Gabatarwa:
Basir ko kuma dankanoma mai tsiro wanda aka fi sani da "hemorrhoids" ko kuma "piles" a turance, larura ce da ke ci gaba da shan gurguwar fahimta a tsakanin al'umma.
A ilmin kiwon lafiya na zamani, ba wani abu ne basir ko dankanoma mai tsiro ba face kumburarrun jijiyoyin jini a cikin ƙarshen babban hanji da kuma dubura. Waɗannan jijiyoyin jini su ne su ke kumbura kana su tale har su yi bulli cikin ƙarshen babban hanji ko a kewayen dubura.
Basir ko dankanoma mai tsirowa a cikin ƙarshen babban hanji shi ne internal hemorrhoid ma'ana basir na cikin dubura yayin da basir a kewayen dubura, wanda shi ne ke zazzagowa har ya fito a waje shi ake kira da external hemorrhoid ma'ana basir na wajen dubura.
Basir mai tsiro a waje, ci gaban basir na kewayen dubura ne wanda ke bayyana yayin da matsalar ta je matakin ƙarshe. Basir mai tsiro a waje yana faruwa ne sakamakon zazzagowa ko saukowar jijiyoyin jinin da suka yi bulli zuwa wajen dubura, musamman yayin yunƙuri ko yin bahaya mai ƙarfi.
Alamomin Basir Ko Dankanoma Mai Tsiro
Alamomin basir sun danganta ga wane irin basir ne mutum yake da, basir na cikin dubura ne ko kuma basir na wajen dubura.
Alamomin basir cikin dubura sun hada da:
1. Zubar jini ba tare da jin ciwo ba yayin bahaya ko kuma tsuguno. Wannan shi ne babban alamar basir na cikin dubura wanda yake fitowa a ƙarshen hanji ba tare da ya zazzago a waje ba.
2. Wani basir mai tsiro wanda ke fitowa a ƙarshen hanji yana girma ya zazzago har zuwa a wajen dubura har sai an tura da yatsa domin mayar da shi. Yana iya haifar da ciwo da raɗaɗi.
Alamomin basir na wajen dubura sun haÉ—a da:
1. Ciwo mai raÉ—aÉ—i yayin bahaya ko tsuguno
2. Ƙaiƙayin dubura ko watarana mutum yaji kamar ana sukar sa a cikin dubara.
3. Kumburi a kewayen dubura da ke fitowa a waje.
4. Zubar jini yayin yunƙurin tsuguno.
5. Watarana tsiron basir din ya kan iya fashewa ya fara zubar da jini ko majina ko ruwan ƙurji.
Abubuwan da ke kawo basir
Basir na faruwa sakamakon takurar jijiyoyin jini a dubura har su kumbura sannan su yi bulli saboda abubuwa kamar haka:
1. Yawan yunƙuri yayin tsuguno ko yin bahaya mai tauri.
2. Tsawaitar lokacin tsuguno.
3. Fama da atini ko kuma taurin bahaya na tsawon lokaci.
4. Rashin yin bahaya na tsawon lokaci
5. Kasancewa mai Ƙiɓa/teɓa.
6. Yawan samun ciki da haihuwa ga mata.
7. Yawan zama wuri daya kullum, kamar masu É—inkin tela, direbobin mota, 'yan achaba da dai sauransu.
8. Cin abincin mai ƙarancin sinadarin fiber, harza ko ganyayyaki.
9. Yawan É—aga kayan nauyi akai-akai, kamar 'yan wasanni masu yawan É—aga karfe, 'yan dako, masu tura baro da dai sauransu.
10. Ciwon tari na tsawon lokaci, kamar masu cutar tarin fuka.
A lura cewa a mafi yawancin cases na basir ko dankanoma mai tsiro yana fitowa mutum haka kawai ne, ba tare da mutum ya gane takamaiman abin da ya kawo masa wannan lalurar ba.
Haka kuma masana sun tabbatar da akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin basir ko dankanoma mai tsiro da gado. Wasu ma sun tafi kan cewa, babban abinda ke kawo dankanoma mai tsiro shi ne ana gadon sa ne daga magabata.
Hanyoyin Kiyaye Basir/Dankanoma Mai Tsiro Cikin Sauƙi
Hanya mafi inganci wajen kiyaye kai daga basir ko dankanoma mai tsiro ita ce sanya bayan gida ya zamo mai laushi yadda zai fice ba tare da yunƙuri sosai ba.
WaÉ—annan hanyoyin da za mu lissafa za su taimaka wajen kiyaye kai daga basir da kuma rage matsalolinsa idan ya riga ya auku.
1. Cin abinci mai É—auke da sinadarin fiber sosai: Abinci mai É—auke da sinadarin fiber ko dusa sun haÉ—a da 'ya'yan itatuwa, ganyayyaki da kuma tsabar hatsi.
2. Shan isasshen abin sha: Shan isasshen ruwa aƙalla lita 2 - 3 kowace rana da sauran ya'yan itace masu masu ruwa-ruwa, kamar lemu, kankana da kuma aiba. Shan wadannan abubuwa yana sa mutum yaji saukin yin bahaya kuma ya dinga yi akai-akai ba tare da takura ba.
3. Rage yunƙuri yayin bahaya: Yunƙuri tare da nishi ko riƙe numfashi yayin tsuguno na takura jijiyoyin jini a cikin dubura. Haka kuma yana ƙara sa jijiyoyin su zazzago a wajen dubura kuma su kumbura.
4. Garzayawa da zarar an ji uzurin bayan gida: Yin buris da bayan gida yayin da aka ji shi na janyo hanji ya ci gaba da tsotse ruwan bayan gidan har ya yi tauri.
5. Atisaye: Yin atisaye ko motsa jiki na taimakawa rage taurin bayan gida. Haka kuma, atisaye na taimakawa wajen rage ƙiba wanda hakan zai rage nauyi ko takura ga jijiyoyin jini a cikin dubura.
6. Kauce wa dogon zama: Dogon zama na ƙara takura jijiyoyin jini a dubura.
7. Yin gashi da ruwan zafi da gishiri: A likitance wannan ita ce hanya mafi inganci wajen kiyaye kumburin basir ko tsiron dankanoma wanda ya ta'azzara.
Yadda Ake Gashin Dankanoma Mai Tsiro/Basir
Gashin dankanoma da ruwan zafi hanya ce mai inganci sosai wajen kiyaye dankanoma mai tsiro ko basir ta hanyar rage masa kumburi, ciwo da kuma dukkannin sauran alamomin sa.
Ana gashin dankanoma ne da ruwan zafi da gishiri. Yadda ake yi shi ne, mutum zai samu baho ko babbar roba da zai iya zama a cikinta. Sannan sai ya dafa ruwan zafi su yi zafin da zai iya zauna wa a cikin ruwan ba tare da sun babbake masa fata ba.
Bayan an zuba ruwan zafi a cikin baho sai a kawo gishiri mai dan yawa a zuba a cikin ruwan, a cigaba da zuba gishiri a cikin ruwan zafin sannu-sannu ana gaurayawa har sai gishirin ya daina narkewa a cikin ruwan zafin. Toh a wannan lokaci ne gishirin ya isa yadda ake bukata.
Daga nan sai mutum ya zauna a cikin ruwan zafin ya shafe kamar mintuna 15 zuwa 20. A lura cewa, yana da kyau maza tallabe ya'yan marinar su da hannun hagu daga cikin ruwan zafi a lokacin da suke zaune a cikin ruwan. Dalili kuwa shi ne; ƙwayoyin halitta da ke cikin ya'yan marina basu bukatar zafi.
Ana so mutum ya kiyaye yin gashi kamar sau biyu ko uku a yini. Yin haka zai taimakawa dankanoma mai tsiro ko basir sosai wajen samun sauki. Munyi rubutu sha kundum a inda muka yi bayani dalla-dallah akan duk hanyoyin da ake bi domin magance basir ko dankanoma mai tsiro a asibiti. Dan wannan rubutun domin karantawa.
Kammalawa
Basir ko dankanoma mai tsiro larura ce da za'a iya samun sauƙi bayan amfani da magunguna da sauran hanyoyi a likitance. Amma idan basir ya yi tsanani yin tiyata na iya zama dole kafin warkewa.
Yana da kyau a tuntuɓi likita da zarar alamomin basir sun bayyana maimakon shan magungunan gargajiya da ba ka da tabbacin ingancin su.
0 Comments