Maganin Warin Baki: Yadda Ake Kula Da Tsaftar Baki Da Hasken Haƙora


Maigida duk abin bai kai haka ba, ta ce masa. Ita uwargida tana ma mijin ƙorafi akan yana da warin baki. Shi kuma yace ya yarda, amma ta daina goranta masa yana yi. Kuma idan ya kusance ta da niyyar saduwa, sai ta dinga juya fuskar ta zuwa wani gefe ko dama ko hagu har sai ya gama. Wannan ma yana masa ciwo. Mu dai mun masa nasiha kuma mun bashi shawarwari. To amma bai kamata a bar shi hakanan ba, ya kamata a yaɗa  wasu hanyoyin da ya kamata kowane mutum ya kiyaye domin tsaftar bakin sa da kiyaye warin baki.

Maganin Warin Baki

Jama'a kun ji yadda warin baki ke yiwa aure barazana. Shi dai warin baki abubuwa da yawa kan iya haifar da shi. Daga cikin su akwai:

  • Rashin kulawa da tsaftar baki
  • Cututtukan baki kamar irin su mouth ulcer, gingivitis, odontitis periodontal abscess, dental carries da dai sauran su.
  • Cututtukan huhu irin su pneumonia, chronic bronchitis, lung abscess and empyema.
  • Wasu cututtukan irin su sinusitis, ciwon sukari, ciwon hanta da dai sauransu. 

Mun yi bayani na musamman akan cututtukan da ke kawo warin baki a cikin wannan rubutu https://www.lafiyata.com.ng/2023/03/yadda-ake-maganin-warin-baki-treatment.html ga masu neman ƙarin bayani.

Saboda haka, idan aka lura warin baki ya ta'azzara duk da ana kulawa da tsaftar baki yadda ya kamata toh sai a garzaya zuwa asibiti domin tantance abin da ya assasa warin bakin. 

A cikin wannan rubutu zamu kawo muku wasu hanyoyi da zasu taimaka wajen tsaftar baki da kuma kariya daga warin baki kamar haka:

1. Amfani da man goge baki (toothpaste) mai kyau 

Tun farko ya kamata ku samu toothpaste masu kyau, bana so na fadi suna amma akwai toothpaste marasa kyau. Misalin masu kyau akwai irin su Colgate, Crest, Tom’s of Maine, Oral B, Dabur da sauran su.

Sannan yana da kyau idan kana da wani matsala na musamman, misali dasashin ka suna da matsala, zaka iya dinga amfani da Sensodyne at a ƙalla sau biyu a mako (A lura cewa, Sensodyne ba toothpaste din yau da kullum bane, so kar ka rika amfani da shi kullum sai idan akwai bukatar yin haka). Sannan shi kansa buroshin goge  baki (toothbrush) ka samu brand din Sensodyne ko Oral B, suna da kyau sosai.

Da zaka daure ko zaki daure a koma sunnah hygiene, da sai nace aswaki is the best tool for mouth hygiene. Yana da sinadarai da suke kashe bacteria mai saka warin baki, sannan yana kara farin hakora. Fake yin shi a lokacin alwala kawai yafi duk wani remedy da wani zai gaya maka. To amma mutanen mu zai wuya suyi amfani da shi, wasu ma suna ganin kamar yin aswaki yawa ne.

2. Kiyaye goge baki kullum 

Kullum kayi brush akalla sau biyu, da safe bayan ka karya, da kuma da daddare lokacin da kake shirin kwanciya. Wasu masana suna bada shawarar yin brush duk bayan cin abinci, haka likitocin hakori suka ce. 

Haka kuma, yana da kyau duk lokacin da ka gama cin kowane irin abu ka kuskure bakin ka da ruwa don hana abinci zama da ruɓewa a cikin haƙori. Sannan ka rika sakace idan ka ci abu mai makalewa a cikin haƙori. Idan kuma bakin ka yana idle baka magana ko cin wani abu, ka iya samun chingum (chewing gum) kana taunawa.

3. Amfani da lemon tsami

Once in a while, za ka iya yin home made toothpaste. Ka samu Baking Soda da lemon tsami, baking soda cikin teaspoon da rabin lemon. Sai kayi mixing. Sai ka dora akan brush din ka kamar toothpaste sai ka wanke bakin. 

Kar kayi fiye da sau ɗaya a sati. Saboda soda tana kashe hakori idan tayi yawa. Another type of mixture shine Kanunfari da charcoal da gishiri. Ka nika su tare, su zama gari, sai ka matsa lemon sai kayi paste kayi kamar yadda nayi bayani a baya.

4. Amfani da shayin wanke baki (mouthwash)

A rika amfani da antibacterial mouthwash irin su Listerine at least sau biyu a sati. Kurkurewar zai kashe kwayoyin cuta na bacteria da take zama. Lokacin da yafi da ake so kayi amfani da shi shi ne lokacin kwanciya ko da zarar ka tashi kafin kayi komai sai ka Kurkure. 

Idan baka da ƙarfin siyan Listerine, zaka iya samun Gishiri da Ruwan dumi kana zubawa don Kurkurewa. Ko kuma za ka iya samun Apple Cider Vinegar wato Kal-Tufa da Hausa, ka saka cikin teaspoon sai ka zuba a Ruwan dumi a kofi ko kwatar kofi ne sai ka kurkura. Shima kar ya wuce sau daya a sati, kuma kar ya wuce minti daya a baki.   

5. Ziyarar likitan haƙora akai-akai 

Daga ƙarshe ka rika zuwa asibitin hakori ana maka wankin baki a ƙalla sau biyu a shekara. Hakan zai taimaka wajen gano matsalar baki da magance ta a cikin lokaci. Sannan wanke baki da injimi yana karawa hakori tsafta da haske da kuma cire wasu datti da buroshi baya iya cirewa. 

Ma'aurata zasu iya yin wadannan routines din tare. Ke kuma uwar gida ki riƙa amfani da hikima wajen gayawa mai gida yayi wanka ko ya wanke bakin sa. Ke ma kuma zaki iya haɗa masa wancen toothpaste din da nayi bayani. Ki bashi, na tabbata zai ji daɗi. 

Amma nuna masa kyama raini ne da kuma rashin sanin darajar miji. Although nasan wasu ƙazamai da yawa basa wanka sai ance suyi, don Allah yan uwana maza da mata a rinƙa tsafta. Sannan a rika kula da tsaftar baki, hammata da kuma gashin gaba da sabunta boxers da underwears a kullum. Ma'aurata dayawa na shiga cikin halin damuwa da rashin jindadin aure idan abokin tarayyar su ya kasance ƙazami. Allah yasa mu gane. 

Post a Comment

0 Comments