Abubuwan Da Ke Kawo Kaikayin Nono Bayan Haihuwa

Assalamu alaikum likitocin mu barkar ku da kokari. Don Allah Ina da tambaya me ke sa kaikayin nono? Na haihu 2 month da haihuwa amma tsakanin jiya da yau nono na dama ke kaikayin can kasan shi zuwa kan shi.
Kaikayin Nono

Amsa

Kaikayin nono bayan haihuwa yana iya kasancewa sakamakon abubuwa masu yawa. Wasu daga cikin dalilan da za su iya kawo kaikayin nono bayan haihuwa sun haÉ—a da:

1. Canjin sinadarai da ke faruwa bayan haihuwa 

Bayan haihuwa, jikin mace yana ci gaba da sauye-sauyen zubar ruwan sinadaran hormones na estrogen, prolactin, da oxytocin, wanda zai iya kawo bushewa ko kaikayi a fatar nonon mace, musamman wuraren da basu saba da wadannan canje-canjen, ba kamar kan nono.

2. Tsotson Jariri

Kaikayin nono bayan haihuwa

Tsotson kan nonon mace da jariri me yi, yana iya sanya fatar nonon mace tayi laushi ko kaushi, wanda zai iya kawowa mace kaikayin nono ko rashin jin daÉ—i a kan nono.

3. Kamuwa da kwayoyin cuta

Idan mace ta samu kaikayin nono mai tsanani tare da kumburi ko canja launin fatar nonon zuwa ja-zur, hakan yana iya zamowa alamar infection kamar mastitis ko thrush.

4. Bijirewar fatar nonon mace ga wasu abubuwa da take yin mu'amala dasu

Wasu lokuta kaikayin nono yana zamo wa saboda matuƙar shafawa, ko wani sabulu, ko ruwa, ko man shafawa, ko rigar nono, ko tufafi waɗanda kikeyin mu'amala dasu ne. Kaikayin nono na iya samuwa saboda rashin jituwar fatar nonon mace da waɗannan abubuwan.

Idan kaikayin ya ci gaba ko yayi tsanani, ko aka lura da kumburi, Æ™uraje ko canjin launin fatar nono, toh, yana da kyau aje asibiti domin likita ya duba ki ya gano ainihin abin da ya haifar da  matsalar.

Post a Comment

0 Comments