Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Abubuwan 18 da ke kawo rashin haihuwa ga maza: 18 Common causes of male infertility in Nigeria

 Gabatarwa:

Masana sun Æ™iyasta cewa rashin haihuwa yana damuwar kashi goma cikin É—ari na ma'auratan duniya. A wani bincike na daban kuma an tabbatar da cewa a duk cikin ma'aurata bakwai (7) to za'a samu kashi É—aya (1) na fama da matsalar rashin haihuwa[¹]. 

Mutane a wannan zamani sunfi yawan danganta matsalar rashin haihuwa ga mata kawai, ba tare da la'akari da cewa maza suna da tasu gudunmawa ba. 

Masana sun Æ™iyasta cewa kashi talatin cikin É—ari (30%) na matsalar rashin haihuwa tana faruwa ne saboda matsalar namiji, kashi 30 cikin É—ari tana faruwa ne saboda matsalar mace,  kashi talatin cikin É—ari (30%) kuma saboda matsalar mata da miji baki É—aya, kashi biyar zuwa goma kuma ba'a san takamaiman abinda ke kawo matsalar ba[¹].




Mene ne ake kira da rashin haihuwa?

Ƙwararrin likitoci a fannin kula da mata masu juna biyu da kuma al'aurar mata sun fassara ma'anar rashin haihuwa da rashin samun juna biyu bayan ma'aurata mace da namiji baligai sun shafe tsawon shekara É—aya suna yin isasshen jima'i ta farjin su ba tare da roba ko wata kariya ba. Isashen jima'i a cikin wannan ma'anar yana nufin jima'in da bai kasa aÆ™alla sau uku a sati ba[¹].

Alamomin rashin haihuwa ga maza

Babbar alamar rashin haihuwa ga maza ita ce namiji ya kasa yiwa mace ciki bayan shafe aÆ™alla shekara É—aya yana isashen jima'i da ita. Amma a wasu lokuta akwai wasu alamomi da ke iya bayyana ga namiji waÉ—anda suna da alaÆ™a ne da cutar da ta haddasa masa rashin haihuwa. WaÉ—annan alamomin sun haÉ—a da[¹]:

  1. Matsaloli a wajen jima'i: Waɗannan sun haɗa da rashin fitar da isasshen ruwan maniyyi ko kuma samun wahala wajen fitar da shi, ƙarancin sha'awar mace ko kuma rashin samun ƙwaƙƙwaran miƙewar azzakari.
  2. Jin ciwo ko kumburi a cikin 'ya'yan marina
  3. Rashin jin ƙamshin komai a hanci
  4. Fitowar nono a ƙirjin namiji
  5. Rashin fitowar gashi a fuska da kuma sauran sassan jiki.
  6. Namiji mai muryar mata
  7. Fitar da ƙasa da isasshen ruwan maniyyi (Isasshen maniyyi shi ne wanda ke ɗauke da tantanin halittun haihuwa da basu kasa miliyan goma sha biyar ba (15 million) a duk cikin mil ɗaya na ruwan maniyyin ko kuma miliyan talatin da tara (39 million) a duk ruwan maniyyin da aka kawo cikin inzali ɗaya).
  8. A lura cewa, za'a iya samun mutum da wasu daga cikin alamomin da muka ambata a sama kuma yana haihuwa[¹][²].

Yaushe namiji ya kamata ya ga likita idan yana fuskantar matsalolin rashin haihuwa?

1. Daga zarar mutum ya fara fuskantar ɗaya daga cikin matsalolin da muka ambata a baya toh ya kamata ya hanzarta ya ga likita ƙwararre a fannin kula da lafiyar al'aurar maza (urologist).
2. Idan namiji da matar sa sunyi shekara É—aya (1) suna neman haihuwa basu samu ba
3. Namiji da aka taɓa yiwa aikin tiyata a al'aurar sa, kamar aikin gwaiwa (herniorrhaphy or hydrocoelectomy)

Abubuwan da ke kawo rashin haihuwa ga maza

Abubuwan da ke kawo rashin haihuwa ga maza kamar yadda bincike ya tabbatar sun kunshi wadannan [¹][²]:

1. Cutar varicocele

Wannan cuta tana  sanya jijiyoyi masu É—aukar jini daga Æ´aÆ´an marina su kumbura. Cutar varicocele ita ce cutar da tafi kawo wa maza rashin lafiya cikin cututtukan da ake iya magani. Tana kawo raguwar adadin tantanin halittun haihuwa da ake samu a cikin ruwan maniyyi.

2. Cututtukan 'ya'yan marina

Wasu cututtuka dake damuwar ƴaƴan marina suna hana haihuwa ta hanyar hana girman tantanin halittun haihuwa ko kuma haddasa wani tabo da zai toshe musu hanya zuwa cikin azzakari. Cututtukan sun haɗa da cutar epididymitis, orchitis, sanyin gonoriya da kuma cutar ƙanjamau (HIV).

3. Fitar ruwan maniyyi koma-baya (retrograde ejaculation)

Wannan shi ne bature yake kira retrograde ejaculation. Yana faruwa ne lokacin da maniyyi yakan É“ace hanyar sa ya koma cikin mafitsara a cikin mara maimakon ya shiga cikin azzakari.

Mai irin wannan matsalar baya fitar da ruwan komai a lokacin inzali, ko ya fitar ba zai kai adadin da ake buÆ™ata ba saboda maniyyin yan komawa cikin mafitsarar shi. Sai idan yazo fitsari sai maniyyin ya fito ta cikin fitsari. 

Akwai abubuwa dake haddasa wannan cutar, kamar yin aikin tiyata a azzakari da kuma wasu magunguna.

4. Sperm auto-antibodies

Musabbabin wannan cutar shi ne, garkuwan jikin mutum ta kan kasa gane tantanin halittun haihuwa da ke cikin ruwa maniyyin mutum sai ta ayyana su a matsayin baƙi ko kuma maƙiya sannan ta tura sojojin garkuwar jiki domin su kashe tantanin halittun haihuwa dake cikin ya'yan marinan shi.

Mai irin wannan cutar zai fitar da ruwa a lokacin inzali, amma ruwan baza su iya komai ba saboda tantanin halittun haihuwa da ke cikin duk sun mutu.

5. Ciwon daji ko sanƙara

Ciwon daji ko kuma sanƙara ya kan hana namiji haihuwa ne ta hanyar shafar wasu gland dake ƙirƙirar sinadarai kamar gland ɗin pituitary dake ƙirƙirar sinadaran LH da FSH. Waɗannan sindaran suna da matuƙar muhimmanci a reno da kuma samar da tantanin halittun haihuwa.

6. Rashin daidaituwar sinadarai a jiki

Kamar yadda muka yi bayani sinadaran hormones kamar su LH da FSH da testestrone suna da matuƙar amfani a wajen haihuwa, saboda haka ƙarancin su, ko yawan su a jiki yana haddasa matsalar rashin haihuwa. Akwai abubuwa da yawa dake kawo rashin daidaituwar sinadarai a jiki, zamu yi bayani akan su a cikin wani rubutu.

7. Toshewar mafitar tantanin halittu

Tantanin halittun haihuwa suna girma ne a cikin tsakiyar Æ´aÆ´an marina sannan a É—auko su zuwa cikin wani kwararo da ake kira epididymiys inda zasu ci gaba da zama a ciki har sai lokacin da mutum yazo inzali yayin da yake jima'i sannan su fito zuwa cikin azzakari. 

Akwai wasu ƙananan hanyoyi ko kuma bututu da ke ɗauko tantanin halittun haihuwar daga tsakiyar 'yan'yan marinar zuwa epididymiys, toshewar waɗannan hanyoyi kan sa rashin haihuwa. Cutar orchitis itace ake yawan ɗorawa alhakin toshewar waɗannan ƙananan hanyoyi.

8. Matsaloli wurin jima'i

Wannan ya ƙunshi rashin samun ƙwaƙƙwaran miƙewar azzakari, saurin fitar da ruwan maniyyi da kuma jin ciwo yayin da mutum ke jima'i.

9. Cutar hypospadia da epispadia

Hypospadia cuta ce da ake haihuwar namiji da ita, ana gane ta ne hanyar buɗewar ƙofar azzakari ta ƙasan azzakari maimakon ta tsinin kansa. Ita kuma epispadia ƙofar azzakarin takan buɗe ne a saman azzakari maimakon a tsinin sa. Masu irin waɗannan cututtukan suna samun matsalar zuba ruwan maniyyin su a inda ya kamata su zuba a cikin jikin mace.

10. Mu'amala da wasu sinadarai (chemicals)

Idan mutum na mu'amala da wasu sinadarai ko chemicals masu ɗauke da guba a cikin su kamar magungunan feshin haki, magungunan feshin ƙwari, wasu daga cikin takin zamani da kayan fenti. Suna iya kawo masa matsalar haihuwa.

11. Hasken bature

Hasken X - Ray da sauran haske (radiations) É—in da bature ke samar wa.

WaÉ—annan suna da illa sosai ga ya'yan marina domin suna kashe tantanin halittun haihuwa.

12. Yawan barin 'ya'yn marina cikn zafi

Wannan shima babban abu ne dake ha shima yana haddasa rashin haihuwa saboda zafin yana hana tantanin halittun haihuwa girma wannan shi yasa yana da kyau namiji ya É—age ya'yan marinar sa da hannu kar ya bari su shiga ruwan zafi a lokacin da yake gashin basir, zaka iya karanta bayani mai faÉ—i game da yanda ake gashin basir a wannan rubutun "Alamomin da kuma yanda ake maganin dan kanoma/basir mai tsiro"

Haka suma masu amfani da komfutar laptop akan cinyarsu suna fallasa ya'yan marinar su ga zafi, wanda yin haka na tsawon lokaci yana iya haifar da matsalar rashin haihuwa ga namiji.

13. Matse ya'yan marina

Yawan sanya wando ko pant dake matse ƴaƴan marina sosai da kuma. Wannan shi yasa aka fi son namiji ya rika amfani da ƙaramin wando underwear da ke da walwala, kuma na auduga da zai bari isasshen iska ya shiga a cikin sa. Amma abin takaici sai ka ga wasu maza na amfani da wandon fatari (pant) saboda lalaci.

14. Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi

15. Yawan shan giya/barasa

16. Yawan shan sigari

17. Yawan ƙiba (taiɓa) sosai.

18. Jin rauni a mara ko a ya'yan marina.


Bayanin rufewa

Rashin haihuwa matsala ce babba dake damuwar ma'aurata, kuma a wani sa'ilin takan haifar da mutuwar aure ko kuma husuma tsakanin ma'aurata. 

Ba mata kaÉ—ai ne ke fama da matsalar rashin haihuwa ba suma maza suna fama da tasu matsalar dai dai da ta mata kamar yadda bincike ya tabbatar.

Mai tambaya ya ajiye a cikin akwatin sharhi (comment box) dake Æ™asa, insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 

Nassoshi


Print this post

Post a Comment

0 Comments