TRAUMAGEL: Sabon Maganin Tsayar da Zubar Jini Nan Take – Fasahar da Za ta Ceci Miliyoyin Rayuka

Maganin tsayar da jini

Kididdiga daga sassan duniya na nuna cewa zubar da jini — musamman sakamakon haÉ—urran mota, haihuwa, da wasu bala’o’i — yana janyo asarar rayuka masu yawan gaske a kowace shekara a fadin duniya. Amma yanzu an samo wata sabuwar fasaha  da ake tunanin amfani da ita zai iya rage wannan matsala ta zubar jini matuÆ™a, har ma a dakatar da rasa rayuka saboda zubar da jini.

Wannan nasara ta samu ne sakamakon ƙoƙarin wani injiniyan kimiyyar lafiya daga Amurka mai suna Joe Landolina, wanda shi ne wanda ya kafa kamfanin Cresilon dake birnin New York.

Zaku iya duba: Maganin Mata da Lafiyar Mace: Abubuwan da Ya Kamata Kowace Mace ta Sani

A cikin shekarar 2025, wannan matashi mai hazaka ya sake jawo hankalin masana da al’ummar duniya ta hanyar Æ™irÆ™irar wani muhimmin magani mai kama da gam mai suna TRAUMAGEL, wanda ke iya tsayar da zubar jini nan take — ba tare da buÆ™atar tiyata ko amfani da É—aure ba.

TRAUMAGEL yana cikin rukunin magungunan da aka samo daga tsirran ruwa na algae, kuma ana amfani da shi cikin sirinji. Idan aka ɗiga shi a wurin da ke zubar da jini, yana haɗuwa da sinadarai na jinin mutum, sannan cikin ƴan daƙiƙu kawai sai jinin ya daskare, ya rufe jijiyar da ke zubar da jinin gaba ɗaya.

Maganin zubar jini
Gwaje-gwajen da aka gudanar sun tabbatar cewa TRAUMAGEL ba kawai yana dakatar da zubar jini bane, har ma yana taimaka wa rauni ya warke cikin sauri.

Kafin wannan sabuwar ƙirƙira, mutane kan dogara da hanyoyin gargajiya kamar ɗaure jiki da maɗauri ko amfani da sinadarai na tsaftace rauni kafin isa asibiti. Amma yanzu, wannan gel ɗin yana iya ceton rayuwa nan take, musamman a wuraren da agajin gaggawa ke da wahalar samu.

A shekarar 2024, Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Amurka (FDA) ta amince da amfani da TRAUMAGEL bayan kammala nazarin inganci da amincinsa.

Ku karanta: Yadda Ake Samun Cikin ‘Yan Biyu — Cikakken Bayani a Hausa

Haka kuma, an saka shi cikin jerin ƙirƙirarrun fasahohin da ake sa ran za su lashe kyautar Prix Galien USA 2025, wadda ke ba da yabo ga sabbin kayan kimiyya masu tasiri a lafiyar ɗan adam.

A halin yanzu, an fara amfani da TRAUMAGEL a wasu asibitocin Amurka, kuma masu aikin ceto, masu ba da taimakon farko, da jami’an gaggawa sun fara amfani da shi wajen tsayar da zubar jini kafin marar lafiya ya isa asibiti.

Da yake wannan ƙirƙira na iya canza tsarin kula da rauni a duniya, tambayar da take gabanmu ita ce:
Shin yaushe za mu fara ganin TRAUMAGEL a asibitocin mu na Najeriya? Ku rubuta min a comment section.

No comments: