Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda zaku kare yaranku daga kamuwa da cutuka bayan komawa makaranta

 Gabatarwa 

Yayin da yara ke komawa makaranta a faɗin ƙasar Najeriya bayan hutun ƙarshen zango da ƙarshen shekara ya ƙare, yana da kyau iyaye da malamai da kuma hukumar makarantu su kula kuma su yi taka-tsantsan da lafiyar ɗalibai musamman idan aka yi la'akari da cewa yanzu muna cikin lokacin da cututtuka suka fi saurin yaduwa a tsakanin al'umma.

A irin wannan lokaci na hunturu ana samun canjin yanayi inda ake samun sanyi da kuma ƙaruwar kaɗawar iska.

School children 

Dalilin haka ne yake sa mutane su kan yi fama da rashin lafiya a irin wannan yanayi, musamman ma ƙananan yara.[¹]

A halin yanzu da iska ke kaɗawa, cututtukan da ke yaɗuwa ta hanyar iska kan yaɗu sannan su bazu tsakanin al'umma.

Hakan ne yasa muka zage damtse domin kawo muku hanyoyi da kuma matakan da ya kamata iyaye da malamai su ɗauka domin kare lafiyar ƴan makaranta daga kamuwa da waɗannan cututtuka da kuma kasancewar kowa da kowa a cikin ƙoshin lafiya.[¹]

Cututtukan da suka fi saurin yaɗuwa a tsakanin yara 'yan makaranta 

Dakta Lawal Attahiru, wani babban likita ne da ya kware a fannin yara, ya ce cututtukan da suka fi yaɗuwa tsakanin yara ƴan makaranta su ne wadanda iska ke yaɗawa da kuma waɗanda ke yaɗuwa ta hanyar cuɗanya.

Wadannan cututtukan su ne kamar haka:[²]

  • Mura
  • Tari
  • Ciwon ido
  • Amai da gudawa
  • Cutuka da ƙurajen fata

Yadda za a kare yara daga kamuwa da cututtuka

Wajibi ne ɓangarori biyu da ke da hannu wajen ilimin yaran su ɗauki matakai domin hana yaɗuwar cutukan. Wato akwai rawar da iyaye za su taka, sannan akwai rawar da hukumomin makarantu za su taka.

Matakan da ya kamata iyayen yara su dauka

Tabbatar da yaro ya samu duka alluran riga-kafi kafin ya fara makaranta

Alluran riga-kafi suna kare yara daga kamuwa da mafi akasarin cutukan da ke yaɗuwa a tsakanin yara. Saboda haka ya wajaba ga iyaye su tabbata yaransu duka sun sami alluran riga-kafin da ake yi baki daya. Tabbatar da yaro ya samu ingantattun alluran riga-kafi kafin sanya shi a makaranta yakan haɓakar ƙwazonsa na neman ilimi da kuma hanashi kamuwa da cutuka da zasu hana shi zuwa makaranta a wani sa'ilin.

Kula da tsaftar yara

Kulawa da tsaftar jiki na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da kesa mutum dan Adam zama cikin koshin lafiya. Ya kamata kowane yaro ayi masa wanka akalla sau biyu, kamin yazo makaranta da kuma daga komawarsa gida bayan ya tashi daga makaranta. Haka kuma yana da kyau kullum a wankewa yaro tufafinsa  na zuwa makaranta.

Saurin zuwa ɗaukar yara daga zarar an tashi makaranta

Rashin saurin zuwa ɗaukar yara shi ke sa yaranka a makaranta su cakuda da sauran yan makaranta a yayin da suke jira. A lokacin irin wannan cakuda da kuma wasanni da akeyi yaro zai iya daukar wani cuta.[¹][²]

Saurin zuwa ɗaukar yara na rage yawaitar cudanyar sa da sauran abokansa da zasu iya yaɗa masa wasu cutuka.

Ba yaro abinci mai gina jiki

Cin abinci mai gina jiki yana karfafa garkuwar jikin yaro da kuma kara masa karfi wajen fada da cututtuka.

Matakan da ya kamata makaranta ta ɗauka

Samar da wurin wanke hannu

Ya kamata makarantu su samar da wuraren wanke hannu ga yara, ta yadda za su wanke hannuwansu lokaci-lokaci domin gudun kamuwa da cututtuka. Haka kuma, yana da kyau a ba kowane yaro man wanke hannu ma ɗauke da sinadarin kashe cututtuka domin wanke hannu akai-akai, ko kuma duk bayan amfani da wani tsohon abu.[¹][²]

Tabbatar da yara na wanke hannuwansu

Wajibi ne makarantun yara su tabbatar da dokar wanke hannu tsakanin ɗalibai a makaranta.

A tabbatar ɗalibai suna wanke hannu bayan sun yi wasa da kafin su ci abinci da kuma bayan sun ci abinci.

Tsaftace muhallin makaranta

Ya kamata hukumar makaranta ta tabbatar da tsaftace ajujuwan yara da harabar makaranta domin guje wa yaɗuwar ƙwayoyin cuta cikin sauki.[¹]

Barin shara birjik a makaranta zai gayyato dabbobi da miyagun ƙwari kamar ɓera da ƙudaje masu yaɗa cututtuka zuwa cikin ajujuwa da harabar makaranta.

Hana malamai marasa lafiya mu'amala da yara

Bai kamata a bar malamin da ke nuna alamar wata cuta mai yaɗuwa kamar mura ko tari ya koyar ko kuma ya kula da ɗalibai ba.

Idan ya kasance ma'aikaci ko malami ya zo makaranta ba shi da lafiya, yana nuna alamun mura ko tari ko wata cuta sai a ba shi sarari ya yi nesa da jama'a ko kuma ya zauna a gida ya killace kansa har sai ya warke. Ta haka sai ya kasance an kare yaɗuwar cutar a tsakaninsa da sauran jama'a.[²]

Ma'aikaci ko malamin da ya zama dole ya je makaranta akan wata lalura kuma yana fama da mura sai ya yi amfani da takunkumin kariya tare da yin nesa-nesa da ɗalibai da sauran ma'aikata.

Hana yara marasa lafiya zuwa makaranta

Yana da kyau makarantu su kafa doka tare da tabbatar da cewa ana amfani da ita wajen hana yara da ke fama da rashin lafiya zuwa makaranta domin kare yaɗa cuta zuwa ga sauran yara.[²]

Kammalawa

A wannan lokaci na hunturu akwai bukatar hukumomin makaranta da kuma iyayen yara su hada ƙarfi da karfe domin daƙushe yaɗuwar cututtuka a tsakanin dalibai a makaranta. Musamman ma cututtuka masu yaɗuwa ta hanyar shaƙar gurɓataccen iska.

Zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 

Nassoshi


Print this post

Post a Comment

0 Comments