Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Hanyoyin da ake kula da lafiyar ido domin kaucewa matsalar rashin gani

 Gabatarwa:

Idanu sassan jiki ne na musamman masu aika saÆ™on gani zuwa ga Æ™waÆ™walwa, ba shakka idanu suna cikin  sassan jiki masu matuÆ™ar amfani a jikin mutum, saboda haka kula da lafiyar idanu ya zama wajibi ga duk wani É—an adam mai hankali. Duba da irin muhimmancin idanu shafin lafiyata ya kawo muku bayani sha-kundum yadda zaku kula da tattalin arzikin lafiyar idanuwan ku[¹].


1. Chin abinci mai kyau

Chin abinci  mai lafiya shi ne  hanya ta farko da mutum zai bi domin kula da lafiyar idanunsa da ma lafiyar jikin sa baki É—aya kamar yadda wata Æ™wararra a fannin kula da lafiyar idanu Dr. Rebeca Taylor wadda ke makarantar koyar da gyaran idanu ta Amurka tayi tsokaci. Anason mutum ya faye chin kayan lambu kamar irin su alayyahu, salad, da sauran nau'o'in ganye.
Idan ana maganar abinci mai gyara ido ana bada daraja ta musamman ga nau'o'in abinci da ke É—auke da sinadarin vitamin - A. Kamar irin su karras (Carrot), anta (Liver), man anta(Liver oil), dankali(Sweet potato),  alayyafo (Spinach), jan yaji (Red pepper) da dai sauransu. Wannan vitamin A shi ne sindarin da yake taimakawa idanu domin yin aikin su yanda ya kamata[²][³].

2. Duba lafiyar ido a asibiti akai-akai

Wannan yana da matukar amfani ko da mutum bai taɓa samun matsalar ido ba idan ya kai waɗansu shekaru yana da kyau ya riƙa ganin likitoci masana fannin ido akai-akai domin su duba lafiyar idanunsa. Yin haka yana taimakawa wajen gane wasu matsaloli tun suna ƙanana sai ayi maganinsu kamin su girma suyi wa idanu karan tsaye.
Makarantar kimiyya ta koyon ilimin kula da lafiyar idanu dake Amurka (American Academy of Opthalmologist, AAO) ta bayar da shawarar yadda wanda yake lafiya Æ™alau zai ga likitan idanu akai-akai domin duba lafiyar idanunsa, kamar haka[²].
  • Da zarar mutum yakai shekara arba'in (40 years) zai je ayi masa dubawa ta farko.
  • Dan shekara arba'in zuwa hamsin da biyar (40-55 years) zai je a duba shi duk bayan shekara biyu zuwa huÉ—u (2-4 years).
  • Dan shekara hamsin da biyar zuwa sittin da huÉ—u (55-64 years) zai je a duba shi duk bayan shekara É—aya zuwa uku (1-3 years).
  • Dan shekara 65 zuwa sama zai je a duba shi duk bayan shekara É—aya (1).


3. Daina shan sigari ko kar a fara sha

Shan sigari yana da illa sosai ga idanun mutum saboda tana ɗauke da sinadarin cyanide, shi wannan sinadarin yakan fito ne daga hayaƙin sigari ya shiga idanu ya lalata wasu tantanin halittun idanu. Haka zalika, shan sigari yana haifar da bushewar idanuwa kuma yana kawo cutar cataract da kuma cutar macular degeneration.

4. Kare idanuwa daga hasken rana

Ana son mutum ya kare idanuwan sa daga hasken rana ta hanyar amfani da tabarau mai kare hasken rana. Tabarau mai kare hasken rana (Sunglasses) yana kare idanu daga hasken rana ta hanyar toshe mafi yawancin hasken shiga idanu kai tsaye. Fatar idanu ba fata ce mai wani kauri ba shi yasa hasken idan yayi yawa yakan iya shiga idanu har yayi musu illah[²]

5. Bada isashen hutu ga idanu.

Yawan aiki da na'ura mai ƙwaƙwalwa ko wayar salula na tsawon lokaci yana kawo bushewar idanuwa, wannan yana faruwa ne sanadiyyar rashin samun ƙyaftawar ido isasshe lokacin da mutum ya tsura idanunsa a gilashi mai bada bayani da kuma hasken da yake fitowa daga gilashin ya shiga cikin idanu kai tsaye. Ana son mutum ya bada isasshen hutu ga idanunsa kuma yayi amfani da tabarau domin kariya daga hasken.
Domin kaucewa bushewar idanu yayin aiki da duk wata na'ura mai bada bayani ta gilashi masana sun Æ™irÆ™iro da wata doka wadda ake yima laÆ™abi da 20. 20. 20. Wannan dokar ta buÆ™aci a duk lokacin da ka tsurawa wani abu idanu na tsawon minti ashirin (20) to ka kauda idon ka zuwa ga wani abu mai nisan aÆ™alla sawu ashirin (20) dagareka, ka kalle shi na tsawon daÆ™iÆ™a ashirin (20)[³].

6. Kula da sinadarin sugar dake cikin jini

Ciwon suga yana cikin cututtukan da suka fi kawo matsalar rashin gani a duniya. Abin la'akari anan shi ne matsalar rashin gani da ciwon suga ke kawo wa mutane ana iya kare ta ta hanyar kula da sinadarin suga da ke cikin jinin mutum, amma sai sakaci yasa mutane su bari har suga yayi musu É“arna a idanu.

7. Kasan lafiyar idanun zuriyar ka

Sanin lafiyar idanun zuriyar mutum yana da amfani sosai. Saboda yana da kyau mutum yasan in akwai mai wata cutar ido a zuriyar sa. Wannan shi zai nuna maka cewa kaima kana iya kamuwa da wannan cutar saboda akwai cututtukan idanu da ake gado da dama[¹][³].

8. Kula da sanya kayan kariyar idanu a lokacin wasa ko motsa jiki

Kula da sanya kayan tsaron idanu (kamar su goggles, sheild and guards) a lokacin motsa jiki ko yin wani abu mai haɗari yakan kare idanuwa daga jin mummunar rauni ko kuma faɗawar wani abu baƙo.


9. Taka tsantsan da taɓa idanu da hannu.

Ana son mutum ya zama ko yaushe hannuwan shi nada tsafta kamin ya taÉ“a idanun sa in ta kama. Ba'a son mutum ya zamo mai yawan taÉ“a idanuwan sa da hannu saboda hakan zai iya É—aukar wata cuta daga hannunsa zuwa idanuwan sa[³].

10. Kula da matsin lambar jini (blood pressure)

Hawan jini yana É—ai daga cikin abubuwan da ke kawo matsalar rashin gani a duniya. Kula da hawan jini ta hanyar shan magunguna da kuma yin abubuwan da ya dace yana kare idanu daga illar hawan jini.

Bayanin rufewa

Idanuwa sassan jiki ne masu muhimmanci waɗan da ke da alhakin ɗaukar saƙon gani suna turawa ƙwaƙwalwa, saboda haka kula dasu ya wajaba domin a kare matsalar rashin gani. Haka zalika, munga hanyoyi daban-daban har guda goma da zamu iya bi domin kare tattalin arzikin lafiyar idanuwan mu.
Mai tambaya sai ya rubuta tambayarsa a cikin akwatin tofa albarkacin baki da ke ƙasa.

Idan kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake Æ™asa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 


Nassoshi

1. Angela R. Elam, Victoria L. Tseng, Tannia M. Rodriguez, Elise V. Mike, Alexis K. Warren, Anne L. Coleman, Ugochi Aguwa, Chrisfouad Alabiad, Cesar Briceno, Hilda Capo, Melissa Contreras, Jane Edmond, Ann-Margret Ervin, Tamara Fountain, David Friedman, James Gao, Lynn Gordon, Joy Harewood, Ken Kitayama, O̢۪Rese Knight, Aaron Lee, Paul Lee, Gary Legault, Kristen Nwanyanwu, Mildred Olivier, Cesar Perez-Gonzalez, Jessica Randolph, Ahmara Ross, Ruth Shoge, Sharon Solomon, Basil Williams, Fasika Woreta, Charles Wright, Nazlee Zebardast,
Disparities in Vision Health and Eye Care,
Ophthalmology,
Volume 129, Issue 10,
2022,
Pages e89-e113,
ISSN 0161-6420,
(https://www.sciencedirect.com/science/article/pii/S0161642022005280)


Print this post

Post a Comment

0 Comments