Auren dole, ko auren tilasta wa ƴaƴa auren wanda ba sa so matsala ce da ta daɗe tana lalata rayuwar mutane. Mata su ne mafi yawan waɗanda ake tursasa wa su auri wanda ba sa so. Shi namiji ko bai son mace, shi zai iya ƙara aure da wacce yake so.
Amma mace ba ta da wannan damar, idan ta ƙi bin umarnin iyaye ta ƙi zama, darajarta na raguwa a idon mutane, domin a al'ada irin tamu ta Hausawa, bazawara ba ta kai budurwa daraja ba.
Wasu na yawan cewa wai mai sonki ya fi wanda kike so. Wannan magana ba gaskiya bace. Aure na samun zaman lafiya ne idan soyayya ta kasance a ɓangarorin biyu, ba a ɓangare ɗaya kawai ba. Ta ya za ki kyautatawa wanda yake ba kya son shi? Shi dai zai iya kyautata miki, amma ke zai wahala ki iya kyautata masa.
Cikakken Bayani: Yadda Mace Zata Dinga Yin Binciken Nono Ko Gwajin Nono A Gida Domin Gano Matsalar Nono Da Wuri
Wasu matan da aka tursasa musu auren wanda ba sa so daga baya sukan koma bin tsofaffin samarin da suke so. Wasu har sukan shiga hanyar da bata dace ba da sunan huce takaicin aure. Wasu ma zuciyar su tana bushewa, idan shaiÉ—an ya samu galaba a kansu su aikata kisa ko su kashe kansu. Duk wannan yana faruwa ne dalilin auren da babu soyayya, wanda aka jefa mutum cikin shi ba da yardarsa ba.
Ga waɗanda suka karɓi auren saboda suna tsoro ko don su girmama iyayensu, suna zama cikin ƙunci da rashin walwala. Duk kyautatawar da za a musu, ba zai taɓa sa su farin ciki ba, domin an keta musu haƙƙinsu na zaɓin wanda suke so. Soyayyar nan fa ba wasa bace!
Amma kuma akwai wani abu mai muhimmanci da ya kamata duk wani mai hankali ya lura da shi. Iyayen da suke hana ƴaƴansu auren wansa suke so, ba wai suna yi ne don mugunta ba. Sau da yawa suna yin hakan ne saboda hangen nesa da kwarewar rayuwa, suna hango abun da kai bai zama lallai ka iya hango shi ba. Suna ganin abin da ke ɓoye a bayan soyayyar ƙuruciya da sha'awa.
Idan yaro ya bi umarnin iyayensa cikin girmamawa da kyakkyawar niyya, zai samu nutsuwa ya gane amfanin hakan nan gaba. Bin umarni da biyayya wani lokaci yana kare mutum faÉ—awa cikin ramin da bai san zurfinsa ba.
Sai dai duk da haka, iyaye su tuna cewa su ne manya, akwai illoli a tilasta wa mutum rayuwar da ba ya so. Nasiha da jagoranci ya dace su yi, ba tursasawa ba. Soyayya da yarda su ne ginshiƙin aure, ba cusawa mutum tsoro ta hanyar yi masa mummunan baki/fata ba.
Ga waɗanda suka haƙura saboda tsoron Allah da ƙoƙarin farantawa iyayensu, suka tsare mutuncinsu, suna tare da lada da albarka. Amma kuma wanda ya ci amanar aure, ya aikata abin da bai dace ba saboda ya auri wanda ba ya so, ya sani cewa Allah ba Ya goyon bayan wannan zalunci. Ki faɗa masa gaskiya idan bakya son shi. Kai ma idan an ce ba a sonka, ka haƙura ka yi mata fatan alheri.
Idan kana da hankali, ba sai ta ce ba ta son ka ba, akwai abubuwan da zata maka wanda zai nuna maka cewa lallai ba kai ne zaɓin ta ba. Ka mata fatan alheri kawai, Allah zai ba ka wacce ta dace da kai. In kuwa ka takura ka matsa aka aura maka, to duk abin da ya faru kai ka ja ma kanka.

No comments:
Post a Comment