*Assalamu Alaikum tareda Fatar Antashi Lpy Doctors.*
Don Allah Miye Maganin Salmonella typhi (Typhoid)
Sannan Don Allah idan ba'ayi Saurin ganotaba Tsawon Lokaci Sai Daga Baya shin Tana iya taba Lafiyar Lungs (Huhu) ko koh ya!
Sannan Dr. Mikesa Mutum na Warin kashi da Farin halshe idan yadda de da ita karfin akula kasan cewar anjima ana treatment na Ulcer Lokaci mai Tsawo .
Amsa
Typhoid infection ko kuma cutar typhoid, cuta ce ta ƙaramin hanji wadda kwayar cutar salmonella ke kawowa. Ana samun cutar typhoid ne ta hanyar shan gurbataccen ruwan da suke dauke da wannan ƙwayar bakteriya.
Cutar typhoid bata da alaƙa da huhu, tana kama hanji ne ko kuma ta yadu cikin jini, haka kuma idan ta dade ba magani tana iya hude hanji, musamman hanjin yara. Har ila yau babu wata ingantacciyar majiya da ta ruwaito typhoid na kama huhu.
Manyan alamomin cutar typhoid sun hada da;
1. Zazzabi
2. Ciwon kai mai tsanani
3. Ciwon ciki
4. Gudawa
5. Amai da dai sauransu
Ana maganin cutar typhoid ne ta hanyar shan magungunan antibiotics dangin, antibiotics din da suka fi kokari wajen kashe cutar typhoid sune dangin fluoroquinolones da kuma cephalosporins.
Tambaya ta biyu maganar warin ƙashi, ba wani abin da ake kira da warin ƙashi sai dai warin ƙazanta. Dalili kuwa shi ne, wasu mutane sunfi wasu saurin yin zufa, haka kuma zufar wasu mutane tafi tafi ta wasu maiƙo sakamakon yawan sinadarin sebum da fatar su ke samarwa. Wannan shi yasa wasu mutane sunfi wasu saurin yin warin jiki saboda bakteriya da ke fatar jikinsu tana yawan amfani da sinadarin sebum da zufan jikinsu domin samar da wari.
Irin wadannan mutanen ne ya zama dole su fi sauran mutane kula da jikinsu, dole suyi wanka da amfani da turare fiye da saura. Idan suna akasin haka shi zai sa a dinga cewa suna da warin kashi, saboda za'a ga kullum suna wanka amma kuma duk da haka suna wari.
Wasu mutane kuma za'a ga cewa ko sun kwana biyu basuyi wanka ba, ba wani wari mai yawa zaka ji suna yi ba, saboda yanayin fatar su.
Print this post
0 Comments