Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Kaikayin Gaban Mace: Me Ke Kawo Kaikayin Gaba Da Kuma Yadda Ake Maganin Kaikayin Gaba

Kaikaiyin Gaba


Shin yar uwa kin taba fuskantar wani mummunan kaikayin gaba, har wasu su ce miki ai baki da tsafta, ko kuma wasu su ce ai kin je wani wurin kwashe-kwashe ne kin kwaso wa kanki wannan kaikaiyin?

Yar uwa da kike karantawa, na tabbata mata dayawa sun taba shiga cikin wannan yanayin, amma kuma kamar yadda nace wasu. 

Shin kin taba shiga wani yanayi kamar kin tafi makaranta ko kuma kinje wurin aiki, ko kuma kin shiga banki, ko kuma kasuwa, kwatsam sai ki ji wani kaikayin gaba ya taso miki, ki rasa yadda zakiyi? 

Kuma dayawa irin wannan kaikayin gaba ba wai yana zuwa kadan kadan bane, a'a wani irin kaikayi ne yake zuwa kwatsam kamr harbin bindiga sai ki rasa yanda zakiyi.

Idan wannan mugun kaikayin gaba ya tasowa mace akwai wadanda suna iya basarwa, ko yayane ba ma zaku gane me suke ciki ba, wasu kuma ƴan gayun sai suyi amfani da cinyoyin su sai su haɗe cinyoyin su domin su sosa kadan wata kuma za tace "Oho babu ruwana!!" ta kalli nan ta kalli chan, in babu wanda yake kallon ta tasa hannu ta sosa abin ta, wata kuma sai ta shiga banɗaki taje ta sosa abin ta. 

Toh ko ma yaya ne, duk wanda kika kasance kina yi ba wanda zai magance miki wannan kaikayin gaba na dim dim dole sai kin je kin ga likita ko kin nemi magani a asibitin kwararru.

A yau zamuyi magana akan wannan kaikayin gaba da mata suke fuskanta, zamu tattauna a kan shin me yake janyo wannan kaikaiyin gaba? Akwai wani abu ne da mutane suke yi da ke janyo musu da kaikayin gaba? Ko kuma akwai wasu abubuwa ne da ya kamata mata su daina yi domin su kare kan su daga wannan matsalar ta kaikayin gaba? 

Me Ke Kawo Kaikaiyin Gaba 

Toh akwai jerin abubuwan daban daban da suke kawo irin wannan kaikaiyin gaba. Zamu tattauna wadannan abubuwan da ke kawo kaikaiyin gaba kamar haka.

 1. Ayyukan da mata ke yi masu kawo kaikaiyin gaba
 2. Cututtukan da ake kwaso wa ta hanyar jima'i masu kawo Kaikaiyin gaba
 3. Cututtukan da basu da alaƙa da jima'i masu kawo kaikaiyin gaba 

Al'adun mata ko abubuwan da mata ke yi masu kawo kaikaiyin gaba 

Shin kun san me yasa kusan a koda yaushe wasu mata suna fuskantar wannan kaikayin gaba? Kamar yadda muka sani gaban mace fah a rufe yake kuma duk inda a kace muku a rufe yake toh ba za a rasa akwai danshi a wajan ba. Banda danshi akwai abubuwan da suke fitowa daga gaban mace da ke buƙatar tsaftace wa, kamar irin su:

 • Jinin al'ada
 • Fitsari
 • Ruwan ni'ima 
 • Maniyyi - idan mace ta fara saduwa 

Banda wannan kuma yanayin da mata suke aski, daban daban ne, akwai wadanda suke amfani da razor, akwai wandanda suke amfani da halawa kamar yadda kuka sani wato wax, kamar yanda ake kiran shi asa takarda a ɗaye, wasu kuma su saka sugar su ɗaye, wasu kuma duka razor hair removal suke amfani dashi, wasu kuma suyi amfani da cream ne wato wani kalar man shafi da ake shafawa mai cire gashi.

Sannan kuma akwai wani sabon abu da ake yi a yanzu wai wato gaban mace yana da turaren shi. Oooh mata hoo!!! Wata ta saka turare a wajen, wata ta dumama wajen, wasu har dafa wajen ma suke yi, su shiga baho da ruwan zafi wai suna gasa wajan. 

Banda wannan kuma wasu mai suke shafawa a cikin wajen, wai akwai na musamman da ake shafawa gaban mace.

Wasu kuma suna amfani da wasu irin sinadaran chemicals na bature wadanda zaku gani ana siyar dashi ana cewa mace ta dinga wanke wajan dashi.

Toh duk fah waje daya, wadannan abubuwan da muka zayyano suke saka wasu mata basu taba rabuwa da kaikayin gaba.

Cututtuka Masu Yaduwa Ta Hanyar Jima'i masu kawo kaikaiyin gaba (Sexually transmitted Infections - STIs). 

Me Sexually transmitted infection ko kuma STI yake nufi? Yana nufin wato sanyi da ake daukar shi ta hanyar saduwa. Akwai sexually transmitted infections dayawa masu sanya kaikaiyin gaba, zamu dauki manyan da suka fi addabar matan mu a yau domin mu yi tsokaci a kan su.

1. Cutar Sanyin Trichomoniasis

Wannan wata cuta ce da ke yaɗuwa ta hanayar saduwa wadda kwayar cutar Trichomonas vaginalis take kawo wa. Shi trichomoniasis shi ma wannan wani kalar sanyi ne da ake ɗaukar sa ta hanyar saduwa wanda ke kawo wa mata matsanancin kaikaiyin gaba.

Amma kada ku manta shi kaikayin gaba alama ce ta cuta daban daban, bawai mace idan taji kaikayin gaba zata ce ai wannan cuta ce ba, a'a kaikayin gaba, symptoms ne, abu ne da mace zata ji a jikin ta. Shi kuma symptoms, cututtuka dayawa na iya kawo shi.

Kaikaiyin gaba yana daga cikin manyan alamomin (symptoms) na cutar sanyin trichomoniasis. Sauran alamomin sun hada da; 

Mace za ta ga ruwan gabanta yana fitowa, yellow yellow, ɗorawa ɗorawa, kore kore haka, yawanci an fi sanin sa da yellow-green, zaku ganshi tsakanin kalar dorawa da kuma kore. 

Banda wannan kuma, wata kuma tana iya fuskantar kaikayin gaba, sannan yayin saduwa tana jin zafi, sannan yayin fitsari ma tana iya fuskantar zafi

Duk da dai cewa akwai mata masu yawa da suke da wannan cutar, amma mafi akasari basusan suna dauke da ita ba, saboda wani sa'ilin cutar baya zuwa da kaikayin gaba kai tsaye, sai dai yazo da ruwan gaban mace ya dan chanza kala kamar yadda muka yi bayani a baya, idan tana da lura za ta gane.

 2. Kurajen Al'aura na Herpes (Genital herpes)

Kurajen al'aura na herpes ko kuma genital herpes a turance shi ma wani sanyi ne da ake daukan shi ta hanyar saduwa. Wannan cutar ta kan fesowa mace da wasu kalan kuraje a gabanta, kurajen suna kama da kurajen wucewar zazzaɓi da yake fitowa mutane akan lebban su. 

Irin wadannan kurajen su ake kira blisters da turanci, zaku gansu sun fito a kan lebban gaban mace ko a kan kumburin dinka. Wani sa'ilin yana dan fitar da ruwa kadan marar kala. Mace tana iya fuskantar matsanancin kaikayin gaba idan ta samu wannan cutar.

Haka kuma, kaikayin gaba yafi ma mace tsanani a yayin da ta saka wandon fatari na roba, watau idan pant dinta yana taɓa wajan yana gurza kurajen.

3. Kwarkwatar Gaba (Pubic Lice)

Kwarkwatar gaba wasu kwarin kwarkwata ne da ke zama a cikin gashin mara da sauran gashin gaba. Ana samun su ne ta hanyar cuɗanya yayin jima'i da wanda yake dauke da kwarkwatar.

 Kwarkwatar gaba daban ce da  kwarkwatar da take fitowa mutane a kai kamar yadda zaku gani a kan hoton da ke kasa. 

Kwarkwatar gaba da yake fitowa ana daukar shi ne ta hanyar saduwa, wato su waddannan kwarin din suna tsalle ne daga jikin mutum daya zuwa jikin abokin saduwa. Kuma kamar yadda muka sani, su kwarin kwarkwata daman shan jini suke yi anan ne abincin su yake. 

Haka kuma, suna yin ƙoyayen su a cikin gashin mara, suna sakin ƙoyayensu a gaban mace da gashin marar namiji. 

Idan mace ta kamu da wannan kwarkwatar suna sa ta dinga samun matsanancin kaikayin gaba, sannan kuma kaikayin yafi tsanani a lokacin dare.  

Toh amma kar ku tsorata saboda akwai maganin da ake iya bayarwa kuma mace ta warke daga kwarkwatar gaba. 

Kaman yadda ku kaji ance kwarkwata, wasu za su dauka babban cuta ce. A'a ana iya bada magani sannan kuma a warke. Saboda haka idan mace tana yawan samun matsanancin kaikayin gaba da zarar ance miki dare ya fuskanto, toh ta garzaya zuwa asibiti domin neman magani, takan yiyu kwarkwatar ce.

Cututtuka Masu Kawo Kaikaiyin Gaba, Wadanda Basuda Alaƙa Da Jima'i 

Akwai waɗansu cututtukan da ke kawo kaikayin gaba, waɗanda ba ta hanyar jima'i ake samun su ba. Irin wannan kalar kaikaiyin gaba ba wai mace ta samu yayin saduwar aure bane. Akwai cututtukan da muke ce ma non STI Causes. Su ba saduwa yake kawo su ba. Zamu ga wadansu daga cikin su kamar haka:

1. Cutar Kazuwa - Scabies 

Kazuwa kamar yadda muka sani cuta ce ta fata wadda ke sanya kurajen fata da kuma kaikayi. 

Yayin da cutar kazuwa ta kama mace, ƙwayoyin cutar suna shiga a karkashin fata ne, idan suka shiga sai suje su ajiye ƙwoyayen su a nan. Toh a  yayin da suka ajiye ƙwoyayen su a karkashin fatar gaban mace, hakan yana janyo kaikayi sosai a gaban mace. 

Shima ƙaiƙayin kazuwa yafi tsanani da daddare. Don haka yana da kyau mace ta kiyaye lokutan da kaikayin gabanta ya fi tsanani domin taimakawa likita gane abun da ya kawo mata kaikayin gaba.

2. Tsutsotsi  - Thread Worms

Thread worms wasu tsutsotsi ne da ake iya samu a gaban mace. Mafi akasari waɗannan tsutsotsi suna fitowa ne ta banhaya ko ta duburar mace kamin su ja jiki zuwa a gabanta. 

Toh a yayin da suka fito a wajen sukan iya janyo wani irin kaikaiyin gaba sosai da mace zata dinga fuskanta. Shima wannan ƙaiƙayin gaba da wadannan tsutsotsi ke kawo wa, yafi tsanani da dare, saboda a wannan lokacin ne mafi yawan tsutsotsin ke fitowa.

Haka kuma idan tsutsotsin suka fito suna iya yin ƙwoyaye a gaban mace, wanda hakan yakan sa kaikayin gaba ya ta'azzara.

3. Cutar Contact Dermatitis 

Shin kun san me yafi janyo wa mata dayawa matsalar samun ƙaikayin gaba? A cikin cututtukan da ke kawo kaikaiyin gaba wadanda ba ta hanyar jima'i ake samun su ba, contact dermatitis ita ce tafi kawo wa mata kaikaiyin gaba.

Cutar contact dermatitis, cutar fata ce dake faruwa a lokacin da wani sinadari ko chemical ya taɓa fata. Fata takan yi kumburi tayi jaa a duk lokacin da wani abu ya taɓa ta wanda ba ta lamunta ba. Wannan cutar tana kawo kaikaiyin gaba ga mata yayin da suke amfani da wani abu a gaban su, wanda bai kamata ba. 

Me yiwuwa tana amfani da turare a wajan, me yiwuwa tana tsarki da sabulu mai kamshi dake ɗauke da wani sinadarin chemical, ko kuma tana amfani da audugar tarye jini dinnan da za su zo za kuji suna kamshi haka, ko kuma tana wani abunda bai kamata ba a gabanta, ko kuma tana amfani da abubuwan da mata suke turawa a cikin gaban su. 

Ko kuma macen da ke samun dryness wato bushewar gaba, tana amfani da wani lubricant mai dauke da wani sinadari. Toh yayin da za taje sayen lubricant kar taje ta saye irin wanda yana da kamshin nan, ko kuma yana da flavours da dai sauransu.

Duk irin wadannan abubuwan suna iya janyo wa mata kaikaiyin gaba, kai har ma da condom wato kororon robar kariya ta jima'i, akwai wandanda zasu iya janyo wannan kaikaiyin gaba.

4. Cutar Psoriasis 

Cutar psoriasis ita ma wata cutar fata ce da ana iya samun ta a ko'ina a fatar mutum. Idan wannan cutar psoriasis ta fito a gaban mace, tana haifar mata da kaikayin gaba sosai da kuma wasu kananan kuraje. 

Kurajen psoriasis zaku gan su kamar hawa uku ne a fata zaku gan shi wajan yayi ja ja, akwai farare fararen abubuwa a kanshi idan mutum na da haske kenan. Amma ga bakaken fata, idan mace na da duhu, wannan baya fitowa sosai.

Duk da dai mun san cewa gaban mace ko da yaushe yana da danshi, wannan yasa ba'a cika ganin farin abubuwan ba. Saboda haka, wani sa'ilin kurajen psoriasis baya nunawa idan ya fito a gaban mace amma za ta fuskanci kaikayin gaba da sauransu.

5. Yoyon Fitsari 

Matan da suka samu matsalar yoyon fitsari, watakila wajen haihuwa ko kuma dogon nakuda suna samun kaikayin gaba. Wannan kaikayin gaba ya samo asali ne saboda sinadarin urea dake ke cikin fitsari yana cin fatar gaba a lokacin da ya ke taɓa ta a koda yaushe.

6. Cututtuka na tsawon rai

Cututtuka na tsawon rai wadanda ba'a warkewa dagaresu kai tsaye, kamar irin ciwon koda, ciwon hanta da kuma ciwon sugar, duk suna iya kawowa mace kaikayin jiki da kuma kaikayin gaba.

Musamman ciwon sugar, yana rage karfin garkuwar jikin mace, daga nan sai ya bada damar kananan ƙwayoyin cuta su sanya mata kaikaiyin gaba.

Maganin Kaikayin Gaba 

Shin kun lura da cewa yayin da mutum yake jin Kaikayi a wani sashen jikin sa, idan ya fara  sosawa a lokacin kaikaiyin yake ƙaruwa? Dalilin wannan shi ne, yayin da mutum yake sosa kaikayi akwai abinda muke kira nerves ending a likitanci (watau jakadun ƙwaƙwalwa dake kan fata), wadannan jakadun suke daukar sakon kaikayi da kuma taɓi su aikawa ƙwaƙwalwa. Susa tana kara tunzura wadannan jakadun, saboda yawan sosa fata yana kara aika sako zuwa ƙwaƙwalwa, haka itama ƙwaƙwalwa tana kara maida martani. So a duk lokacin da mutum ya sosa jikin jakadun sukan kara tunzura su aika sako, daganan sai kaikayin ya ƙaru shi ma.

Wannan shi yasa yana da muhimmanci yayin da mutum yana jin wannan kaikaiyin to yayi kokari kar ya sosa shi. Amma mutum zai iya dinga dan daddannawa da hannu, bawai mutum ya dinga gurza jikin shi ba. 

Ba'a son mutum ya gurza don kar yazo ya jiwa kansa ciwo. Saboda ta hanyar wannan ciwon wani bakteriya zai iya shiga a jikin mutum ya janyo wani kalar infection na daban. 

Kamar yadda nace mata dayawa suna fuskantar wannan kaikayin gaba, amma basa iya magana, wasu wai sai su ce kunya ne, wasu kuma su ce tsoron su ke su fada ayi zargin wani dalili ne ya janyo musu kaikayin. 

Wannan shi yasa wasu sun gwammace suyi tsit da bakin su. Toh amma anan babu boyewa zamuyi magana a kan duk abinda ya kamata.

Shin akwai wasu abubuwan da ya kamata mata su dinga yi yayin da suke samun wannan matsalar? Ko kuma akwai wasu abubuwan da ya kamata suna yi domin kare kansu daga wannan matsalar?

Toh 'yaruwa yayin da kika fara jin wannan kaikayin gaba, ƴaruwa kar kiyi saurin caka caka ki sosa kamar yadda muka yi bayani a baya. 

In ma dai kin dage sai kin sosa gurin, toh ki tabbatar farcen ki ba dogaye bane, ki tabbatar baki da farce sannan ki dan sosa. Haka kuma ki tabbatar hannun ki ba datti. 

Banda wannan kuma mata masu feshe feshen turare a gaban su, wasu suna ajiye turare na musamman kawai na wajen ne, wai su a dole su ne iyayen tsafta. Wasu suna bleaching wurin, wasu suna gasa wurin, wasu suna amfani da sabulu mai karfi da kamshi a wurin. Ina so mata ku sani, a gaban mace bai kamata ana yin duk irin wadannan abubuwa ba. 

Haka kuma akwai sabulun wanki da omo masu kaifi da suke kode tufafi. Suma wadannan bai kamata mace na amfani dasu tana wanke pant dinta ba, ya kamata mata su wanke pants din su da wanda baya da kamshi kwata kwata. 

Mata masu saka matsatstsin kaya, shima ƴar uwa ku daina yawan saka ɗamammun underwears, musamman in ba na auduga ba ne. Matsatstsin underwaters na roba suna iya kawo cutar contact dermatitis.

Yaushe Ya Kamata Mai Kaikaiyin Gaba Ta Je Asibiti?

 • Ƴaruwa yayin da kika fara jin wannan kaikayin gaba sai fah a hankali ko kuma 
 • Ki dinga ganin ruwa mai kala yana fitowa
 • Ko kuma ki dinga ji kina fitsari da zafi
 • Ko kuma yayin da kike saduwa kina jin zafi
 • Ko kuma kina jin wajan yana wani irin wari
 • Ko kuma kiga wajan yayi jaa!

Toh ƴaruwa ba lokacin da zaki haɗe wannan a baho bane ki zauna ki gasa wajan ba, lokaci ne za kiyi maza ki tattara ƙafafuwan ki, ki tafi asibiti domin a duba ki a baki magani.

Nassoshi

1. Jessica A. Savas, Rita O. Pichardo, Female Genital Itch, Dermatologic Clinics, Volume 36, Issue 3, 2018, Pages 225-243, ISSN 0733-8635, ISBN 9780323610803, https://doi.org/10.1016/j.det.2018.02.006.

(https://www.sciencedirect.com/science/article/pii/S0733863518300172)

2. Lawton, Sandra MSc; Littlewood, Sheelagh MB, ChB, FRCP, Vulval Skin Conditions, Disease Activity and Quality of Life, Journal of Lower Genital Tract Disease 17(2):p 117-124, April 2013. | DOI: 10.1097/LGT.0b013e3182652450

Print this post

Post a Comment

0 Comments