Ciwon Sanyi Na Mata: Alamominsa, Maganinsa Da Yadda Zaki Kare Kanki

Gabatarwa:

Maganin sanyin mata

Ciwon sanyin mata wata babbar matsala ce dake addabar mata a yanzu, akasarin mata na fama da wannan cutar, daga kauye zuwa birni, matan aure har ma da yan mata. Kafin nayi wannan rubutun sai dana tattauna da mata dayawa akan wace cuta ce tafi damun mata a yanzu? Amsar dana samu kuma ita ce ciwon sanyi. 

Shin mene ne ciwon sanyi? Meke kawo wannan cutar? Menene maganinta? Taya zamu kare kanmu daga kamuwa da ita? Domin samun amsoshin wannan tambayoyin ku biyo mu sannu a hankali a cikin wannan rubutun.

Mene ne ciwon sanyin mata?

Ciwon sanyin mata, ko wasu suce toilet infection ko vaginal infection duka na nuni akan abu daya ne. Ciwon sanyi wasu kwayoyin cuta ne dake addabar farjin mace. Wannan kwayoyin cutar na hana mace sukuni ta hanyar janyo kaikayin gaba, warin gaba, fesowar kuraje, fitowar ruwa fari ko yellow ko kore, jin zafi yayin jima'i, jin zafi yayin fitsari da dai sauransu.

Ire iren ciwon sanyi

Ciwon sanyin dake damun yaya mata bincike ya nuna kala kala ne kuma suna da yawa. A cikin wannan rubutu zamu yi bayanin mafi yawancin cututtukan sanyin da ke damun matan mu a yanzu banda cutar sanyin PID, saboda bayanin cutar sanyin PID ya riga ya gabata a baya.

1. Sanyin da kwayoyin bakteriya suke janyowa (Bacterial vaginosis)

Kwayoyin cutar bakteriya suna daya daga cikin manya manyan dake janyo cutar sanyi. Acikin mata 100 da su keda ciwon sanyi, kashi 50 suna dauke da bacterial vaginosis ne. Wannan na faruwa ne saboda yanayin canji na bakteriya din da ke jikin mace da kuma haɓakar ƙwayoyin bakteriya dangin Gadnerella.

Asali akwai bakteriya masu bada kariya a farjin mace wanda ake kira da "normal flora". Idan wannan bakteriya suka habaka suka yadu sukan zama kwayoyin cuta masu illah, kaman 'Gardnerella vaginalis' sai su haifar da ciwon sanyi.

Yaya ake kamuwa da wannan cutar sanyin bacterial vaginosis?

Abubuwan da ke karawa mace haÉ—arin kamuwa da wannan cutar sanyi na bacterial vaginosis sune kamar haka;

1. Rashin tsaftace farji

2. Amfani da abubuwan tsara iyali kaman su implanon, intrauterine device (IUD).

3. Samun ciki

4. Mu'amala da maza dayawa.

Alamomin Bacterial vaginosis

Maganin Bactelrial Vaginosis

1. Metronidazole (Flagyl)

Idan kinada ciki daya haura wata 3 kada kiyi amfani da wannan maganin.

2. Clindamycin (cleacin)

3. Ornilox

2. Ciwon sanyi wanda kwayoyin fungi ke janyowa (Yeast Infection ko Candidiasis)

Wannan kalan ciwon sanyin na faruwa ne sakamakon haɓakar kwayoyin cutar 'fungus' watau Candida albicans a cikin farjin mace. Asali farjin mace na dauke da wannan kwayoyin halittar amma basa cutarwa har sai sun kara yawa, sun haɓaka sun kai wata ƙima. Suna kara yawa ne idan suka samu damshi, ko waje marar iska, ko mace tana yawan amfanin da kayan ƙamshi a gaban ta wanda yin haka yana kashe normal bakteriya na farji masu hana kwayoyin Candida haɓaka.

Wannan kwayoyin cutar ba farji kadai suke tsayawa ba, idan garkuwar jiki tayi Æ™asa, suna iya yaÉ—uwa a cikin baki da maÆ™ogwaro su kawo wa mace oropharyngeal candidiasis ko candida esophagitis. 

Mata da yawa suna kamuwa da wannan cutar ta vaginal yeast infection a wani lokaci na rayuwarsu. A cikin kashi 100 kashi 75 suna kamuwa da shi. Cuta ce mai hatsarin gaske idan ba'a magance ta da wuri ba musamman ga masu ciki, ciwon suga ko kuma masu dauke da cuta mai karya garkuwan jiki kamar HIV.

Amma ciwon sanyi na yeast ba ciwo ne dake iya yaÉ—uwa yayin jima'i ba, ma'ana, ba ciwon da namiji zai iya dauka bane, kuma namiji ba ya iya yaÉ—awa mace yayin jima'i, duk da cewa bincike ya nuna a cikin kashi 15 cikin 100 na maza na samun kaikayin gaba ko fesowar kuraje bayan saduwa da macen dake dauke da wannan cutar ta yeast infection.

Alamomin yeast infection

1. Kaikayin gaba

2. Radadi a farji

3. Fitan farin ruwa mai kauri, ko mai yanayi kamar awara ko dussa fari kal.

4. Jin zafi yayin jima'i

5. Labben farji suyi jawur ko su kwaile

6. Fesowar kuraje.

7. Kumburin gaba

Maganin yeast infection

Akwai magungunan da zaki sha domin magance wannan cutar...

1. Fluconazole (Diflucan) ko

2. Itraconazole (Sporanox)

Likita zai miki bayani a kan yadda zaki sha magungunan.

Sannan idan cutar bata fara karfi ba akwai wasu magungunan da mace za ta iya amfani dasu. Wannan sakawa a keyi a cikin farji, akwai vaginal tablets ko creams na kwana 7 zuwa 14 d ya danganta da yadda likita yace kiyi amfani dashi. 

Koda kin fara amfani dashi sai kika ji sauki bayan kwana 2 ko 3 kada ki dena amfani da shi ki cigaba har sai kin gama dose din da likitan ki ya fada saboda idan cutar bata mutu baki daya ba zata iya dawowa daga baya. Daga ciki akwai magungunan inserting akwai:

- Klovinal

-Nystatin (Mycostatin)

-Miconazole

-Clotrimazole 

Yana da kyau idan kina maganin ciwon sanyi, idan da hali ki canja wandonanki, idan babu hali ki wanke su duka da ruwan É—umi ki shanya a rana.

3. Ciwon sanyin mata wanda kwayoyin cutar virus yake kawowa.

Wadannan wasu kalolin ciwon sanyin mata ne da ake kamuwa dasu ta hanyar jima'i wato, watau ta hanyar saduwa tsakanin namiji da mace. Mace zata iya shafawa mijinta idan tana mu'amala da wasu mazan banza a waje. Haka shi ma namiji zai iya shafawa matar sa idan yanada mata sama da daya ko kuma idan yana neman matan banza a waje.

Namiji ba kasafai yake gane yanada wadannan cututtukan ba saboda alamomin su basu cika bayyana a jikin namiji ba. Yawanci sai idan ciwon ya bayyana a jikin mace, wajen neman magani sai ya gane shima yana dashi. Kwayoyin cutar virus na dangin Herpes da kuma human Papilloma Virus su ne suka fi kawo wadannan cututtukan sanyi maso feso da ƙurajen gaba.

Amma idan anyi sa'a ya bayannana cikin namiji akwai alamomi kaman haka;

1. Jin zafi yayin fitsari

2. Jin zafi bayan fitan maniyyi

3. Fesowar kuraje a al'aura

4. Kaikayin gaba

Alamomin mata

1. Fesowar kuraje a gaban mace

2. Jin zafi wajen fitsari

3. Warin gaba

4. Fitan ruwa mai launin yellow ko kore ko fari tass.

5. Kwailewar farji

6. Ƙaiƙayin gaba

Mafi akasari cututtukan sanyin mata da kwayoyin virus ke kawowa suna bayyana ne ta hanyar fesowar kuraje a gaban mace ko namiji, wasu kurajen sukan zo da ƙaiƙayi wasu kuma kuraje ne kawai ke fitowa ba ciwo ba ƙaiƙayi.

Wasu alamomin ciwon sanyi da mata basu kula da su

- Ciwon mara: Ciwon sanyi na janyo ciwon mara sosai koda ba lokacin ala'ada ba.

- Wasa da al'ada: Sai kiga ala'ada na miki wasa, ko yanayin fitar jini ya karu ko ya ragu.

Yadda mace za ta kare kanta daga kamuwa da sanyin mata

A wannan gabar, zamu yi bayanin dabi'un mata na yau da kullum da zasu iya janyo wannan cutar na ciwon sanyin mata da rigakafinsu.

1. Yanayin tsaftace farji

Wasu matan suna amfani da abubuwa da dama wajen tsaftace farjinsu, a ganinsu hakan shi ne dai-dai. Kaman amfani da ruwan gishiri, ruwan dettol, ruwan lemun tsami, medicated soaps da sauransu. Wanann ba tsaftace farji suke yi ba, hasalima kina kara É“ata halittar farjin ki. 

Kamar yadda mukayi bayani a baya game da normal flora, yawan amfani da wadannan abubuwa na kashe hallitun na normal flora a cikin farjin mace. Kuma asali shi farjin mace na tsaftace kansa da kansa a yanayin hallitar sa, saboda haka yar uwa ki dinga amfani da ruwan dumi kawai wajen tsaftace kanki.

2. Yadda ake wanke dubura bayan kinyi bayan gida

Asalin yadda ya dace ki wanke bayan gida shi ne ki fara daga gaba zuwa baya, ma'ana daga farji zuwa dubura. Amma mata da yawa akasin haka sukeyi. Wannan dabi'ar sam bata dace ba. Idan kika fara daga baya kina É—ebo kwayoyin cutar dake cikin bayan gidanki kina aikawa cikin farjinki. Hakan zai janyo miki da matsala babba saboda shi farji baya bukatar bakon abu a tattare dashi.

3. Amfani da bandaki mai datti

Yawancin mata na daukan ciwon sanyi bayan amfani da bandakunan da mutane dayawa ke amfani, watau public toilet. Shi yasa wasu ke cewa ciwon sanyi toilet infection.

Bandakin tsugunno: Idan misali mace mai wannan cutar sanyin mata tayi fitsari a kasa, sai ke ma kika je kika tsugunna, fitsarinki ya taba wajen kuma ya dan fallatso a gaban ki, toh fah 'yar uwa zaki kamu da cutar sanyin da waccan matar ke dauke da ita. Saboda haka idan zaki tsugunna ki tsugunna waje mai kyau inda ba'ayi fitsari ba, kuma kiyi hankali kada ya fallatsa a jikin ki.

Bandakin zama (water closet system):

Kafin ki zauna ki saka tissue a cikin toilet sit din saboda farji a bude yake zai iya dauka kwayoyin cuta cikin sauki daga cikin toilet sit din. Kuma kada ki dade kina zaune akai.

4. Amfani da turare ko sabulu mai kamshi a gaban mace 

Dayawa mata na da wannan dabi'ar fesa abun kamshi ko wanke farji da sabulu mai kamshi. Wannan kuskure ne babba, saboda su wadannan kwayoyin cutar suna girma ne a inda yakeda damshi ko kamshi. Haka kuma mafi yawan kayan ƙamshi suna kashe normal flora, ma'ana kwayoyin halittu masu amfani dake zama a cikin farji.

5. Amfani da jikakken wando ko pant mai damshi

Amfani da jikakken wando na haifar da cutar ciwon sanyin mata, saboda kaman yadda mukayi bayani a baya, kwayoyin cuta musamman na yeast na son waje mai damshi domin karin hayayyafa da kuma haɓaka. Idan kin gama tsarki yanada mahimmanci daki tsantsane jikinki da tissue paper ko tawul mai kyau kafin ki maida wandon ki.

Kuma ki kasance kina amfani da wando da akayi da auduga (pure cotton) saboda sunfi tsotse damshi da kuma ba farji damar shan iska fiye da wanda akayi da nylon. Haka kuma ki dinga shanya wandunanki a rana saboda kashe kwayoyin bakteriya akan ki shanya su a inuwa cikin bandaki.

6. Shan magani ba bisa ka'ida ba

Mutane nada wata dabi'ar siyan magani barkatai ba tare da sanin likita ba. Misali yawan shan antibiotics da kinga kurji a jikinki ko kina ciwon wuya da sauransu, yawan haka na janyo infection. Bama vaginal infection kawai ba, hadda wasu cuttukan ma na daban, saboda haka a kiyaye yawan shan antibiotics batare da sanin likita ba.

7. Tsarin iyali.

Idan mace na tsarin iyali domin samun tazarar haihuwa toh akwai yiwuwar zata iya kamuwa da ciwon sanyi. Saboda yanayin chanji na sinadaran hormones din mace na shafar farjin ta. Koda kina shan pills, ko kinada implant a hannu, ko an daure bakin mahaifarki da dai sauransu.

Kammalawa 

A cikin wannan rubutu munyi bayani game da mafiyawancin cututtukan da ake kira sanyin mata. Idan kuna da tambayoyi game da rubutun, toh kuyi mana su a akwatin sharhi da ke kasa.

Post a Comment

0 Comments