Assalamualaikum warahamatullah Dr Allah ya Saka da alkhairi ya biya ku da alkhairi.
Dan Allah me yake kawo mace taji Wani qululu a breast dinta?Kuma me zata Sha ya baje,Amma baya ciwo.
Amsa
Jin ƙololo ko tsiro ko wani ƙurji a cikin nonon mace abu ne mai buƙatar kulawa ta gaggawa, saboda akwai bukatar tabbatar da wannan ƙololon ba ƙololon ciwon kansa bane.
Mafi yawancin ƙololon da ke fitowa yara ƙanana da ke kasa da shekaru 30 bai cika zama sanadiyyar ciwon kansa ba, yana fitowa ne mostly dalilin fibroadenoma, wanda da an yi aiki an cire shikenan ba matsala.
Amma jin ƙololo a cikin nonon mace a karon farko bayan ta kai shekaru 45 yana iya nuni zuwa ga ciwon kansar nono. Sauran alamomin ciwon kansar nono sun haɗa da; ƙurjin nono, tamuƙewa ko squeezing na fatar nono, ƙololo a cikin hamata, zubar ruwa mai jini-jini daga nono da kuma rama maras dalili.
Idan ƙololo ya fito a nono, babu ingantaccen magani da ake badawa domin ya baje ko ya rage masa girma. Anayin aikin tiyata ne a cire, sannana aika ƙololon a dakin gwaji domin gane kansa ne ko akasin haka.
Kumburi, Karin Girman Nono Ko Ciccikowarsa
Nonon mace yana iya ciccikowa ya kumbura, har ya rika yin ciwo ko kuma fitar da ruwan nono ko da kuwa ba tana dauke da ciki ba, ba tana shayarwa ba, ba lokacin al'adarta ba, ba lokacin saka kwan haihuwar ta ba, ko lokacin yaye ba. Ga wasu dalilai da suke iya haifar da hakan:
1. Rashin Daidaiton Zubar Ruwan Sinadarai (Hormonal Imbalance)
Canje-canjen zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone a cikin jikin ta yana iya sanya nonon ta ya cicciko. Matsalolin rashin lafiya kamar Polycystic Ovary Syndrome (PCOS) ko ciwon jakar sinadarin thyroid (thyroid gland disorders) suna iya haifar da wannan yanayin.
2. Laulayin Amfani Da Wasu Magunguna (Medication Side Effects)
Wasu magungunan da mata suke yin amfani dasu, kamar magungunan tazarar haihuwa (hormonal contraceptives) ko magungunan da suke haɓaka yawan sinadaran da mace take da karancinsu (hormone replacement therapy), ko magungunan ciwon ƙwaƙwalwa (antipsychotics), ko magungunan ciwon damuwa (antidepressants), ko magungunan ciwon cancer (chemotherapy drugs), duk suna iya haifar da karin girman nono da zubar ruwan nono.
3. Kumburin Nono Saboda Shigar Kwayoyin Cuta (Mastitis)
A wasu lokuta, karin girman nono ko kumburin nono yana iya zamowa sakamakon shigar kwayoyin cuta a cikin nono ne (mastitis) koda ba lokacin shayarwa ba.
4. Kullutun Nono (Cysts or Fibrocystic Lumps)
Kullutu zai iya fitowa mace a cikin nononta, sa'annan ya kumbura, ya haifar mata da taruwar ruwa da ciccikowar nono, ko rashin jin dadi a nonon kamar yadda bayani ya gabata.
5. Shiga Cikin Yanayin Tashin Hankali Ko Tsananin Rashin Hutu (Stress)
Babbar damuwa ko rashin hutu suna iya shafar tsarin sinadaran estrogen da progesterone a cikin jikin mace, kuma hakan zai iya haifar da ciccikowar nono ko zubar ruwan nono.
6. Bugewa Ko Samun Rauni A Nono (Breast Physical Trauma Or Injury)
Idan mace ta sami rauni a nono ko yankin kirjinta, hakan yana iya haifar mata da ciccikowar nono ko zubar ruwan nono.
Idan karin girman nono ko ciccikowar sa ko zubar ruwan nono ya dade, ko ya hadu da jin ciwo mai tsanani, ko wasu alamomi wadanda bata saba gani ba, to, ya kamata mace taje asibiti domin ayi bincike a tabbatar da abinda yake faruwa da ita.
0 Comments