguna ko halayen da ke ba da gudummawa ga aukuwar wannan matsala.
Wasu abubuwan da ke kawo wannan matsala na iya buƙatar wata jiyya ko kuma kulawa ta musamman.  Misali:

 • Ana iya buƙatar tiyata don magance varicocele ko toshewar hanyoyin halittun maniyyi daga ƴaƴan marina zuwa azzakari.
 • Likita ko mai kula da kiwon lafiya na iya bada abubuwan da zasu ƙara wa mutum sinadaran hormones na maza.
 • Likita ko mai kula da kiwon lafiya na iya rubuta magungunan antibiotics don cututtuka.
 • Likita na iya ba da shawara don magance al'amura kamar tabarbarewar mazakuta ko fitar maniyyi da wuri ko saurin inzali.

A wasu lokutan ba za ku iya ƙara yawan adadin halittun da ke cikin ruwan maniyi ba. Amma idan kuna neman haihuwa ruwa a jallo, likitanku na iya ba da shawarar wasu hanyoyi don taimakawa wajen samun haihuwa kamar irinsu:
 • In-vitro fertilisation and embryo transfer
 • Intrauterine sperm insemination
 • Gamete intrafallopian transfer
 • Zygote intrafallopian transfer

Yadda namiji zai kare kansa daga karancin halittun ruwan maniyyi

Domin kare namiji daga ƙarancin ƙididdiga na halittun ruwan maniyyi, akwai wasu abubuwa da ma'aikacin lafiya ko likita zai iya ba da shawarar ayi.  Waɗannan na iya haɗawa da canje-canje ko kuma sauyin yadda ake gudanar da rayuwa, kamar:
 • Kula da nauyin da ke da lafiya a gare ku ta hanyar motsa jiki da cin abinci mai kyau.
 • Dakatar da shan taba da amfani da kayayyakin taba.
 • Rage shan abubuwan sha masu ɗauke da barasa.
 • Dakatar da amfani da marijuana (ganyen wiwi) da/ko wasu abubuwa masu ɗauke da shi.
Wataƙila kun ji labarin bitamin ko ma'adinai ko kayan abinci na ganye waɗanda zasu iya taimakawa wajen kara muku ruwan maniyyi.  Tuntuɓi likita ko mai kula da lafiyar ku kafin gwada kowane ɗaya daga waɗannan abubuwan.

Kammalawa

Ƙarancin halittun da ke cikin ruwan maniyyi yana ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke hanawa maza samun haihuwa. Sauran abubuwan munyi bayanin su a cikin wani rubutu da ya gabata, "Bayani game da abubuwan da ke kawo rashin haihuwa ga maza da kuma yadda ake maganin su". Yana da kyau duk namiji ya sansu domin kiyayewa, haka ma mace domin taimakawa mijinta.

Idan kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake ƙasa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 
Print this post

Post a Comment

0 Comments