Ad Code

Responsive Advertisement

Ticker

6/recent/ticker-posts

Tusar Gaba Ko Fitar Iska Ta Gaban Mace - Queefing

Tusar gaba


Tusar gaba ko kuma fitar da iska mai kara da karfi ta gaban mace lokacin jima'i ko ma wasu lokuta da basu da alaƙa da jima'i, matsala ce mai kunyatar da mace a idon mijinta ko ma cikin jama'a idan hakan ya faru da ita a cikin taro. 

A cikin wannan rubutu, zamuyi tsokaci game da abubuwan da ke kawo tusar gaba ko kuma fitar iska daga gaban mace da kuma hanyoyin da za'a maganin tusar gaba.

Mene ne Tusar Gaba

Tusar gaba wani iska ne dake fitowa daga gaban mace mai karfi da kara a lokacin da mace take saduwa ko ta durƙusa ko tayi wani yunkuri, watarana tusar ma ta kan zo haka kawai ba tare da mace na yin wani aiki ba.

Ba kamar tusar ciki ba, ita tusar gaba ba ta da wari ko ɗoyi, sai dai tana da babbar matsala ga ajin mace a idon mijinta da kuma sauran jama'a.

Watarana tusar gaba idan tayi yawa lokacin saduwa tana sa namiji ya tsani mace, ya daina jin sha'awar ta kuma yaji baya son saduwa da ita.

Yawanci mata dayawa na fuskantar wannan matsalar ta tusar gaba, amma basu san me yake kawo musu matsaalar ba, balle su san hanyoyin da za su bi su kare kansu dagareta ko kuma su maganin ta.

Me Ke Kawo Tusar Gaba?

Mafi akasari, tusar gaba ko tusar farji ba wata cuta ko wani rashin lafiya ke kawo ta ba. Tusar gaba tana faruwa ne yayin da iskar ke taruwa a cikin farji ta fito da karfi. Duk abubuwan da ke sanya taruwar iska a cikin farji su ne ke sanya tusar gaba. Zamuyi bayanin su daya bayan daya kamar haka:

1. Zaman Mace Ba Wando

A lokacin da mace ta lazimci zama ba wando, har dai mata masu yawan yin wawan zama, iska yakan shiga cikin farjin su ya taru. Wannan iskar da ta shiga a cikin farji ita ce ke fitowa da ƙarfi da ƙara kamar tusa a lokacin da mace tayi wani dogon yunkuri musamman a lokacin da ake saduwa da ita.

2. Jima'i Ko Saduwa

Tusar gaba tafi faruwa a lokacin jima'i ko yayin da mace ke saduwa. A lokacin saduwa, idan sha'awar mace ta motsa, farjin ta yakan bude ya kara girma domin shiryawa karban azzakari. Hakan yakan kara ba iska damar shiga farjin mace a lokacin da aka fara jima'i musamman idan mace tana wani salon kwanciya kamar durƙushe ko goho. Wannan iskar shi ne yake makalewa ya taru sannan wani sa'ilin ya fito da karfi a matsayin tusar gaba.

3. Yawan Haihuwa

Yawan haihuwa yakan kara bude gaban mace, haka kuma yakan raunana tsokokin da ke da alhakin riƙe tusa da kuma sarrafa ta. Wasu mata suna fara tusar gaba ne bayan haihuwa.

4. Chusa Magungunan Mata a Cikin Farji

Chusa magungunan mata marasa asali da tsari a cikin farji, da sunan yin matsi ko wani amfani yana kawo rarakewar farji har iska ta samu damar fantamawa a cikin farjin. Kuma dayawa magungunan da mata ke amfani dasu domin matsi suna musu aiki ne kawai na wani dan ƙankanin lokaci. Daga baya in karfin maganin ya kare, sai wajen ya sake luguiguicewa kuma ya bude fiye ma da farko. Toh kinga tanan kin karawa farjin girma, iska sai ta samu damar shiga.

A kasan wannan taken, zamu kawo wasu abubuwan da mata ke chusawa a cikin farjin su domin tarye jinin al'ada. Kamar irin su audugar da ake sakawa a chan cikin farji, robar kofin jinin al'ada (menstrual cups) da dai sauransu. Idan mata zasuyi amfani da wadannan domin tarye jinin al'ada, su tabbatar da sunyi amfani da su yadda aka bada umurni daga maƙerar su domin gujewa matsala.

5. Yin Zinar Hannu ko Istimna'i

Yawan chusa yatsu, ko roba ko duk wani abun chusawa a cikin farji domin biyawa kai buƙata yana cikin manyan abubuwan da ke lalata farjin 'ya mace. Dayawan mata kan buɗe ta hanyar zurmuƙa hannu ko wasu ababe a cikin farji. Hakan yakan taimakawa iska taruwa a cikin farji kuma yasa mace ta kama tusar gaba a duk lokacin da namiji ya kusance ta.

Wadannan kaɗan kenan daga cikin manyan abubuwan da ke kawowa mata matsalar lalacewar gaba, har kaji yana ta kara yana fitar da iska kamar buddari idan ana saduwa da mace.

Maganin Tusar Gaba

Hanya ta farko wajen maganin matsalar tusar gaba ita ce kiyayewa da daina yin duk abubuwan da ke kara lalata farji da kuma bude shi, sannan a kiyaye zama ba wando.

Idan mace tana yawan tusar farji a lokacin saduwa toh ya kamata ta duba yanayin kwanciyar ta a lokacin saduwar. Tusar gaba tafi faruwa a lokacin da mace tayi goho ko botso ko kuma durƙushe yayin saduwa. Idan haka take saduwa toh sai ta koma kwanciya a gadon bayanta ta yadda zata iya sarrafa tsokokin da ke riƙe tusar ta hanyar matse kafafunta.

Haka kuma kwanciya a gadon baya tana rage yiyuwar shigar iska cikin farji a lokacin saduwa.

Akwai wani salon motsa jiki na musamman da ake kira Kegel's Exercise a likitanci. Wannan salon motsa jikin yana taimakawa mata wadanda suke bude sosai saboda yawan haihuwa ta hanyar karfafa tsokokin kunkumin su da kuma yi musu matsi. Hakan yakan kara matse musu da farjin su ya rage yiyuwar shigar iska a cikin sa.

Yadda ake yin wannan salon motsa jiki shi ne, mace za ta matse gabanta da bayanta sosai kamar yadda take matse fitsari da bahaya idan sun matse ta kamin ta kai ga shiga banɗaki. Idan ta matse jikin ta sosai anaso ta riƙe a haka kamar na minti uku (3) kamin ta saki jikin, sa'annan sai ta dan huta sai ta sake maimaitawa kamar sau goma, tana yi tana hutawa a tsakani.

Kullum anaso mace tayi wannan motsa jiki kamar sau uku. Insha Allah zata ga amfanin shi idan ta ɗore tana yi.

Kammalawa

Tusar gaba abu ce ta gama gari ga mata, amma kuma mafi yawanci ba wata cuta ce ke kawo ta ba. Mata dayawa suna fuskantar wannan tusar gaba a lokacin saduwa sakamakon budewar farji, wasu kuma sakamakon yin botso ko goho wasu kuma haka kawai suke yin tusar.

Nassoshi

1. Hui-Hsuan Lau, Tsung-Hsien Su, Ying-Yu Chen, Wen-Chu Huang, The Prevalence of Vaginal Flatus in Women with Pelvic Floor Disorders and Its Impact on Sexual Function, The Journal of Sexual Medicine, Volume 18, Issue 3, March 2021, Pages 487–492, https://doi.org/10.1016/j.jsxm.2020.12.008

2. Hedwig Neels, Xavier Mortiers, Sybrich de Graaf, Wiebren A.A. Tjalma, Stefan De Wachter, Alexandra Vermandel, Vaginal wind: A literature review, European Journal of Obstetrics & Gynecology and Reproductive Biology, Volume 214, 2017, Pages 97-103, ISSN 0301-2115,

https://doi.org/10.1016/j.ejogrb.2017.04.033.

(https://www.sciencedirect.com/science/article/pii/S0301211517302063)

Print this post

Post a Comment

0 Comments