Ad Code

Responsive Advertisement

Ticker

6/recent/ticker-posts

Bayani Akan Ciwon Dan Sanƙarau

Ciwon Sanƙarau

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya, Nimet ta lissafo wasu jihohi a ƙasar da suke cikin haɗarin barkewar cutar dan sanƙarau.

A shafinta na X, hukumar ta Nimet ta ce jihohin da suka fi haɗari galibi a yankin arewacin ƙasar ne da suka ƙunshi Sokoto, Jigawa, Yobe da Borno.

Jihohin da suma suke cikin haɗarin ɓullar cutar sun haɗa da Zamfara, Katsina, Kano, Bauchi, Gombe, Kebbi da Adamawa.

Bayanin na Nimet na zuwa ne a daidai lokacin da baya-bayan nan hukumomi a jihar Yobe suka tabbatar da ɓullar cutar ta dan sanƙarau a makarantun sakandaren mata uku, da kwalejin ƴan mata ta gwamnatin tarayya a ƙananan hukumomin Potiskum.

Cutar ta dan sankarau tayi ajalin ɗalibai 17 ƴan makarantar kwana yayin da ragowar ukun ƴan makarantar Firamare ne sai kuma wasu da dama da suke jinya a asibiti sakamakon kamuwa da cutar ta dan sanƙarau.

A cikin asibitin ƙwararru na Potiskum, an samu adadin mutum dari biyu da sha huɗu (214) da suka kamu da cutar, sannan wasu mutane uku kuma suna cikin sashen kula da lafiya na asibitin suna karɓar magani.

A bayanin Nimet, akwai jihohin da ke da sauƙin haɗarin kamuwa da cutar da suka haɗa da Kaduna da Filato da wani ɓangaren na jihar Adamawa da Neja, Kwara, Abuja, Nassarawa, Taraba, Benue da kuma Kogi.

Sai kuma sauran jihohin da ba sa cikin haɗarin kamuwa da cutar ta dan sanƙarau da suke yankin kudancin Najeriya.

A wannan gaɓar za mu duba alamomin cutar ta dan sanƙarau da kuma yadda mutum ke iya kare kansa daga ita.

Alamomin Cutar Dan Sanƙarau

Dan sanƙarau cuta ce da ke iya shafar ƙwaƙwalwa da laka. Ƙwaƙwalwa da laka suna lulluɓe da wasu fatu marar nauyi guda uku da ake kira meninges a likitance. Cutar dan sanƙarau tana shafar wadannan fatun ne.

Alamomin cutar ta dan sanƙarau na iya zama bai ɗaya sannan a wani lokaci suna iya bambanta a jikin waɗanda suka kamu da ita. Alamomin cutar sun haɗa da:

 1. Zazzaɓi
 2. Ƙagewar wuya
 3. Matsanancin ciwon kai
 4. Tashin zuciya
 5. Shiga yanayin kasa tsugune ko tsaye
 6. Fitar hayyaci
 7. Jijjigar jiki kamar farfaɗiya
 8. Rashin son haske ko rana ko fitila

Illolin da cutar Dan sanƙarau za ta iya yi wa lafiya

Akwai illolin da wannan cuta ta sankarau za ta iya yi ga lafiyar wanda ya kamu da ita. Illolin sune kamar haka:

 1. Lalata ƙwaƙwalwa baki ɗaya, wanda hakan na iya sanya mutum ya rasa ransa
 2. Suma
 3. Shanyewar ɓarin jiki ko mutuwar rabin jiki ko rashin karfin hannaye da ƙafafu
 4. Kamuwa da cutar farfaɗiya
 5. Cutar mantuwa
 6. Watsuwar ƙwayar cutar zuwa ɓangarorin jiki
 7. Kurmancewa ko makancewa ko bebancewa
 8. Taruwar ruwan ƙurji a cikin kwakwalwa

Yadda Mutum Zai Kare Kansa Daga Kamuwa Da Cutar Dan Sanƙarau

Babbar hanyar kariya daga cutar sanƙarau ita ce yin rigakafin cutar. Akwai alluran riga-kafi masu kare mutane daga kwayoyin cuta na gama gari masu kawo cutar dan sanƙarau.

Don haka akwai buƙatar hukumomi su samar da isassun alluran a kan lokaci, yadda mutanen da ke buƙata za su samu.

Haka kuma ya kamata mutane su je su yi rigakafi da su da ƴaƴansu domin samun kariya ba sai lokacin da aka samu ɓarkewar cutar dan sanƙarau ba.

Bugu da ƙari, tabbatar da tsaftar jiki yana da matuƙar amfani wajen bada kariya ga cutar dan sanƙarau - yawan wanke hannu da kuma kiyayewa wajen yin attishawa da tari da hamma a kusa da wasu saboda galibi cutar na yaɗuwa ne ta hanyar shaƙar gurɓataccen iska. 

Yawan sanya takunkumi musamman ga mutanen da ke cikin jahohin da suka fi haɗarin kamuwa da cutar dan sanƙarau yana rage hadarin mutum na kamuwa da cutar yayin da ta ɓarke.

Har wayau, matakan kariya daga cutar sanƙarau ba zasu cika ba, sai anyi magana kan rage cinkoso. Idan ana buƙatar kariya daga cutar dan sanƙarau dole a rage cinkoso da yawan a makarantun kwana da sansanonin gudun hijra inda ake da mutane da dama da ke zaune a wuri daya lokaci guda.

Print this post

Post a Comment

0 Comments