Gabatarwa:
Hanta wata gaba ce mai girma a cikin kayan ciki, ita ce kayan ciki mafi girma da ƙarfi a cikin jikin dan Adam. Hanta tana zaune a ƙarƙashin kejin haƙarƙari a gefen dama na ciki. Hanta tana da mahimmanci a wajen narkar da abinci da kuma kawar da abubuwa masu daci ko guba domin hana su yiwa jiki karan tsaye.
Ana iya gadon ciwon hanta (genetic). Hakanan kuma ana samun cutar hanta ta hanyar abubuwa da yawa waɗanda ke lalata hanta, kamar kamuwa da wasu ƙwayoyin cuta, shan barasa, shan sigari, mummunan kiba da dai sauransu.
A lokacin da wadannan abubuwa masu lalata hanta suka dauki tsawon lokaci a jikin dan Adam ba tare da wuta kulawa daga marar lafiya ba sukan haifar da tabo a jikin hanta, yanayin da ake kira da cirrhosis kenan a turance. YaÉ—uwar wannan tabo da kuma mamaye hanta zai iya haifar da gazawar hanta. Gazawar hanta yanayi ne mai haÉ—arin gaske ga rayuwar dan Adam.
Mene ne Ciwon Hanta?
Ciwon hanta shine duk wani gazawar aikin hanta wanda zai haifar da rashin lafiya. Hanta tana da alhakin yin ayyuka masu mahimmanci da yawa a cikin jiki kuma idan ta kamu da cuta ko ta ji rauni, asarar waÉ—annan ayyukan na iya haifar da babbar illa ga jiki.
Ciwon hanta kalma ce mai fadi wacce ke tattare da dukkan matsalolin da ke iya aukuwa idan hanta ta kasa yin ayyukan da ta saba a jikin mutum. Mafi akasari, sai fiye da 75% ko kashi uku na naman hanta ya lalace kafin raguwar aikin hanta ya fara bayyana, sannan alamomin ciwon hanta suma su fara bayyana.
Amfanin Hanta a Jikin dan Adam
1. A matsayin wani ɓangare na aikinta, hanta tana samar da wani sinadari da ake kira bile ko kuma bile acid. Bile wani ruwa ne wanda ya ƙunshi wasu sinadarai da ke taimakawa wajen narkar da abinci mai ɗauke da kitse ko maiƙo.
2. Adana sinadarin glucose ko sukari a matsayin sinadarin glycogen, sannan ta mayar da shi zuwa glucose lokacin da jiki ke buƙatarsa don kuzari.
3. Samar da abubuwa da sinadarai masu tsayar da zubar jini a yayin da mutum yaji rauni.
4. Samar da sinadarin amino acid (tubalan ginin sinadarin furotin), gami da samar da sinadaran furotin din da jiki ke amfani da su don yaƙi da kamuwa da ƙwayoyin cuta.
5. Sarrafawa da adana sinadarin bakin karfe (iron) da ake buƙata domin samar da halittun jini jajaye.
6. Samar da sinadarin cholesterol da sauran sinadarai da ake buƙata don jigilar man kitse a cikin jini.
7. Narkar da ko wane irin abinci mutum yaci da kuma tace sinadaran abinci masu amfani zuwa cikin jini.
8. Sarrafa abincin da aka ci marar amfani zuwa shara wadda za'a iya fitarwa a cikin fitsari ko bahaya.
9. Sarrafa magunguna da kuma guba zuwa shara.
Abubuwan da ke kawo ciwon hanta
1. Shan giya ko kuma barasa
2. Kamuwa da ƙwayoyin cuta
Kamuwa da ƙwayoyin cuta masu lalata hanta shi ne abu na farko da yafi kawo ciwon hanta a kasashe masu tasowa kamar Nigeria. Ƙwayoyin cutar da ke kawo ciwon hanta sun hada da;
- Ƙwayoyin cutar virus na Hepatitis A
- Ƙwayoyin cutar virus na Hepatitis B
- Kwayoyin cutar virus na Hepatitis C
- Kwayoyin cutar virus na Hepatitis D
- Ƙwayoyin cutar virus na Hepatitis E
- Kwayoyin cutar virus na Epstein Barr
- Ƙwayar cutar Fasciola hepatica
3. Shan magungunan barkatai
- Dukkan magungunan gargajiya
- Paracetamol
- Isoniazid
- Tetracycline
- Nitrofurantoin
- Da dai sauransu
- Gilbert's disease
- Wilson's disease
- Non-alcoholic steatohepatitis (NASH)
- Autoimmune hepatitis
- Hemochromatosis
- Da dai sauransu.
5. Ciwon daji
6. Gado
Ana gadon ciwon hanta, kamar yadda muka yi bayani a baya.
0 Comments