Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Alamomi, abubuwan dake haddasawa da kuma maganin saurin inzali (Premature ejaculation)

Gabatarwa:

Masana sun ƙiyasta cewa kashi talatin zuwa kashi arba'in (30%-40%) na mazaje sun taɓa samun matsalar saurin inzali. Wannan yana nuna cewa a duk cikin namiji uku za'a sami aƙalla mutum ɗaya da ya taɓa samun wannan matsalar ta saurin inzali(1). 

Saurin inzali yana da illah sosai musamman ga ma'aurata, saboda daga zarar namiji yayi inzali toh sha'awar sa zata karye. A lokacin da namiji yake yin inzali, toh a lokacin yake samun ƙololuwar jindaɗin jima'i wanda bayan haka sha'awar sa zata kwanta gaba ɗaya.(1)  Saurin inzali matsala ce babba saboda yakan kawo matsalar rashin jituwa a tsakanin ma'aurata lokacin jima'i, saboda inzalin yakan faru ne kamin mace ta gama gamsuwa yayin da sha'awar ta ke matashiya, shi kuma namiji daga yayi inzalin, azzakarin sa zai kwanta kuma ya daina jin sha'awar jima'i kwata-kwata(2).Me ake nufi da saurin inzali?

Inzali yana nufin fitar da ruwan maniyyi daga cikin jikin mutum zuwa waje ta hanyar al'aura a yayin da yake cikin ƙololuwar jindaɗin jima'i.
Duk da cewa fassarar mene ne saurin inzali ya danganta da ƙungiyoyin masana, amma ƙungiyar ƙwararrin likitoci masana al'aurar maza ta Amurka ta fassara saurin inzali da fitar da ruwan maniyyi daga zarar an fara jima'i ko kamin a fara ko kuma yayin da akeyi kamin a buƙaci fitar ruwan, idan haka ya zama sanadiyyar ƙunci ga mai yin jima'i ko abokiyar saduwar shi(2).

Alamomin saurin inzali

Lokacin fitar da ruwan maniyyi a yayin jima'i ya danganta daga wani namiji zuwa wani namiji, wannan shi yasa ƙayyade lokacin saurin inzali yana da matukar wahala sosai. Amma duk da haka masana sunyi ittifaƙi akan cewa waɗannan guda huɗu alamomi ne na saurin inzali(2).
 1. Mutum yana fitar da ruwan maniyyi kamin ya sanya azzakarin sa a cikin farjin abokiyar saduwar shi.
 2. Koyaushe mutum yana fitar da ruwan maniyyi cikin minti ɗaya zuwa uku (1-3 minutes) bayan sanya azzakarin sa a cikin farjin abokiyar saduwar shi.
 3. Mutum ya zama baya iya sarrafa kansa a lokacin da yake ƙoƙarin fitar da ruwan maniyyi.
 4. Ɗaya daga cikin ma'aurata ya shiga ƙunci ko ya daina son jima'i sakamakon saurin fitar da ruwan maniyyi.
Yana da kyau a lura cewa duk da babu takamaiman lokacin da ake buƙatar namiji yayi inzali bayan fara yin jima'i amma masana sun ƙayyade matsakaicin lokacin da maza ke yin inzali a matsayin minti biyar (5 minutes) bayan shigar azzakari a cikin farji. Don haka ana ganin cewa lafiyayyen mutum duk zai iya yin jima'in aƙalla minti uku bayan saka azzakarin sa acikin farjin mace(3).

Abubuwan da ke kawo saurin inzali

Kamin muyi bayani akan abubuwan da ke kawo saurin inzali yana da kyau muyi tsokaci game da yanda ɗa namiji ke yin inzali a lokacin da sha'awar sa takai ƙololuwa yayin da yake yin jima'i. Amma wannan bayani ya riga ya gabata a cikin wannan rubutun "Bayani akan ilimin kimiyyar jima'in ɗan adam" anyi bayani dalla-dalla game da yanda namiji ke yin inzali.
Duk da cewa ba'a san takamaiman abinda ke kawo wa wasu maza saurin inzali ba, amma ana ɗora alhakin saurin yin inzali ga waɗannan abubuwa(3):

1. Rashin isasshen sinadarin serotonin a jikin mutum.
2. Ƙunci ko damuwa
3. Gajiya
4. Rashin yadda da kai wurin jima'i
5. Fara harkokin jima'i tun kamin namiji ya balaga
6. Rashin ƙarfin mazakuta
7. Rashin dai-daituwar wasu sinadarai a jikin mutum.
8. Sabawa da yin istimna'i (masturbation).
9. Masu ƙaramin jiki sunfi fama da wannan matsala.
10. Cututtukan dake damuwar al'aurar maza.

Yadda ake maganin saurin inzali a asibiti

Da farko dai likita zai tattauna da marar lafiya akan sha'anin rayuwar sa ta jima'i da kuma ɗaukacin lafiyar sa. Likita yakan iya duba mutum akan gado. Ya kan iya aika marar lafiya a ɗakin gwaji musamman idan saurin inzalin ya haɗu da rashin samun ƙaƙƙarfan miƙewar azzakari.
Akwai hanyoyi da dama da ake bi domin maganin saurin inzali, zamuyi bayanin su dalla-dalla a ƙasa(4).

1. Pelvic floor muscles exercise / Kegel's exercise (Motsar da tsokokin kwankwaso)
Wannan wata hanya ce da ake bi domin koyar da tsokokin kwankwaso yadda zasu iya riƙe inzali idan mutum yaji uzurin inzali kamar yadda ake iya riƙe fitsari zuwa wani ɗan lokaci. Yadda mutum zai yi wannan aikin shi ne zai yi kaman zai riƙe fitsari ko kuma zai riƙe tusa duk da ba komai yake ji ba. Anason mutum ya takura kansa kamar zai riƙe fitsari ko tusa zuwa na wani ɗan lokaci da bai kasa daƙiƙa uku ba sannan ya saki. Sai ya ƙara maimaita haka kamar sau goma, to shikenan ya gama. A rana anason mutum ya maimaita irin haka kamar sau uku. 
Wannan dabara ce da zata ƙarawa tsokokin kwankwaso ƙarfi domin su iya riƙe inzali a lokacin da yazo wa mutum ba tare da shiri ba.

2. Maida hankali akan wani abu a yayin da ake yin jima'i.
Idan mutum yana fuskantar saurin inzali anaso ya ɗauke hankalinsa da tunaninsa akan harkokin jima'i baki ɗaya a yayin da ya sanya azzakarin sa a cikin farjin mace. Daga nan sai ya fara tunanin harkokinsa na yau da kullum, kamar wurin aikinsa ko masana'antar sa ko wani abu na daban. Wannan yakan ƙara masa lokaci sosai kamin yaji uzurin inzali yazo masa(4).

3. Pause and squeeze method (Dabarar a tsaya a matse)
Wannan wata dabara ce da ake yi domin dakatar da inzali a lokacin jima'i. Yadda ake yi shi ne mutum zai fara yin jima'i kamar yadda ya saba, amma daga zarar yaji uzurin inzali sai ya dakata sannan ya ɗora hannun sa dai-dai layin da ya raba kan azzakarin sa da gangar jikin azzakarin sai ya matse sosai, sannan kuma yakan iya matsewa tun daga tushen azzakari, haka zalika, yakan iya kama matsowa daga kan azzakarin zuwa tushen sa kamar yadda zamu iya gani a hotunan da ke ƙasa (abokiyar saduwar mutum zata iya yi masa). Yin haka zai dakatar da uzurin inzali. Toh bayan mutum ya daina jin inzalin sai ya cigaba da jima'i abinsa har sai ya sake jin wani uzurin inzali yazo masa sannan in yana so sai ya ƙara maimaita wa. Ana iya maimata hakan har sai mutum yaji ya gamsu. 

4. Pause and start method (Dabarar a tsaya a huta)
Wannan ma wata dabara ce ta tsaida yin inzali, ita wannan dabarar idan mutum na cikin yin jima'i daga yaji uzurin inzali yazo masa sai yayi sauri ya fitar da azzakarin sa ya tsaya ya huta har sai yaji ya daina jin uzurin inzali sannan sai ya koma yaci gaba. Haka mutum zai chi gaba da yi har sai yaji ya gamsu sannan sai yayi inzali.
Ita wannan dabarar bata kai ta saman ta inganci ba saboda idan mutum bai yi saurin fitar da azzakarin sa ba yo ko ya fitar inzali zai iya kucce masa a yayin da yake hutawa.

5. Scrotal pull back (Jan fatar 'ya'yan marina daga baya)
Wannan ma wata dabara ce ta tsaida yin inzali a lokacin da ya taso. Idan mutum ya kusa yin inzali ƴaƴan marinar sa sukan taso su laƙe kusa da tushen azzakarin sa domin zuba tantanin halittun haihuwa a cikin bututun fitsari. Toh a lokacin da mutum ya fara jin uzurin inzali ana so ya sanya hannun sa ya kama jan ya'yan marinar zuwa baya (abokiyar saduwar mutum zata iya yi masa). Wannan zai taimaka sosai wajen hana yin inzali. Domin cimma burin wannan dabarar, turawa sun ƙirƙira wasu robobi na musamman da mutum zai sanya ga ƴaƴan marinar sa kamin ya fara jima'i. Waɗannan robobin zasu hana shi saurin inzali(4).
6. Use of condoms (Yin amfani da robar yin jima'i)
Amfani da robar yin jima'i yana rage jin taɓi da kuma yawan sakon da ƙwaƙwalwa ke samu daga jakadun ta da ke azzakari. Hakan yakan sa ƙwaƙwalwa ta daɗe bata yi umurni da yin inzali ba. Duk da cewa akwai robobin jima'i (condoms) na musamman da aka tanada domin rage saurin inzali (kamar irin su Trojan extended pleasure da kuma Durex prolong), amma ko wane condom yana rage saurin inzali bakin gwargwado.

7. Amfani da magungunan shafawa
Akwai magungunan shafawa da aka tanada domin rage yawan saƙon da ƙwaƙwalwa ke samu daga jakadun ta na fatar azzakari. Waɗannan magungunan ana shafa su ne kamar minti goma zuwa goma sha biyar kamin a fara yin jima'i. Rage saƙon da ƙwaƙwalwa kan samu yana ƙarawa mutum lokaci sosai kamin yaji uzurin inzali saboda ƙwaƙwalwa baza ta yi saurin yin umarni da yin inzali ba. Magungunan sun haɗa da(3):
 • Anbestol cream
 • Xylocain Jelly
 • Vagisil cream
 • Nasstoys cream
 • China prolonged pleasure cream da dai sauransu.
A lura cewa yana da kyau a wanke azzakari  kamin a fara jima'i idan an shafa waɗannan magungunan (ba daga shafawa za'a wanke ba, sai yayi kamar minti goma zuwa goma sha biyar) in ba haka maganin zai iya shafar fatar farji sannan ya rage saƙon jindaɗin da fatar ke isar wa ƙwaƙwalwar mace wanda hakan zai rage mata jindaɗin jima'i sosai.

8. Amfani da ƙwayoyin magani
Akwai ƙwayoyin maganin da cikin matsalolin da suke kawo wa mutum idan yasha su akwai rashin yin inzali da sauri. Duk da cewa waɗannan magungunan hukumar bada magani da abinci bata amince ayi amfani dasu domin saurin inzali ba, amma wasu mutane sukan yi amfani dasu sosai wajen tsawaita lokacin inzali da kuma miƙewar azzakarin su.
Waɗannan magungunan sun haɗa da(4):
 • Paroxetine
 • Depoxitine
 • Escitalopram
 • Sertraline
 • Tramadol
 • Sildenafil
 • Tadalafil
A lura cewa, wasu daga cikin magungunan da muka lissafa a sama suna da wasu matsaloli da sukan iya kawo wa mutum, musamman idan yasha su dayawa. Waɗannan matsaloli sun haɗa da ciwon kai, ganin juwa, rashin bacci, ƙara sha'awar jima'i, amai, yawan zufa da kuma rashin narkewar abinci da sauri(4).

Haka zalika, akwai wasu magunguna da ake ganin nan gaba zasu zama jigo a wajen maganin wannan matsalar ta saurin inzali, sai dai har yanzu masana na matakin bincike akansu, waɗannan magungunan sun haɗa da;
 • Modafinil
 • Silodosin
 • Levosulphride
 • Onabotulinumtoxin A

Bayanin rufewa

Saurin inzali matsala ne babba da kan iya kawo hatsaniya a tsakanin ma'aurata. Acikin wannan rubutu munga abubuwan da ke kawo saurin inzali da kuma hanyoyi daban-daban da akan za'a iya magance su. Duk mai tambaya yayi ta acikin akwatin sharhi da ke ƙasa, zamu karɓa masa In sha'Allah.

Nassoshi 
Print this post

Post a Comment

0 Comments