Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Me Ke Kawo Ciwon Nono A Lokacin Jinin Al'ada (Period)?

Maganin ciwon nono

Irin wannan ciwon nono yana faruwa ne ga mata a lokutan da sinadaran sex hormones dinsu (oestrogens da progesterone) su ke hauhawa ko kuma suke a halin rashin daidaituwa. Normally sunfi samun irin wannan ciwon a lokuta 3 kamar haka:

  • 1. Lokacin da suke yin al'ada 
  • 2. Lokacin da suke yin ovulation, wannan yana faruwa kamar kwanaki 10 ko sha biyu bayan al'adar su ya dauke
  • 3. Lokacin da suke da É—anyen ciki.

Haka kuma suna iya samun irin wannan ciwon a lokacin da suke shayarwa, da kuma kananan yara a lokacin da suke tashen balaga da kuma tsofaffi a lokacin aladan su ya kusan É—aukewa. Duka irin wadannan matan suna samun hormonal imbalances wanda shi ne zai kawo musu wannan ciwon.

A irin wannan ciwon ba abu ne mai buÆ™atar magani ba, saboda yakan zo ya wuce daga zarar hormones na mace sun daidaita. Amma wasu matan yakan takura su har ya hana su sukuni, wasu kuma yakan shafi mu'amalar su ta aure tsakanin su da mazajen su. 

Saboda haka, matan da suka kasa jurewa ana basu simple pain relievers; kamar irin paracetamol, diclofenac ko ibuprofen.

Haka kuma ana basu shawarar yin amfani da rigar nono dake kame jikinsu da kyau. Bugu da kari, zasu iya gashi da ruwan zafi ko abu mai É—imi haka.

A wani lokaci ana ba mata magungunan bada tazarar iyali masu É—auke da sinadaran sex hormones na mata (Estrogen da Progesterone) domin daidaita musu sinadaran. Amma kuma wani bincike ya nuna cewa su ma wadannan magungunan suna iya kawowa mace irin wannan ciwon nonon ta hanyar barkata musu sinadaran.

A lura cewa, dole sai an tabbatar da cewa nonon ba wani ƙololo, ƙurji, ko tsiro a cikinsa kamin a alaƙanta ciwon nonon da abubuwan da muka lissafa a sama.

Print this post

Post a Comment

0 Comments