Ko da yake maza dayawa suna sa matsatstsen fatari (ɗan kamfai) ne domin ƙara suturta al'aurar su. Kuma hanya ce ta kare al'aura daga bayyana musamman bayan an saka manyan tufafi kamar riga ko wando. Sai dai masana sun ce sa matsatstsen fatari (ɗan kamfai) na da illah ga lafiyar namiji.
Yadda lamarin yake shi ne, a cikin ƴaƴan marina, nan ne ake samarwa tare da adana ya'yan halittun haihuwa na maniyyi, watau "sperm cells" a turance. Waɗannan ya'yan halittun haihuwa su ne ƙwayayen haihuwa da ɗa namiji ke ba da gudunmawa domin samun ciki.
Daga cikin hikimar Allah na saukar da jakar ƴaƴan marina (scrotum) ƙasa daga ciki, akwai samar da ɗumi ƙasa da ɗumin jiki. Wato ƴaƴan marina su na buƙatar muhalli mai sanyi fiye da sauran kayan ciki domin samar da lafiyayyun tantanin halittun haihuwa.
Saboda haka, saukar da jakar 'ƴaƴan marina ƙasa da jiki yana samar da raguwar ɗumi da maki 4 - 6 a ma'unin salsiyos ƙasa da ɗumin sauran jiki, wanda shi ne kyakkyawan yanayin da ƴaƴan marina za su iya samarwa tare da adana lafiyayyun tantanin halittun haihuwa.
Don haka, sa matsatstsen fatari (ɗan kamfai) zai ɗaga jakar ƴaƴan maraina tare da matse ta ko takura ta da gangar jiki. Hakan kuma zai sa yanayin ɗumin ƴaƴan marina ya ƙaru kuma ya sade da na jiki.
Bincike ya nuna cewa, maza da suke sa matsatstsen fatari tsawon rana ɗaya suna da ƙarancin adadin tantanin halittun haihuwa a cikin ruwan maniyyin su idan aka kwatanta su da mazan da ba sa sa matsatstsen ɗan kamfai. Wanda hakan zai iya kawo rashin haihuwa ga namiji ko kuma matuƙar shan wahala kamin yayiwa mace ciki.
Bugu da ƙari, yawan sanya matsatstsen ɗan kamfai na taƙaita ko rage gudanar jini zuwa a ya'yan marina da ma dukan al'aura, wanda hakan na iya haifar da matsaloli ga lafiyar al'aura.
Har wa yau, ta ɓangaren tsafta kuwa, sa matsatstsen ɗan kamfai na haifar da gumi tare da riƙe danshi ga al'aura da kewayen ta. Hakan kuwa na iya janyo cutukan fata a al'aura da kewaye, kamar irin su kaikayin matse-matsi da sauran su.
Wannan shi ne dalilin da yasa ake ba maza shawarar yin amfani da guntun wando mai yelwa (boxer) maimakon ɗan kamfai, idan kuma har namiji ya nace sai yayi amfani da kamfai toh ya zaɓi ɗan kamfai mai yelwa, ba wanda zai takura al'aura ba.
0 Comments