Yadda Mace Zata Dinga Yin Jarrabawa Ko Gwajin Nono A Gida Da Kanta

Yadda ake taba nonon mace

Yin jarrabawar ko gwajin nono a gida yana taimakawa mata wajen gano canje-canjen da ke faruwa a nonon su a cikin lokaci, domin su tattauna su da likita ko mai ba da kiwon lafiya a kan lokaci. Jarabawar ko gwajin nono na yau da kullum na taimakawa mace kula da lafiyar nonon ta da gano cutar kansar nono da wuri domin fara magani a lokacin da za'a iya warkar da mace daga cutar. 

Yawancin kullutun da ke fitowa mata a cikin nono da ma wasu canje-canje da ke faruwa ga nonon mace ba ciwon kansa ba ne, amma duk da haka ana buƙatar mace ta kawowa likita ƙorafin duk wani sabon canji da ta samu a nonuwan ta.

Mene ne Jarrabawar Nono?

Jarrabawar nono hanya ce mai mataki-mataki da mata za su iya amfani da ita da kansu a gida don bincike akan nonon su. Wannan jarrabawar nono ta ƙunshi kallon nono a madubin dubawa, taɓa nonon mace duk lungu da sako da shafa dukkan nonon, matsa kan nono domin dubawa ko yana fitar da ruwa da kuma binciken ƙullutu ko ƙololo a hamattan mace.

Ta hanyar kallo da taba nonon mace akai-akai, mata za su iya lura da canje-canje a nonon su ko gane lokacin da wani abu ya bambanta ga nonon su, ko aukuwar wani sabon abu ga nonon.

Yawancin masu ba da kiwon lafiya sun yarda cewa yayin da gwajin mammogram shi ne mafi kyawun gwaji wajen aikin tantancewa don gano sauye-sauyen da ke faruwa a cutar kansar nono, gwajin nono ko jarrabawar nono da mata za su iya yi a gida ita ce hanya mafi kyau don sanin waÉ—annan canje-canjen nono da wuri.

Yadda Mace Zata yi Jarrabawar Nono a Gida

Jarrabawar nono tana da matakai da ake bi É—aya bayan É—aya domin mace ta gudanar da ingantaccen bincike ga nonon ta da kanta a gida ba tare da ganin likita ba.

1. Matakin Duba Nono A Madubi 

A wannan mataki ana so mace ta tsaya tsaye ko a zaune a gaban babban madubin da zata iya ganin dukkan Æ™irjin ta, sannan ta cire rigar ta da kuma rigar nono ko underwear domin bayyanar da nonon ta da kuma dukkan Æ™irjin ta a fili. 

Yadda ake duba nonon mace


Daga nan mace za ta fuskanci madubin domin la'akari da waÉ—annan abubuwan É—aya bayan É—aya:

  • Duba girman nonon ta da siffar su da kuma la'akari ko akwai banbancin girma ko siffa a tsakanin nonon mace guda biyu.
  • Duba kan nonon mace da la'akari da ko kan nono ya shige daga ciki, ko ya lanÆ™wshe ko canja kamanni.
  • Duba fatar nono da la'akari da canjin fata kuraje, tamuÆ™a ko squeezing na fatar nono.
  • Mace ta É—ora hannayen ta a kan kumkumi tare da danna kumkumin sosoi, wannan zai kara ba nonon mace damar fitowa a fili domin la'akari da waÉ—annan abubuwan da muka ambata a sama.


  • Mace ta daga hannayen ta sama gaba É—aya sannan ta kara duba nonon ta guda biyu tare da la'akari da abubuwan da ake so a duba.


  • Mace ta sa hannu ta É—aga kowane nonon ta domin duba Æ™asan nono tare da la'akari da ko akwai, kuraje, canje-canje ko banbanci tsakanin layin Æ™asan nonuwan ta guda biyu.

2. Matakin Taba Nonon Mace Da Hannu

A wannan mataki zamu yi bayanin yadda ake taba nonon mace a lokacin jarrabawar nono, wannan mataki yakan biyo bayan kammala matakin farko, ana bukatar mace ta kwanta a kan gado rairam a kan gadon bayan ta, wannan zai ba nonon mace damar shimfiÉ—ar da kansa akan Æ™irjin ta, idan mace tayi a tsaye babu laifi, amma dai yi a kwance yafi. 

Yadda ake taba nonon budurwa

Ana so mace ta fara taba nonon ta da tafin yatsu uku na tsakiya domin jin duk ilahirin nonon da kuma la'akari da wani kumburi, ƙololo, ƙullutu ko wane canje-canje a cikin nono. Mace zata ɗage hannun ta na dama zuwa saman kanta a lokacin da take taba nonon ta na dama, haka kuma zata ɗage hannun ta na hagu sama a lokacin da take taba nonon ta na hagu.

Hoton yadda aka taba nonon mace


Ana amfani da yatsun hannun dama domin taba nonon mace na hagu, sannan ayi amfani da yatsun hannun hagu domin taba nonon mace na dama. Bugu da kari, ana so mace ta fara da shafa nonon sannu-sannu (light pressure) kamin ta fara taba nonon sosai (medium pressure), daga bisani sai ta danna yatsun cikin nonon sosai (high pressure) domin jin kowane lungu da sako na nonon. Ana so mace ta yiwa kowane nonon ta haka É—aya bayan É—aya.

Bayan kammala shafawa da taba nonon ana bukatar mace ta matsa kan kowane nono domin ta gani ko nonon ta yana fitar da ruwa ko madara ko ma jini idan an matsa. 

Hoton yadda aka matsa nonon mace


Domin karin bayani, duba wannan rubutun "Fitar Ruwan Nonon Mace Ba Tare Da Ciki Ko Shayarwa Ba (Galactorrhea)"

Daga karshe mace za ta kammala taba nonon ta da taba cikin hamatta. Ana so mace ta saka tafin yatsu a cikin kowane hamatta kamar yadda muka yi bayani a baya, ta taba kowane lungu da sakon hamattan, tare da la'akari ko akwai wani kumburi, ƙullutu ko wani ƙololo a cikin hamatta.

Duba hamattan mace


Idan ana jarrabawar nono, ko a gida ko a asibiti binciken hamatta dole ne, saboda akwai wani sashen nonon mace da ya shiga cikin hamatta, haka kuma mafi yawancin ciwon dajin nono ko kansar mama tana haifar da ƙollutai do ƙololo a cikin hamatta.

Yaushe Ake So Mace Tayi Jarrabawar Nono?

Ana so kowace mace da ta balaga, budurwa ko matar aure, mai shayarwa ko wadda bata shayarwa ta dinga yin jarrabawar nono a Æ™alla sau 1 a duk wata. 

Toh wane lokaci ne aka fi so ayi jarrabawar nono a gida? Masana sun so ayi jarrabawar nono a lokacin da nonon mace yake da baya mata ciwo idan an taba.

Wannan dalili ne yasa masana suna bada shawarar kauracewa jarrabawar nono a lokacin da mace ke daf da ganin jinin al'ada, saboda a wannan lokacin nonuwan mace suna dan tsami su dinga yi mata zugi da ciwo watarana har sai jinin al'ada ya dauke. Domin ƙarin bayani, duba amsar wannan tambaya "Me Ke Kawo Ciwon Nono A Lokacin Jinin Al'ada (Period)?"

Saboda haka, lokaci mafi kyau da ya kamata mace ta dinga yin jarrabawar nonon ta shi ne, bayan sati ɗaya da daukewar jinin al'adar ta. A wannan lokaci za ta fi sakin jiki ta taba nonon lungu da sako saboda ƙaranci zafi ko tsamin nono.

Kammalawa

Jarrabawar nonon ta kunshi duba da kuma taba nonon mace da kanta akai-akai domin gane lafiyar nono da kuma fahimtar canje-canjen da ke faruwa ga nonon mace a cikin lokaci. Wannan hanya ce da masana ke bada shawarar aikatawa domin gane ciwon dajin nono da kuma sauran cututtukan nono da wuri.

Domin cimma wannan makasudi dole mace ta kawowa likita ƙorafin duk wani sabon abu, canji ko wani shakka da ta samu a lokacin jarrabawar nonon ta a gida.

Rubutu Masu Alaqa 

1. Fitar Ruwan Nonon Mace Ba Tare Da Ciki Ko Shayarwa Ba (Galactorrhea)

2. Me Ke Kawo Ciwon Nono A Lokacin Jinin Al'ada (Period)?

3. Bayani Game Da Tsiro, Kololo, Kumburi Ko Karin Girman Nonon Mace

4. Zubar Ruwan Nono Ga Budurwa Wanda Bayada Alaqa Da Shan Nono Ko Shayarwa - Galactorrhoea 

5. Bayani Game Da Cututtukan Nono