Me Yake Kawo Jin Zafin Azzakari Bayan Saduwa?

Jin zafin azzakari

1. Goge-goge mai tsanani

Idan farjin mace ya bushe ko ba'a sami isasshen ruwan ni'ima ba, gogayyar fata da fata na iya haifar da jin zafi ko yan kananan raunuka a kan azzakari. Haka kuma saduwa da karfi ko ba tare da shiri ba na iya haddasa irin wannan jin zafin.

Rubutu Mai Alaka: Ire-iren Azzakari Da Sahihan Bayanai Akan Azzakarin Namiji

2. Tsananen jin taɓi bayan releasing

Bayan releasing, azzakari yakan zama mai matuÆ™ar jin taÉ“i (high sensitivity). Idan aka ci gaba da saduwa ko aka taÉ“a shi da sauri, zaka iya jin zafi ko Æ™una. Wannan ba matsala ce ta lafiya ba — halittar jiki ce kawai.

3. Ƙananan raunuka

Wani lokaci Æ™aramin rauni ko gogewa na iya faruwa yayin jima’i, musamman idan babu isa­shen ruwan ni'ima daga mace ko an yi jima’i da karfi ko ba tare da ra'ayin mace ba.

Ku karanta: Jarababben Namiji: Fadakarwa Akan Alamomin Rashin Lafiyar Namiji

4. Cutar magudanan fitsari 

A lokacin da maniyyi ke fitowa ta bututun fitsari, idan akwai ƙaiƙayi, kumburi ko kamuwa da wani irin infection ko cutar magudanan fitsari, zaka iya jin zafi yayin releasing ko bayan haka.

5. Rashin jituwa da condoms, gel ko sabulu

Wasu na samun matsalar fata ta hanyar amfani da mayukan shafawa (lubricants) ko latex, lubricants ko sinadarai da ke cikin condoms ko gel, wanda ka iya janyo zafi ko kaikayi.

Tsaraba: Abubuwan 18 da ke kawo rashin haihuwa ga maza: 18 Common causes of male infertility in Nigeria

6. Infections

Wasu cututtuka kamar urethritis, chlamydia ko gonorrhea na iya haifar da zafi, fitsari mai ƙuna, yawan fitsari, ko fitar ruwa mai wari daga azzakari.

Me zaka kula da shi a jikinka?

Idan zafin yana faruwa ne bayan kawowa na farko kuma baya maimaituwa, yawanci ba matsala ce mai tsanani ba. Yana iya zama sensitivity ne ko gogewa kawai. Amma ka tuntuɓi likita idan:

  • Zafi baya dainawa har bayan saduwa,
  • Zafin yana maimaituwa,
  • Kana jin zafi lokacin fitsari,
  • Kana fitar wani ruwa mai wari ko launi.

Abubuwan da zaka iya yi idan ba ka da alamun infection

Ka tabbatar mace tana da isasshen ruwa na sha’awa kafin ku fara.

Idan mace a bushe take, bata da ruwan ni'ima, amfani da lubricant mai kyau zai taimaka.

Kada ka cigaba da jima’i nan da nan bayan kawowa na farko; bari jiki ya dan sarara.

Ka guji sabulun da ke busar da fata ko haifar da kaikayi.

Ka sha ruwa sosai, sannan ka rika cin abinci mai kyau tare da multivitamin da zinc domin lafiyar azzakari.

Idan matsalar ta maimaitu ko ta tsananta

Ka je wajen likitan urology ko a STD Clinic domin a duba ka, a yi gwaji, a kuma ba ka magani idan an sami infection.

Ku karanta: Alamomi, abubuwan dake haddasawa da kuma maganin saurin inzali (Premature ejaculation)

No comments: