Gabatarwa
A al’ada, mata da dama musamman budurwai na nuna damuwa game da yadda girman nononsu yake. Wasu na ganin nononsu Æ™anana ne fiye da yadda suka ke so. Wannan dalili ne ya sa tambaya kamar “ maganin girman nono na budurwa ko ta yaya zan Æ™ara girman nono na” ke yawan bayyana a shafukan bincike na Google da sauran kafafen sada zumunta.
GargaÉ—i: Wannan rubutu anyi shi ne kawai saboda ilmantar wa da kuma inganta kyakkyawar zamantakewa da mu'amala tsakanin ma'aurata, duk wanda yayi ma rubutun wata mummunar fahimta, ko ya bashi wata mummunar ma'ana ko yayi amfani dashi ta hanyar da bata dace ba, toh ya ha'inci marubucin.
A wannan rubutu, za mu tattauna abubuwa kamar haka:
- Abubuwan da ke shafar girman nono
- Magungunan gargajiya da na zamani da ake amfani da su wajen kara girman nono
- Abinci da motsa jiki masu ƙarfafa girman nono
- Hanyoyin da ya kamata ki guje musu
- Shawarwarin lafiya da ya kamata ki kiyaye
Me ke Tabbatar da Girman Nono?
Kafin mu tafi ga magani, yana da mahimmanci mu fahimci cewa girman nono yana da nasaba da abubuwa kamar haka:
Kwayoyin halitta (Genetics)
Idan mahaifiyarki ko 'yan uwanki mata suna da nono masu girma ko ƙanƙanta, akwai yuwuwar hakan zai shafe ki kema.
Sinadaran Hormones
Musamman hormone na estrogen da prolactin suna taka muhimmiyar rawa.
Kiba da nauyin jiki
Yawan kitse a jiki yana ƙara girman nono, saboda tarin kitse a cikin nono shi ke saka shi ya fito yayi laushi
Shekaru
Budurwa na girma tana kara samun sauyin jiki yayin balaga, wanda ke shafar girman nono. Haka kuma idan shekarun mace suka jaa, to girman nono ya kan fara lalacewa ya ƙanƙanta
Maganin Kara Girman Nono na Gargajiya
A ƙasashen Hausa, akwai hanyoyi da dama na gargajiya da mata ke amfani da su domin ƙara girman nono. Ga wasu da aka fi sani:
1. Man Hulba
Ana amfani da man hulba don girman nono, hulba tana ɗauke da sinadaran da ke ƙara yawan hormone na estrogen a jiki. Ana shafawa nono bayan an dumama man, a yi ta tausa a hankali.
2. Ganyen Tafasa (Fenugreek)
Ana yin tea daga ganyen tafasa, ana sha sau É—aya ko biyu a rana domin kara girman nono.
3. Man Zaitun
Man zaitun yana taimakawa wajen ɗaga fatar nono da kuma kara masa laushi. Ana iya haɗa shi da man kwakwa domin ƙara tasirin aikin sa.
4. Tausa da kayan ƙamshi
Ana amfani da tausa don ƙara girman nono, saboda tausa da kayan ƙamshi irin su lavender, rosemary da lemon oil na taimakawa wajen motsa jini a nono.
5. Gyaran Jiki da Nono ta Hanyar Amfani da Dabino
Ana shan dabino da madara ko zuma domin ƙara sinadaran hormones a jiki.
Hanyoyin Gyara Tsayuwar Nono Budurwa
A taƙaice za mu faɗi hanyoyi guda uku da ke maganin zubewar nono ko miƙar da nono ya tsaya chak ba tare da shan wahala ko kashe kuɗi ba;
1. Ƙanƙara
A samu ƙanƙara a shafa a jikin nono duka biyun, a shafa a hankali har sanyin ya game ko'ina na jikin nonuwanki har na tsawon kamar minti biyu, za'a maimaita hakan na tsawon wasu kwanaki.
Ƙanƙara yana da tasiri sosai wajen matse nono da hana shi zubewa, amma kada yawuce minti uku ana shafawa, kuma smoothly za a dinga shafawa daga bisani idan an kin kare shafawa sai ki dauki bra wadda take maki daidai ki sanya.
2. Man Zaitun
Dayawa yan'uwa mata suna da kokarin ajiye man zaitun amma suna neman maganin zubewar nono a wani wuri, to wallahi yar uwa kin bar magani mai mahimmanci sosai a gefe.
Domin maganin zubewar nono anaso ki shafe nononki da man zaitun kullum safe da yamma ki shafa a hankali sannan a take bayan kin kammala shafawa ki saka bra wanda ya dace dake. Za'a maimaita haka na wasu kwanaki, kuma za'a iya amfani da zaitu lawz ko jojoba oil a madadin man zaitun din.
3. Neem Oil
Za'a iya haÉ—a neem oil tare da garin ruman cokali É—aya a garwaya wannan haÉ—in sai a É—aura a kan garwashi ya É—an yi zafi kaÉ—an sai a sauke a bar shi ya huce, daga nan sai a dinga shafawa nono sau biyu a wuni, na wasu kwanaki kaÉ—an. Wannan hadin yanada tasiri sosai.
Maganin Kara Girman Nono na Zamani
Wasu mata na amfani da breast enlargement pills, cream don ƙara nono, wasu kuma capsules da supplements da ake sayarwa a shaguna ko kasuwa ko online a yanar gizo. Duk da yake wasu daga ciki na aiki, yana da kyau ki nemi shawarar likita kafin ki fara amfani da su. Ga wasu misalan magungunan da ake yawan amfani dasu:
- Breast enhancement cream
- Herbal breast enlargement capsules
- Pueraria mirifica supplements
Abinci Masu Amfani don Kara Girman Nono
Abinci na da matuƙar tasiri wajen bunkasa kwayoyin jiki da hormones. Ga jerin abinci masu taimako wajen kara girman nonon mace:
1. Madara da Dabino
Dabino na da sinadaran da ke motsa jiki, madara na ƙarfafa girma. Hade su tare yana haifar da sakamako mai kyau wajen bunkasa nonon mace.
2. Kwakwa da Man Kwakwa
Ana ci da shafawa – yana Æ™ara kitse a jiki da nono.
3. Gyada da Wake
Gyada da wake na da sinadaran protein da estrogen wanda ke taimakawa wajen haɓaka nonon mace.
4. Kifi da Kaza
Suna ƙara kitse mai kyau a jiki, musamman kitsen da ke taruwa a cikin nono.
5. Kayan Lambu
Fruits kamar Avocado, Apple da Abarba, suna taimakawa wajen cika nono da tarin lafiyayyen kitse a nono.
Motsa Jiki da ke Ƙara Girman Nono
Kodayake nono ba tsoka bane, motsa jiki na iya ƙara masa ɗan girma da ƙyalli, kuma motsa jiki yana karfafa tsokokin ƙirjin mace wadanda nono yake kwance a kai. Ga wasu motsa jiki da za su taimaka don girman nono:
1. Push-ups - Wannan kalar motsa jiki yana ƙarfafa tsokar kirji wanda ke daga nono ya tsaya.
2. Chest Press da Dumbbells - Ana yin wannan kalar motsa jiki sau 3 a mako domin ƙarfafa kirji da tsokokin da ke rike nono.
3. Wall Press - Mai sauƙi kuma yana amfani musamman ga masu buƙatar sauƙin motsa jiki.
4. Arm Circles - Wannan kalar motsa jiki na taimakawa wajen motsa jini da kuma É—aga siffar nono.
Yadda ake Maganin Girman Nono Budurwa da Shammar (Fennel)
1. Ta hanyar shan garin Shammar (Fennel):- Mace ta samu garin maganin Shammar mai kyau ta riƙa ɗiba cokali ɗaya tana zubawa a cikin ruwan ɗumi kofi ɗaya, sannan ta dinga sha safe da yamma.
2. Shafa man Hulba: Ana so mace ta samu man Hulba da man Gelo (Castor Oil), ta haÉ—a su a waje É—aya, sai ta garwaya. Sai ta dinga shafawa a dukan nono gaba É—aya sau biyu a rana.
3. Sanya rigar nono wadda tayi daidai: Anaso rigar nono ko bra da mace za ta dinga amfani da ita kada ta matse ta sosai, kuma kada ta yi yawa.
In sha Allah, idan aka bi wadannan hanyoyin na tsawon wata ɗaya, za'a ga canji ba tare da wahala ko kashe kuɗi mai yawa ba. Idan kin samu biyan buƙata nonon ki ya cika yadda kike so, toh ki dakata da amfani da maganin don kada girman nonon ya wuce misali har ya zube.
Ana samun wadannan magunguna duka a wajen masu sayar da magungunan Musulunci (Islamic Medicine Stores). Maganin Shammar na asali yana da ƙamshi kamar turare, idan aka baki wanda baya ƙamshi, toh ba na asali bane.
Abubuwan Da Ya Kamata Ki Gujewa Idan Kina Bukatar Girman Nono
- Amfani da magungunan da ba su da rijista da NAFDAC
- Shan magani ba tare da shawarar likita ba
- Sake fasalin nono ta tiyata (surgery) ba tare da cikakken bincike ba
Shawarwari Kula da Nono Masu Amfani
1. Ki kasance mai haÆ™uri – girman nono ba ya canzawa cikin dare daya.
2. Ki zaÉ“i hanya mai lafiya – kada ki É—ora kanki a haÉ—ari don neman Æ™ara girma.
3. Ki guji kwatanta kanki da wasu – jikin kowace mace daban yake.
4. Ki kula da lafiyar jikinki gaba É—aya – nono É“angare ne kawai na jikin ki.
Tambayoyi da Amsoshi (FAQs)
1. Nonona ƙanana ne, shin zai iya girma da lokaci?
Eh, musamman idan kina matakin balaga, akwai yuwuwar ya ƙara girma da lokaci.
2. Wane lokaci zan ga canji bayan amfani da man hulba?
Yawanci bayan sati 3 zuwa 6 ana iya fara ganin sauyi idan ana amfani da shi akai-akai.
3. Shin motsa jiki yana taimaka wa girman nono?
Kwarai, yana ƙara ƙyalli da cika siffar nono.
4. Wane abinci ne ya fi tasiri wajen girman nono?
Dabino da madara, avocado, gyada da wake na da matuƙar tasiri.
5. Shin ana iya haÉ—a magungunan gargajiya da na zamani?
Ba a bada shawarar hakan ba sai da izinin likita.
Kammalawa
Girman nono abu ne da ke damun budurwai da dama, amma yana da mahimmanci a fahimci cewa komai yana tafiya ne da lokaci da jikin mutum. Ki zaɓi hanya mai lafiya da tasiri, ki guji saurin sakamako da zai iya janyo matsala ga lafiyarki.
Ki kasance da ƙaunar kanki yadda kike, domin kyawunki na gaske ba a girman nono yake ba, a yadda kike ji da kanki ne.
Rubutu Masu Alaƙa
1. Yadda Mace Zata Dinga Yin Jarrabawa Ko Gwajin Nono A Gida Da Kanta
2. Maganin Kara Girman Nono Da Man Shafawa Na Gyaran Nono: Hanyoyin Gyaran Nono A Likitanci
3. Maganin Girman Nono Na Budurwa Idan ÆŠaya Yafi ÆŠaya Girma