Gabatarwa
A al’adance da kuma a zamanin yau, maganin mata ya zama sanannen abu a tsakanin mata da maza ma’aurata. Ana kiran wannan magani da sunaye daban-daban, wasu suna kiransa maganin inganta mace, maganin karfin sha’awa, maganin rike miji, ko kuma maganin kara karfin jima’i.
Yawancin mata suna amfani da shi domin Æ™ara jin daÉ—in saduwa, kara karfin sha’awa, ko kuma domin jan hankalin namiji. Duk da haka, masana lafiya sun sha gargadi cewa amfani da maganin mata yana iya kawo illoli masu tsanani ga lafiyar mace idan ba a yi amfani da shi yadda ya dace ba.
A cikin wannan rubutu za mu tattauna dalla-dalla game da illolin maganin mata, dalilan da yasa mata ke amfani da shi, da hanyoyin da za a bi don kauce wa haÉ—ari.
Ku karanta: Yadda Ake Tsokano Sha'awar Namiji Zuwa Kwanciyar Aure
Menene Maganin Mata?
Maganin mata kalma ce da ake amfani da ita wajen kiran duk wani sinadari, ganye, ko kwaya da ake ikirarin yana taimaka wa mace wajen:
- Ƙara sha’awar jima’i
- Rage bushewar farji
- Tsawaita lokacin jima’i
- Inganta kuzarin mace
- Jan hankalin namiji ko ƙarfafa dangantakar aure
Akwai nau’ukan maganin mata guda uku da suka fi shahara:
1. Maganin mata na gargajiya: Wannan ya haɗa da ganye, ƙwayoyi, shayi, ko man gyada da ake haɗawa a gida ko a kasuwa.
2. Maganin mata na zamani: magungunan da ake siyarwa a kantin magani ko online ta hanyoyin sada zumunta.
3. Maganin mata na abinci da kayan marmari: irin su zuma, kankana, kubewa da kwakwa da ake dangantawa da kara kuzarin mace.
Ko da yake wasu daga cikin waÉ—annan suna da amfani idan aka yi amfani da su yadda ya dace, amma akwai kuma illoli masu yawa da ke tattare da wasu.
Illolin Maganin Mata
1. Matsalolin Al’aurar Mace
Amfani da maganin mata na iya jawo zubar jini a farji, farin ruwa ko kumburi, ko tsananin kaikayin gaba.
Karin Bayani: Maganin Kaikayin Gaba Na Budurwa: Meke Kawo Kaikayin Gaba Na Mata
Wasu mata suna samun ƙuraje da ciwon ciki sakamakon amfani da sinadaran da ba a gwada ba.
2. Rikicewar Sinadaran Hormones na Mace
Magungunan mata na iya yin tasiri kai tsaye a kan hormones na mace. Wannan yana iya haifar da:
- Tsayawar haila ko rikicin jinin haila
- Matsalolin haihuwa
- Kiba ko yawan ramewa fiye da kima
Domin karin bayani game da rikicewar sinadaran hormones ku karanta: Rikicewar Sinadaran Hormones A Jikin Mace (Hormonal Imbalance)
3. Illolin ga Zuciya da Hawan Jini
Wasu sinadarai na haifar da hawan jini (hypertension).
Wasu na iya jawo bugun zuciya ga mata masu matsalar zuciya.
4. Dogaro da Magani (Addiction)
Mace na iya sabawa da amfani da maganin mata har ba za ta iya jin sha’awar namiji ko jima'i ba sai ta sha shi.
Wannan yana iya lalata dangantakar aure idan mijin ya gano mace ba ta da kuzari idan babu magani.
5. Matsalolin Hanta da Koda
Bincike ya nuna cewa yawan amfani da magungunan mata na iya lalata hanta da koda.
Mata masu ciki suna iya jawo lalacewar jariri idan sun yi amfani da wasu irin maganin mata.
6. Rashin Inganci
Yawancin maganin mata da ake siyarwa a kasuwanni ba su da rajistar hukumar lafiya (NAFDAC ko WHO). Wannan yana nufin mace na iya shan sinadaran da suka ƙunshi guba ba tare da ta sani ba.
7. Matsalolin Zamantakewa
Yawancin mata suna amfani da maganin mata ne saboda matsin lamba daga mijin su ko abokin tarayya. Hakan kan haifar da matsala a dangantaka saboda mace za ta iya kasa samun sha’awa idan babu magani.
Dalilan Da Kesa Mata Amfani da Maganin Mata
1. Karancin sha’awa saboda damuwa, gajiya, ko matsalolin lafiya.
2. Tallace-tallace a kafafen sada zumunta da ke yaudarar mata da sakon “maganin rike miji”.
3. Son gwaji da karfin sha'awa.
4. ƘoÆ™arin faranta wa miji rai a lokacin jima’i.
Duk da wadannan dalilai, amfani da maganin mata ba tare da kulawar likita ba yana iya zama haÉ—ari.
Hanyoyin Kariyar Lafiya Daga Illolin Maganin Mata
1. Neman shawarar likita: Idan mace na fama da rashin sha’awa ko bushewar farji, ya dace ta tuntuÉ“i likita.
2. Motsa jiki da cin abinci mai kyau: Abinci kamar kifi, kayan marmari, ganye, da zuma suna ƙara kuzari.
3. Guje wa damuwa: Yin hutu da gudanar da rayuwa cikin annashuwa yana taimakawa wajen Æ™ara sha’awa.
4. HulÉ—a mai kyau da abokin aure: Kyakkyawar fahimta da soyayya tsakanin ma’aurata na Æ™ara kuzari ba tare da maganin mata ba.
5. Guje wa magungunan da ba su da lasisi: Kada a sayi maganin mata a kasuwa ko online ba tare da tabbatar da ingancinsa ba.
Shawarar Masana Lafiya Akan Amfani Da Maganin Mata
Likitoci suna gargadi cewa maganin mata na gargajiya ko na zamani da ba a tabbatar da ingancinsa ba, na iya haifar da haÉ—ari ga lafiyar mace.
Mata masu ciki, masu shayarwa, ko masu cututtukan zuciya su guji amfani da irin waÉ—annan magunguna ga baki É—aya.
Kowace mace da take fuskantar matsalar sha’awa ya kamata ta tuntuÉ“i likita saboda akwai hanyoyin magani na kimiyya masu aminci.
Kammalawa
Maganin mata yana da haÉ—ari fiye da amfanin da yake samarwa na kankanin lokaci. Duk da cewa wasu suna iya bayar da É—an kuzari na wucin gadi, illolinsa sun haÉ—a da:
- Rikicewar sinadaran hormones.
- Matsalolin zuciya da hawan jini.
- Matsalolin hanta da koda.
- Rashin haihuwa.
- Dogaro da maganin.
Don haka, mata su yi taka-tsantsan wajen amfani da maganin mata saboda haÉ—arin da ke tattare da shi. Kyakkyawar hanyar inganta lafiyar mace a fannin jima'i ita ce:
- Shawarar likita.
- Abinci mai kyau.
- Motsa jiki.
- Kyakykyawar hulÉ—a tsakanin ma’aurata.
No comments:
Post a Comment